FreeArewaPen original
INUWAR DUTSE.......
- 1views
- 74chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Hausa Novel writer
Sample · Episode 1
*_🗻𝙄𝙉𝙐𝙒𝘼𝙍 𝘿𝙐𝙏𝙎𝙀...🗻_* *_Rabi'a wakili_* *_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* *_Book 1_* *_Episode 1_* _______________________ Kowane ɗan adam yana ratsa sararin duniya ne ɗauke da wani tsari na daban wanda Allah Ya tsara mana a rayuwa. Wannan tafiyar ba ta da wata fuska ta zahiri, kuma ba ta da siffa ko launi da za a iya kallo da idanu muddin mutum yana raye, sai dai nauyinta da zafinta suna sauka ne kai tsaye a kan zukatan da ke ɗauke da ita. Akwai lokutan da walwala da daɗi ke bayyana a fili tamkar farin wata, akwai kuma lokutan ƙalubale masu ɗaci da ke girgiza jiki da firgita tunani, har ya kai ga mutum ya ringa gani a ransa tamkar dukan kofofin mafita da hanyoyin samun sauƙi sun riga sun datse, an bar shi shi kaɗai tsakanin tsananin fargaba da fita tsammani. To sai dai, a daidai lokacin da hasken rayuwa ya dusashe, s...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.