FreeArewaPen original
MASIFAFFAN NAMIJI
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 001
*MASIFAFFAN NAMIJI..!*****:Jamilaumar315**Arewa:JamilaumarJanafty*_Bismillahir rahmanir Rahim in the Name of Allah, the most Beneficent The Most mercefull Praise be to Allah Lord of The Words..._*BA SABON LABARI BA NE REPOSTING NE BAN SAUYA HARAFI KO ƊAYA DAGA CIKIN LABARIN BA**001**ZARIA..*Area:Tukur-Tukur...'"Hafsah!...Hafsah...!Hafsah...! sunan danaji Megidana Abdullahi na Tsagamin shi da Asuban fari,wanda hatta mazan da suke wucewa ta kofar gidanmu in sun dawo Daga masallaci suna iya Jiyo kwakwazon Kiran Sunana da Abdullahi keyi muryansa Kakkausa kamar zata tsaga gidan.Kai ta ta Dafe tana Daga Durkushe acikin karamin Kichen din su Dake tsakar Gida tana Faman kunna Risho sai ta kunna Lagwanin sai ya mutu da kanshi Tun Wajen 6 da wani abu na safe ta Fito tana idar da sallar Asuba ba ta ma yi Tunanin komawa ba Saboda yau din Litini ne farkon Sati Su Amira nada Makaranta kada su makara Abdullahi ya Dora Laifin akanta Tunda tare yake Wucewa dasu in zai tafi aiki Bisa Mashin Dinsa mai Suna Wayyo Kudina.Saurin Mikewa tayi Jin kiran yafara Kusanto ta kada ta Kular Dashi dogon Sikat din Jikinta ta gyara Lokaci daya da Hijabin da ta yi sallah wanda ba ta cire ba Jin garin yau din an Tashi da sanyi sanyin Damuna dayake Jiya an kwana Tsala ruwa,tana kokarin Shiga Dakin suka ci karo Dashi zai Fito,Da Sauri ta yi baya tana Raba Ido Cikin Kulufuwa da Takaichi yake Jifanta da wani kallo kafin ya Daga Murya yana Fadin"Wani sabon Iskanci kuma kika samo Hafsah..!?Muryanta cikin Sanyi ta ce"Name fa Abban Amira..? Harara ya wurga mata yana Fadin''Bansani ba..Nace bansani ba bandama Salon iskanci kira nawa nayi miki Tun ina Daga cikin Daki baki amsa ba sai da na Fito..? Yafada yana wani karkace tsayuwa Cikin Jin Haushinta,Ajiyar Zuciya ta sauke kafin ta kada kai kawai ta wuce shi Zuwa Cikin Dakin bayanta yabi yana Fadin"Hafsah ina mgana kina Tafiya..? Yafada cikin Mamakinsa.Atsakiyar Falon Taja ta tsaya tana Fadin"A"a kayi Hakuri ba Tafiya nayi ba na Shigo Daki ne kada makota su jiyo Fadanka,mganar kuma Kira banji bane Lokacin danaji na amsa kenan zan taho Dakin sai ga ka kayi Hakuri.."Tafada Cikin Sanyin Murya Kawai Tsayawa yayi yana Kallonta cikin Fada,sai yanzu na karemai kallo Dogon Namiji ne mai Cikar zati da kamala mai Fadin Kirji da cikar Cikakken Da Namiji mai iko Ba fari bane ammh Wankan Tarwada ne,Fuskarsa bata da Tsawo sosai sai dai tana da Fadi kadan Hancinsa Dogo ne Turbarkallah Masha Allah Sajensa daya zagaye bakinsa shi yake karamai kyau da Kwarjini.Abdullahi Usman Direba kenan Dan Misalin Shekaran Haihuwan 32 da biyu Aduniya Mai iko ne kuma mafadacin Namiji ne ga iyalansa bai da sauki ko kadan Ballatana Ragowa a kallan Farko in kayi mai bazaka taba Zaton Abdullahi ya iya Fada ba ammh Ranar dakayi katarin zuwa gidansa nan zaka ga Abunda ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.