FreeArewaPen original
ZARGEN ƘAYA
- 1views
- 41chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm writer ✍️✍️✍️
Sample · 1
*ZARGEN ƘAYA* *NA**AYSHER ANGEL*Page 1WhatsApp ****The Fractured Bond: When Resentment Runs Deep And Innocent Pay The Price...**Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina hukunta wasu akan laifin wasu? Shin har sai yaushe ne mutanen yau zasu daina wasarairai da zumunci akan son zuciya ko kuma dalilin da bai taka ƙara ya karya ba? Komai girman laifin da mutum yake ganin anyi mashi ai sulhu alheri ne bugu da kari zumunci ba abu ne da ya kamata ayi wasarairai dashi ba*Daga inda nike zaune shurum ina iya jiyo maganata da ake yi wacce ba magana bace mai ɗaɗi a kunnuwa da zuci musamman ga wanda aka jefa da su, kalamai ne masu wahalar mantawa ga wanda aka furtawasu. Dangin mijina mai rasuwa suna aibatani akan abun da ya faru tun kafin aurena da shi. Zaman gaisuwa da ya kamata su yi mashi addu'a ni kuma su nuna min tausayawa akan wannan iftila'i da ya faru amma sai suka zabi maido maganar da ta riga ta wuce a tsakanina da shi.Na saka hannuwana akan karamin cikin da nike dauke da shi ina ayyanawa a raina koda abun da za su yi min zai fi haka bazan yarda wannan zumuncin nasu mai wahalar sha'ani ya ƙara lalace ta dalilina ba saidai kuma kamar yadda hausawa suka ce idan an ciza a hura.Tun kafin a haifi mijina mai rasuwa madakalar wannan zumuncin take wacce har wani ba ya son a dangantashi da wani, har ta kai ga matakin da wasu suke shan wahala akan laifin da aka aikata tun kafin a haifesu.Tunda har suka nuna kulafuci akan ɗan da yake cikina ni kuma zanyi amfani dashi in gyara wannan zumuncin nasu mai wahalar sha'ani tamkar TABARMAR ƘASHI.Dama ina da tabbaci akan ba zasu barni da abun da na haifa ba, kuma ba zan hanasu ba, da hannuna zan ɗauki yaron in basu ina da tabbaci akan duk yadda za su yi ƙoƙarin cusa tsanata a ransa idan ya mallaki hankalinsa ya ji abun da ya faru zai gane cewa bani da laifi and the fact that nice wacce aka yi wa laifin.Zumuncin dai da suke son lalata da kuma fitina da suke son ayi ni Rumana ba zan bari a samu tangarda daga wajena ba saidai idan abun ya fi karfina. Namiji ne ko mace idan na haifa suka amsa zan bar masu domin na san komai daren dadewa zai neme uwarsa mahaifiya wannan abu ne da basu isa su hana ba.Zumunci abu ne mai girma don haka na yarona da dangin ubansa ko kuma dangina ba zan bari ya samu nakasu a saboda rashin hakurin dangin mahaifinsa ba, komai za'a yi min zan yi hakuri domin shi hakuri ba ya faduwa kasa banza, Allah yana sane da ni kuma zai kawo min mafita.Lamarin mutanen yau yana bani matuƙar mamaki da tu'ajjibi da har wasu lokuttan nike jina kamar wacce ta kamu da ciwon MUTUWA A MAƘOSHI koda yake shi HAWAYE AKAN RUWA idanun da suke fitar da shi ne kawai suka san raɗaɗi da kuncin da ya ke fita da fitarsa, kamar ZANE AKAN RUWA ne mai wahalar gane kamanni.Shin har sai yaushe ne mutanen ya...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.