FreeArewaPen original
Da walakin...
- 1views
- 22chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · PAGE 1
Tamkar wacce za ta je gasar kyau haka ta caɓa kwalliya da ado, ta shafe ilahirin jikinta da shu'umar humra, wacce take ɗaya daga cikin manyan makamanta dake yi mata jagora wajen tashin kan namiji cikin ƙanƙanin lokaci. A hankali ta fito tana taku cikin yanayin da ke nuna tana fargabar wani ya ganta. Da alama haƙanta bai cim ma ruwa ba, domi kuwa tana ƙarasawa falon ta tarar da matar da take yi wa kallon dodo hakimce a kujera tana latsa waya, kallo ɗaya ta yi mata gabanta ya faɗi, ta ji irin yanayin da takan ji a duk sanda suka haɗa ido, daidai sanda ta zo dab da ita matar ta ce"A shiga a fito dai, don mijina ya fi ƙarfin haɗa jiki da ke wallahi". Ko juyowa ba ta yi ba, don idan da sabo ta saba da jin maganganu makamantan wannan, daga bakin kishiyar tata, kuma sam ba ta iya tanka mata, saboda haka ta wuce, ta tunkari turakar mai gidan nata kai tsaye cike da fargaba da fatan Allah Ya sa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.