DANGAR WUTAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

DANGAR WUTA

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

HAUSA NOVELS WRITER

More from @maryamstar248

Sample · Chapter 1

*** 𝙒𝙐𝙏𝘼🔥            𝘕𝘈𝘔𝘈𝘙𝘜𝘉𝘜𝘊𝘐𝘠𝘈𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍⭐💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙨 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪𝙂𝙖𝙗𝙖𝙩𝙖𝙧𝙬𝙖𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙙𝙪𝙠𝙖 𝙖𝙗𝙞𝙣 𝙙𝙖 𝙮𝙖 𝙠𝙪𝙣𝙨𝙖 𝙠𝙞𝙧𝙠𝙞𝙧𝙖 𝙣𝙚, 𝙗𝙖𝙣𝙮𝙞 𝙨𝙝𝙞 𝙙𝙖𝙣 𝙘𝙞𝙣 𝙯𝙖𝙧𝙖𝙛𝙞 𝙠𝙤 𝙢𝙪𝙩𝙪𝙣𝙘𝙞𝙣 𝙠𝙤𝙬𝙖 𝙗𝙖 𝙣𝙖 𝙧𝙪𝙗𝙪𝙩𝙖 𝙨𝙝𝙞 𝙣𝙚 𝙙𝙤𝙣 𝙞𝙡𝙞𝙢𝙖𝙣𝙩𝙪𝙬𝙖 𝙙𝙖 𝙛𝙖𝙙𝙖𝙠𝙖𝙣𝙩𝙪𝙬𝙖, 𝙞𝙙𝙖𝙣 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙗𝙖𝙣𝙜𝙖𝙧𝙚 𝙮𝙖𝙮𝙞 𝙠𝙖𝙢𝙖 𝙙𝙖 𝙧𝙖𝙮𝙪𝙬𝙖𝙧 𝙧𝙖𝙣𝙞 𝙩𝙤 𝙖𝙧𝙖𝙨𝙝𝙞 𝙣𝙚 𝙖𝙠𝙖 𝙨𝙖𝙢𝙪.𝙂𝘼𝙍𝙂𝘼𝘿𝙄𝘽𝙖𝙣 𝙖𝙢𝙞𝙣𝙘𝙚 𝙠𝙪𝙢𝙖 𝙗𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙢𝙞𝙣𝙘𝙚 𝙖 𝙨𝙖𝙧𝙧𝙖𝙛𝙖 𝙢𝙞𝙣 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞 𝙩𝙖𝙠𝙤 𝙬𝙖𝙘𝙚 𝙨𝙞𝙜𝙖 𝙗𝙖 𝙩𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙞𝙯𝙞𝙣𝙞 𝙣𝙖 𝙣𝙞 𝙢𝙖𝙧𝙪𝙗𝙪𝙘𝙞𝙮𝙖 𝙗𝙖, 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙢𝙖𝙡𝙡𝙖𝙠𝙞𝙣𝙖 𝙣𝙚 𝙣𝙞 𝙠𝙖𝙙𝙖𝙞.𝙁𝘼𝙏𝘼𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 𝙮𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙣𝙖 𝙛𝙖𝙧𝙖 𝙡𝙞𝙩𝙩𝙖𝙛𝙞𝙣 𝙣𝙖𝙣 𝙠𝙖 𝙗𝙖𝙣𝙞 𝙞𝙠𝙤𝙣 𝙜𝙖𝙢𝙖 𝙨𝙝𝙞 𝙡𝙖𝙛𝙞𝙮𝙖 𝙗𝙖 𝙩𝙖𝙧𝙚 𝙙𝙖 𝙣𝙖 𝙧𝙪𝙗𝙪𝙩𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙞 𝙖𝙗𝙪 𝙬𝙖𝙣𝙙𝙖 𝙯𝙖𝙞 𝙯𝙖𝙢𝙚 𝙢𝙖𝙣𝙞 𝙠𝙖𝙡𝙪𝙗𝙖𝙡𝙚 𝙠𝙤 𝙢𝙖𝙩𝙨𝙖𝙡𝙖 𝙗𝙖🤲.𝘿𝘼𝙉𝙂𝘼𝙍 𝙒𝙐𝙏𝘼 🔥   𝘽𝙊𝙊𝙆 𝙊𝙉𝙀 📖1001*******(Manzon Allah S.A.W ya ce. "Ba ƙarfi bane jarunta lallai abin da ke jarunta shine mallakar zuciya a yayin fushi.")*******Shimfiɗar labari.   Da gudu motar ke cin hanya, yayin da iska ke kaɗa bishiyoyin da suka yiwa hanyar ƙawanya da matsanancin ƙarfi, ta yanda ganyayyaki ke kaɓaɓɓowa musamman waɗanda suka bushe zuwa ƙasa, ƙoƙarin matsa sitiyari ya ke da sauran ƙarfin daya rage ma shi, amma duk ƙoƙarin shi ya kasa, kwatsam motar ta sake cin karo da wata babbar bishiyar nan take motar ta soma jujjuyawa tana dukan bishiyoyin gaba da bayanta.   Bai sare ba ya sake ƙoƙarin taka burki a karo na babu adadi sai ina motar ta rigada ta zame saboda gudun da take yi tana kai karo ko ina.   Yayin da tayoyi suka yi ƙara tare da jan ƙasa me razanarwa motar na tafiya streight ta wata hanya me duhuwa saboda bishiyun da suka lulluɓe.   Cikin rashin abin yi ya riƙe belt amma kuma lokaci ya riga da ya kure lokacin wanzuwar ƙaddara marar tsammani ya soma.   Cikin daƙiƙu kaɗan motar ta yi mummunar karo da abin da ya zama na ƙarshe kuma maƙurar hanyar da take tafiya, Airbag ya buɗe nan takr da ƙarfi glashin gana ya tarwatse, hayaƙi ya soma tashi daga ƙarƙashin bonet, ƙahon motar ya ci gaba da ƙara ba tare da tsayawaba.    Nan take sauran ƙwarin gwuiwar daya ke da shi ya idasa rushewa, rintse ido yayi da ƙarfi yana jiran wa'adin wanzuwar ƙaddara, ƙarar da motar ke yi na cike ƙofofin kunnuwan shi suna hana masa jin sautin komi.   A hankali ganin shi ya soma ɗaukewa jin shi yayi nisa sosai ta yanda ba...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play