FARASHIN RAYUWAFree

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

FARASHIN RAYUWA

  • 1views
  • 13chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · BABI NA ƊAYA — M-ARROW

AbujaKatafaren fili ne da ya ƙunshi wani babban ɗakin taro na musamman mai suna The V.I.P. Imperial Conference Hall. Wuri ne da aka tsara daki-daki cikin tsarin zamani, cike da dukkan manyan kayan more rayuwa da fasahohin da suka dace da tarukan manyan shugabanni da attajiran duniya.Daukacin mutanen da ke cikin zauren taron sun maida hankalinsu gaba ɗaya kan wata katafariyar na'urar sadarwa ta zamani da ke manne a bangon gabashin ɗakin, wato The Smart Interactive Holographic Display.A gabanta kuwa, Comrade Aliyu A. Manga, The Deputy Director of Human Rights Commission, ya tsaya daram cikin cikakkiyar ƙwarewa, yana gabatar da bayanai masu cike da hujjoji da ƙididdiga. Yana nuna bayanai da yatsansa a kan holographic display ɗin, yana bayyana yadda sabon tsarin zai gudana da kuma amfanin da zai haifar wa al'umma.A gefe guda kuma...Shi yana zaune cikin zallar ƙasaita da cikakkiyar nutsuwa.Ya jingina faffaɗan bayansa da lallausar kujerar fata ta alfarma, yana ɗan lila jikinsa a hankali. Lokaci zuwa lokaci yana juyawa kaɗan hagu da dama, kamar wanda babu abin da ya dame shi.Ƙafarsa ɗaya tana kan ɗaya.Idanunsa kuma a lumshe suke, tamkar mai barci.A tsakanin dogayen yatsunsa masu ƙarfi kuwa, yana sarrafa wani tsadadden Golden Executive Pen, yana juyawa cikin natsuwa kamar wani abu da ya saba yi.Duk da cewa idanunsa a rufe suke, babu kalma ko guda daga cikin bayanan da ke kubuce masa.Kowace magana...Kowace hujja...Kowace gardama...Duk suna shiga kunnuwansa daki-daki.Sai dai duk mai lura da yadda jijiyoyin wuyansa suka fito suka miƙe, da yadda yake matse muƙamuƙansa lokaci zuwa lokaci, zai fahimci cewa ba kwanciyar hankali ne ke lullube shi ba...A'a.Wani irin tafasasshen fushi ne da ke ci gaba da taruwa a zuciyarsa, yana jiran lokacin da zai balle.Ba zato ba tsammani...Ɗaya daga cikin manyan attajiran kamfanoni ya miƙe tsaye cikin isa da nuna ƙarfin iko. Ya zaro idanu, sannan ya katse bayanin da Comrade Aliyu A. Manga yake yi.Cikin kakkausar murya ya ce:"What kind of nonsense policy is this? Me ake nufi da wannan tsarin? Bayan mun riga mun sauke farashin kayayyakinmu a baya, yanzu kuma ana so mu sake rage wani sabon farashi? No! This is absolutely impossible! Idan manufarku ita ce ku kassara kamfanoninmu, ku durƙusar da tattalin arziƙinmu, then forget it! Ba za mu taɓa amincewa da irin wannan tursasawar ba. If the poor can't afford our products, let them work harder and make more money. Amma mu kam ba za mu yi asarar biliyoyin Naira saboda wani sentimental decision ba!"Da jin waɗannan kalamai masu cike da raini da rashin mutunci, Comrade Aliyu ya dakatar da bayaninsa.A hankali ya juya ya kalli mutumin.Sai dai kafin ya yi magana...Idanunsa suka sauka kan mutumin da har yanzu yake zaune cikin nutsuwa.Har yanzu idanunsa a lumshe suke.Amma kallo ɗaya kacal da Aliy...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters13
premium0
01

BABI NA ƊAYA — M-ARROW

Free sample
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play