FreeArewaPen original
KISHIYA TARA
- 1views
- 71chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci ba makaryaci ba ne
Sample · Chapter 1
*KISHIYA TARA* *RUBUTUN* *MARYAM LITEE* Wani irin daji ne mai manyan bishiyoyi iya ganin idonka tare da kukan tsuntsaye, ba tare da la'akari da cikin jikina ba nake gudu duk inda na taka kafata kuma sai dai ka ji cas karar da take bayarwa kenan gumi gabadaya ya lullube ni na kara daga kafa yayin da na hango karshen dajin wani fili ne fetal na isa gare shi ban fasa gudu ba wani irin zafin rana na ji a tafunan kafafuna duk da babu ranar ban fasa ba na cigaba da gudu har na fara hangen wasu gidajen Fulani na karasa cike da sa rai wata mata da ta fara shiga shekarun girma na gani jikin wata bukka ta zubo mini ido. Baka ce gajeriya, na kusa daf da ita na yanke jiki na fadi daidai da farkawa ta daga barcin da nake wannan mafarki, duk na yamutsa shimfidar gadona gumi ya rufe ni na tashi zaune ina dafe da kaina kafin na mike tsaye ba abin da nake so sai na bar gidan na nufi inda na gani a mafarki jikina daga ni sai bakar doguwar riga da bakar hula sanye a kaina. Ban tsaya neman takalmi ba na fita ba da wanda na hadu har na fice sashena na isa harabar gidan masu hidimar gidan da ke kai da kawo ba wanda ya gwada ya gan ni har na bude kofar masu fita a kafa get man da abokansa biyu masu taya shi hira ba su dube ni ba. Da fita ta gabas na nausa sai da na yi tafiya mai tsananin gaske na riski dajin da na gani a mafarki abin da ya faru a mafarkin shi ya kasance banbanci wannan ba gudu nake ba, har na tarar da bakar mata a bakin bukka faduwa ta ban san me ya faru ba na farka ne na gan ni karkashin bishiya an yi mini shimfida wani kakkarfan matashi fari tas dogo da ba zai gaza shekaru talatin ba durkushe gabana da wata yar matashiya da na yi tunanin matarsa ce. "Ta tashi Amine. Samo ruwa a ba ta." Ya ba ta umarni, ta tashi da saurin gaske ta tafi. Ta dawo da koko ta mika masa ya dube ni "Tashi baiwar Allah." Na yunkura sai na ji jikina ko'ina na ciwo, sai da na daidaita zamana ya miko mini kokon na karba farin ruwa ne tas na sha sai ya ce na shafa ma fuskata. Na yi kamar yadda ya ce sai ya fara tambaya ta sunana da garin da na fito na bude baki da niyyar magana na kasa, na kama makoshina amma magana ta gagara wai wankin kuturu da sabulu. Ya dubi matar ta dube shi "To raka ta dakin Inna." Ta yi saurin zaro ido sai ta dubi cikin jikina sai ta yi masa magana da fulatanci ya amsa mata da Hausa sai ta tashi ta tafi. Mun zauna shiru na wani dan lokaci ta dawo ya ce ta taimaka mini na tashi na mike da taimakonta muka taka zuwa wani daki da ke bayan bukkokin su ta daga farin labulen dakin mai shara-sharan da ake hangen waje muka shiga da alamar dakin na ajiye shirgi ne duk da ta yi kaye-kaye da sauran kaya sai gadon kara wanda aka yi wa shimfida ta ce na zauna na yi yadda ta ce ta zauna kusa da ni tana murmushi "Bakinki zai bude z...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.