FreeArewaPen original
A TSAKANIN ZUCIYA DA KADDARA
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Narrator, Producer, Audio Novel Editor
Sample · Tushen Ƙaddara
A TSAKANIN ZUCIYA DA KADDARA_Aiimar Voice/Talk_*01*A ciki. Wata ranar Litinin ce, ranar ba ta da zafi sosai, iska kuwa tana kadawa a hankali tana motsa ganyen bishiyoyin mangwaro da ke tsaye a bakin gidan. Hayaniyar yaran unguwar ta cika ko'ina; wasu suna tsalle tsalle, wasu suna buga ƙwallo, wasu kuma suna guje-guje suna ta nishadi da murna.A tsakiyar wannan hayaniyar ne wani ƙaramin yaro mai kimanin shekaru takwas ya fito daga cikin gidan su, riƙe da wata ƙaramar leda a hannunsa.Sunansa Abdurrahman, amma kusan kowa a unguwar yana kiransa da Aiimar.Aiimar ba shi da yawan magana. Yaro ne mai natsuwa, wanda ko da yake yana cikin yara masu hayaniya, ba kasafai yake shiga rigima ba. Idan aka samu matsala, shi ne na farko da zai yi ƙoƙarin sasanta su.Ya tsaya a ƙofar gidan yana kallon yaran da ke wasa.Sai ya ga wata yarinya ta fito daga gidan da ke ƙetaren hanya.Tana sanye da wata doguwar riga mai launin ruwan hoda, kanta a ɗaure da ɗan ƙaramin mayafi. Hannunta ɗauke da kwandon roba, yayin da take kallon yaran da ke wasa.Sunanta Shamsiyya.Amma saboda ita ce autar gidansu, kusan kowa yana kiranta da Autar Mama."Aiimar!"Muryar ɗaya daga cikin yaran ta katse tunaninsa.Murmushi yayi sannan ya kallesa "Zo mu buga ƙwallo!"Aiimar ya juya ya kalle su yace "Ku fara, zan zo."Ya sake maida kallonsa akan Shamsiyya.A wannan lokacin kuwa ita ma ta ɗago kai cikin murmushi suka kalli cikin idanun juna.Shamsiyya ta saki wani murmushi.Aiimar kuwa sai yayi saurin kawar da kansa kamar wanda aka kama yana aikata wani laifi."Me ya sa kake kallonta?"Wata murya ce daga bayansa take tambayarsa, Aiimar ya juya da sauri cikin tsoro, Ɗan uwansa ne, Salisu, yana tsaye yana dariya."Ba kallonta nake ba." Aiimar ya amsa fuskarsa a yamutseSalisu ne ya sake tambayarsa "To me kake yi?""Ba Komai." Aiimar ya amsa yana sake maida kallonsa a kan Autar Mama Salisu ne ya ƙara fashewa da dariya."To ka daina kallon Autar Mama dai."Aiimar ya daure fuska. "Ni ba kallonta nake ba.""To shikenan." Salisu ya amsa sannan ya juya yana tafiya, waigowa yayi sannan ya ƙara da cewa "Amma dai kasan na gan ka ko."Aiimar ne ya ɗauki ƙaramin dutse ya jefa masa, kaucewa Salisu yayi sannan ya ruga da gudu.A gefe guda kuma juyawa Shamsiyya tayi ta shige gidan su."Autar Mama!"Mahaifiyarta ta kira ta daga cikin ɗaki."Na'am Mama.""Kin kai wa Babanku maganin da ya ce ki kai?""Na kai." Autar mama ta amsa"To zo ki taimaka min."Shamsiyya ta ajiye kwandon sannan ta zauna kusa da mahaifiyarta."Mama..." Shamsiyya ta kira mahaifiyarta tana murmushi."Na'am Autata"Shamsiyya ce ta nisa sannan tace "Yau Aiimar ya zo."Mahaifiyarta ta kalle ta tace "Aiimar?"Gyada kai shamsiyya tayi tace "Eh.""To me ya faru?" Mama ta tambayeta tana murmushi"Ba komai." Shamsiyya ta amsa tana saukar da kanta kasa, Ta yi shiru.Mahaifiyar ta ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.