FreeArewaPen original
SILAR HALLACI
- 1views
- 17chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · FITAR AMO
*SILAR HALLACI...*!*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*FITAR AMO..!"Ahmed ka manta Wacece ni...? Nice fa masoyiyarka Samiha..? Ka manta alƙawarin mu...? Ka manta yadda muka tashi muna gina yadda Rayuwar Aurenmu zata kasance..? Amma yau rana ɗaya saboda wani dalilinka mara tushe ballatana makama kakeso kaƙi amfani da damar data samemu Ahmed...?"Hannu ya ɗaga mata lokaci ɗaya yana faɗin "Ya isa haka Samiha..!Nace ya isa Haka...? Ya kikeso nayi dake ne eh..? Karki manta ke matar Aure ce yanzu duk waɗannan burunkan namu sun yanke daga Lokacin da Mahaifinki ya bada ke..! Taya ya zan iya bin Buƙatarki alhalin kina matsayin matar Uban gidana..! Kuma nima ina matsayin Surukinsa ina Auren 'ƴarsa ta cikinsa kuma sai na biye miki naci amanarshi.? A'a ba zai Taɓa faruwa ba bazan Taɓa yima Maigidana Haka ba SILAR HALLACIN da yayi min bazai Taɓa barina na iya cin Amanarsa ba SAMIHA...Kiyi Haƙuri...!Wani irin kallo take Jifanshi dashi Lokaci ɗaya manyan Idanuwanta na Tara ƙwallah cikin Takaici da wani taku ta ta fara takawa zuwa gabanshi shi kuma yayi saurin Juya mata baya yana Ɓoye Siririyar ƙwallar dake Cikin Idanuwansa, murmushin dayafi kuka ciwo ta saki kafin tace "Ahmed kar ma ka fara wannan ganganci... Karma ka fara Tunanin wannan karon zaka iya Guje min... Baka isa ba Wlhi Tallahi na yi ma kaina alƙawarin sai na mallakeka Ahmed a matsayin Mijina ko ta Halin ƙaƙa.." Ta faɗa Lokaci ɗaya tana Zurama bayansa Ido Cikin mamaki ya Juyo yana faɗin "Me kike Nufi Samiha..? Karki manta kefa yanzu ba yarinya bace kin zama babbar mace kin mallaki hankalin kanki..Balle nace yarinta na damunki kiyi gaggawan barin mun office kafin na saka afitarmin Dake..." Ya faɗa yana Haɗe Ransa Lokaci ɗaya yana Nuna mata hanyar waje Wani Murmushin Mugunta ta saki kafin tace "Ni kake kora Ahmed...?"Bai mata magana ba illah Nufar Teburinsa da yayi yana danna wasu lambobi bisa Telephone ɗin dake kan Teburin Wata ƙaramar Dariya ta saki Lokaci ɗaya tana faɗin "Zan tafi... Amma ba domin zaka kira min Jami'an Tsaro ba sai domin Soyayyar da nike maka ta gaskiya ne ina sonka Ahmed kuma ina son kasancewa da kai..amma ba domin haka ba zan ƙyaleka ka kira wanda zaka Kira kafin su taho nayi Tsirara agabanka suna zuwa zan Fara kuka nace kai ne kake neman yimin Fyaɗe, daga nan in Alhaji yaji komai ya lalace maka.." Ta faɗa tana wani Sakar mai Idanuwanta.Tsam yayi kawai yana Kallonta bai samu Zarafin magana ba ta ƙara Taku zuwa gabanshi sai ta wani juya mai kafin tace "Karka damu bazan yi haka yanzu ba...Matukar kabani Haɗin kai komai Zai tafi yarda na Tsarashi in kuma ka cigaba da Taurin kai.." Ta Ƙarashe faɗa tana Shafa Sajen Fuskarsa Saurin Kauda kai yayi Cikin ɓacin Rai jakarta ta Ɗauka da wayarta dake saman Kujera ta kama Hanyar Fita tana Kadamai Mazaunanta Saurin ɗauke kai yayi yana ta'awizi acikin R...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.