FreeArewaPen original
MATAR BELLO
- 1views
- 24chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm writer ✍️✍️✍️
Sample · 1
*MATAR BELLO.*_The Bride Who Brought Chaos_By Aysher AngelPage 1*When What Was Meant to Be Joy Became Trouble?**** ***Amaryar Bello...Fara ce sol har yellow fatarta take saboda haske, tana sanye da expensive Egyptian Abaya wacce ta matuƙar suiting dinta tayi matuƙar kyau kamar a sace a gudu, saidai hakan bai saka wautarta da kauyancinta sun gushe ba, kyawun da tayi daban, wautarta da kauyanci daban.Duhu ne mamaye da falon, a hankali ta turo ƙofar ta turo kanta tana leƙe kamar wacce take tsoron leƙa ƙarƙashin kabari.Ta tsaya cak ta ja lumfashi a hankali kamar wacce ta shigo gidan da yake cike da ifiritun aljanu, ta sake leƙawa Idanunta suna yawo a cikin falon, zuciyarta na bugawa kamar ana dukan gangar waka a tsakiyar taron bikin aure. Ta sake tura kanta kaɗan, ta ɗaga ƙafarta ɗaya, sai kuma ta dawo da ita baya."A’ah, idan wani abu ya fito fa?" ta raɗa wa kanta.Ta ɗaga ƙafarta a karo na biyu, ta taka. Ƙarrrrr! ƙofar ta yi ƙara.Ta zabura kamar an ce mata 'kama ta!..' Ta dafe ƙirji idanunta a waje."Na shiga uku, wannan ƙofar sai da ta tona min asiri," ta faɗa a zuciya.Ta sake leƙawa, babu motsi, shiru kamar an zuba ruwa ƙasa ta shanye.Babu zato babu tsammani ta ji wata ƙara daga kusurwar falon: ƙuuuu... ƙuuuu...Ta tsaya cak ta zaro idanu tana tarababbi gashi kishirwa takeyi ba kaɗan ba ballantana ta juya ta koma dakinta.Ta ƙara jin ƙara: ƙuuu... ƙuuu..."Wayyo! Wannan murya ba ta mutane ba ce, mutanen ɓoye kuyi haƙuri ruwa kadai zan sha in koma inda na fito," Ta furta a hankali tana takatsantsan kada ta motsa domin a wannan lokacin motsin motsawarta kanshi tsoro yake bata.Ta ƙara matsawa ciki tana tafiya da sanɗa kamar barawon da ya shiga sata gidan gardawan maza.Tana tafiya, sai ta taka wani abu a ƙasa caaak. Ta yi tsalle sama kamar an jefa ta da spring."Na shiga uku! Wane irin abu ne wannan kuma?" Ta sunkuya da rawar jiki, ta taɓa, ashe takalmi ne.Taja siririn tsaki, "Mtseew! Takalmi ya kusa sakawa in gudu in bar ƙafata a nan," ta ƙarasa maganar tana girgiza kai.Sai ta sake jin ƙuuuu... ƙuuuu... amma wannan karon da ƙarfi.Har tayi ready ta tattara rigarta da nufin ta koma ɗakinta a tamanin sai kuma taji shiru babu ƙarar.Ta saka ƙafarta tana tafiya tana haskawa da touch, tana neman inda za ta samu fridge ta sha ruwa domin kawar da kishirwar dake ragargazar maƙoshinta.Yadda take tafiyar kansa tako ne na wanda yake a tsoro ce, kafarta ɗaya gaba, zuciyarta uku baya.Ta ɗaga touch ɗin sama, hasken ya haska bango, inuwarta ta motsa."Wayyo!" Ta fasa ihu ta juya da sauri, ashe inuwarta ce.Ta girgiza tana faɗin, "Ke dai Bulkuma matsoraciya ce kina neman ki tsorata kanki da kanki."Ta ci gaba da tafiya a hankali, tana baza idanu kamar mai neman zinariya a tumun dare. Kishirwa na ƙara matsa mata, makogwaronta kamar an shanyashi a rana."Wallahi idan na ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.