FreeArewaPen original
MATUKAR INA RAYE
- 1views
- 31chapters
- 2audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Matukar Ina Raye 1
MATUƘAR INA RAYEWriter — MRS ISHAM *** ***.~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM~Page 01Iskar hunturu mai sanyi tana kaɗawa a hankali, tana ɗauke da ɗan ƙurar da ta lulluɓe sararin samaniya. Titunan garin sun yi duhu, sai hasken fitilun gidaje da na motocin da ke wucewa lokaci zuwa lokaci suke karya wannan duhun. Duk inda ka kalla, akwai wani irin hazo mai duhu da ya rufe komai. Hasken fitilun tituna ba ya haskakawa yadda ya kamata, sai dai ya fito cikin ƙurar kamar wani ɗan ƙaramin haske da ke ƙoƙarin yaƙi da duhun dare. Gidaje sun rufe ƙofofinsu da tagoginsu.Tafiya ta ke a hankali, hannunta ɗaya riƙe da wayarta, ɗayan kuma ta matse gefen mayafinta da yake ƙoƙarin kubucewa saboda iska. Idanunta suna yawo daga wannan gefe zuwa wancan, kamar wadda take fatan ganin wani mutum a duk lokacin da ta ɗaga kai.Amma babu kowa.Ta tsaya tana duba wayarta, sai dai babu kira balle saƙo. Ta ɗaga idanunta sama, ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.“Waheeda…”Ta furta sunan a hankali, hawaye na zubowa daga idanunta. Ta sa hannu ɗaya ta share su.“Ya Allah… ina ne inda wannan yarinyar ta shiga? A ina zan samo ta?”Ta tambayi kanta, kuka na ƙoƙarin kubuce mata. Wani dakali ta hango, jikinta a sanyaye ta ƙarasa wurin, ta zauna, sannan ta soma rera kuka.A lokacin hunturu, abin da aka fi buƙata shi ne abin da zai bayar da ɗumi ga jiki. Ba jiki kaɗai ba, hatta cikin mutum yana buƙatar wani abu mai ɗumi domin ya ji sauƙin sanyin da ke ratsa kowane sashe na jiki, ciki da waje.Majalisa ce. Magidanta da samari suna zaune a kusa da wata wuta da suka hura, tana ci a tsakiyar inda suke zaune, su kuma sun kewaye ta suna jin ɗumin da ke ratsa jikinsu. Ga kuma shayin da suke sha suna hira cikin natsuwa, kowa hankalinsa kwance.“Kamar ina jiyo sautin kuka,” wani saurayi daga cikinsu ya faɗa.Hakan ya sa suka yi shiru, suka kasa kunne. Ai ko ba ƙarya ya yi ba, tabbas su ma kunnuwansu sun jiyo musu wannan sautin kukan.Wani magidanci ya furta, “Je ka dubo waye yake wannan kukan, sannan ka zo da shi.”Bayan tafiyarsa da ’yan mintuna, sai ga shi ya dawo majalisar tare da ita. Da mamaki suke kallonta, suna tambayar kansu me ya fito da ita a wannan lokacin na dare da sanyi.“Yarinya, ke kuwa me kike yi a nan? Daga ina kike? Yaya sunanki?”A maimakon ta ba su amsa, sai kawai ta sanya kuka tana rufe fuskarta da gefen mayafinta. Jikinsu ne ya yi sanyi, tausayinta ya kama su. Hakan ya sa suka bukaci ta zauna, sannan suka samu suka lallashe ta har ta yi shiru.“Amma ke ba ’yar wannan unguwar ba ce, ban taɓa ganinki ba.”Kai ta gyada masa alamar eh. Mutumin ya jinjina kai.“Sani, ba ta shayi ka ji,” ya umarci matashin da ya zo da ita.Bayan ya ba ta shayin, sai matashin ya ce, “Kanwata, na san ba ƙaramin abu ba ne zai sa ki bar gida a wannan lokaci...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.