DUHUN ZUCIYA❤️❤️❤️Free

ArewaPen original

Non-fictionFreeOngoing

DUHUN ZUCIYA❤️❤️❤️

  • 1views
  • 50chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Am not just to here to write but to entertain and touch the heart of the readers

More from @sadnaf

Sample · Chapter one

DUHUN ZUCIYADarkness of the HeartNA SADNAFA Z CollectionPage 1ZAHRAA guje ta ƙarasa dakinsa, hankalinta a matuƙar tashe da irin kiran da yake mata a haukace.Har gobe ta kasa sabo da wannan balain nashi. Ta kasa yarda wai yau mijinta, uban ‘ya’yanta, wanda ya so ta kamar ya yi hauka da tarin alkawaruka,yau shi ya zame mata dodo, da sautin muryarsa yake zame mata tashin hankali, saboda ta san duk lokacin da ya mata kiran nan, tashin hankali ke biyo baya.Ko da ta isa dakinsa, kirjinta bai bar bugawa ba, don dukan da ya mata kwana uku da suka wuce, har yanzu ba ta gama jinyar jikinta ba.Ta gaji da dukan da yake mata. Duk da tsoronsa da take ji, yau in dai ya taɓa ta, sai ta rama. Sai dai idan kasheta zai yi, ya kashe ta.Ta gaji da auren. Ta gaji da komai ma.A tsaye ta tarar da shi da wandon shaddarsa a hannunsa da ya sa a daren jiya.“Ke, wa ya shigo min ɗaki ya ɗauke min kuɗi?”Ido ta zuba masa tana kallonsa, don zuwa yanzu ba ta san yadda za ta fassara irin ƙiyayyar da yake mata ba. Har tsanar da ya mata ta kai ga ya mata sharrin sata?“Kika zuba min ido kina kallona? Wa ya kwashe min kuɗi a aljihun wandona? Kin san dai daga ni sai ke a gidan nan? Ameer ne zai ɗaukar min kuɗi ko Ahmad?“Lameer, ban ɗaukar ma kuɗi ba, don kai ma ka san ban shigo ma ɗaki ba. Tun da kulle ɗakinka kake idan ka dawo, kuma ba masallaci kake fita ba. Ballantana ka ce kana zuwa masallaci na kwashe ma kuɗi kana cikin ɗaki. Har yaushe na shigo ma ɗaki na kwashe ma kuɗi?“To, idan ba kece kika ɗaukar min kuɗi ba, uban wa ya ɗaukar min kuɗi? Na ce Ameer ne zai ɗauka ko Ahmad? Iya dai mu ne a gidan nan. Wa ya ɗauka idan ba ke ba? Wallahi tallahi, kafin na gama shiryawa ki fito min da kuɗina. Idan ba haka ba, wallahi sai kin yi dana-sani, sanina a rayuwarki. Na lura kwana biyu ina ƙyaleki, shi ya sa har kika samu ƙofar da za ki shigo min har ɗaki ki kwashe min kuɗi. Abin naki ba iya iskanci ya tsaya ba, har da sata.“Kuma ina ce miki ki ɗauko min kuɗina, kina rainawa kanki hankali.”Zahra, hawayen da ta yi sabo da zubar su ne suka hau zubo mata. Tana kallon uban ‘ya’yanta da ta zame masa maƙiya a rayuwa, wanda a shekarun da suka wuce, idan aka ce mata zai taɓa iya tsanar ta haka ba tare da ta masa komai ba, ba za ta taɓa yarda ba.Har gobe ta kasa samun amsar tambayarta na abin da ta masa ya mata wannan mugun tsanar.“Ki ɗauko min kuɗina, na ce miki.”“Lameer, tsanar da ka min ta kai ga ka min sharrin sata? Tun da nake da kai, ko allura na taɓa ɗaukar ma? Dan Allah, me na maka a rayuwar nan ka tsaneni? Lameer, ka san ba ka sona, me ya sa ka shigo min rayuwa da yaudara, ka nuna min, ka nunawa duniya kana sona, bayan ba ka taɓa sona ba? Na duba, na hanga, ban ma komai da na cancanci haka daga wajenka ba. Kiri-kiri kake nuna min tsana kamar za ka kashe ni. Ina matarka, haka za ka sani a gaba, ka...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “DUHUN ZUCIYA❤️❤️❤️” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play