5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUARFree

ArewaPen original

General fictionFreeCompleted

5TARS CHRONICLE End Book 4 CENTUAR

  • 1views
  • 18chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

About the author

NobleWriter

More from @xayyeesherthulhumaerath

Sample · CHAPTER 1

MABUƊIDuniya da mutanen da ke kewaye cikinta sun jima yi mini kaura tun ina shakar matsakaiciyar iska a cikin mahaifiyata,a lokacin da ko numfashi ban taɓa yi a cikin duniyar ba.Abun mamakin sai ya zamto harda wanda ya zama silar kasancewar rayuwata a cikin cikin ma'ana mahaifina!Me muka aikata?Me muka yi wanda ba daidai ba?Shin Musuluntar da mahaifiyata tayi tare da sadaukarwa shi ne ya zame mana tikitin siyan rigar da za a wofantar damu?In danginta kirista sun gujeta domin bijerewa umarni da addininsu da ta yi.Kuma suma musulman sai kyamacemu,saboda daga mara sallah ta dawo mai sallah?Abar ƙyamace?Abar guduce?Abar kyamatace?Ba ma wannan ba to ni kuma mene ne laifina?Aa!Addinin musulunci bai koyar da haka ba,hasalima ya nunar da a kyautattawa kowanni Ɗan Adam ko da kuwa ba musulmin bane,bare kuma wanda ya musuluntar.Tabbas mahaifiyata jarumace da ke iya juriya,jajircewa hakuri tare da sadaukarwa wajen tabbatuwar rayuwata a duniya ba tare da taimakon kowa ba kuma ba tare da jin cewa hukuncin da ta yanke na kasancewarta a musulma laifi bane.Ban da wata jarumar da ta zarce ta domin kuwa ta kara gasgata babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, a lokacin da take da tsananin bukatar taimako ta kauda kanta ga duk wata hanya da zata iya sauya mata kudirinta,ta rayu ita kaɗai,cikin kadaici,talauci da tsanani har zuwana duniya kuma ta ɗaurani akan Addinin musulunci ba tare da wani tantama ko jin cewa ba a kyauta mata ba,illa kara nuna mini d take lallai duk rintsi ka da in bari zuciyata ta yi galabar rabani da addinin gaskiya.Yanzu na girma na mallaki hankalin kaina na yi karatu kuma na san daraja da kimata ina son rama juya mun baya da duniya da mutanen cikinta da suka yi tun kafin zuwana cikinta ta wata sigar da ni kadai na san mai nake aikata,to amman kuma sai ana yi mini kallon mara adalci? mara gaskiya kuma macuci? Aa sam ba zan fasa ba na tabbata akwai tarin mutanen da ke fuskantar irin kalubalen da ni da mahaifiyata muka fuskanta.....☆☆☆MalaysiaKwance Farouq ya ke a cinyar mahaifiyarsa tana shafa gashin kansa,kamar an tsikaresa ya tashi ya zauna yana kallonta."Lafiya?"Maah ta furta.Murmushi ya yi kafin ya ce,"Maah."Ta amsa da ,"Yes me ya faru?"Farouq ya ce,"me yasa duk da cewa sanadin shiga musulunci duniya da mutanen cikin ta suka juya miki baya amman kin gagara fita daga ciki?"Numfasawa ta yi ita ma ta saki wani Murmushi kafin ta ce,"Dalilan suna da yawa amman kuma kafin nan ina so in fara sheda maka cewa babu wani ingataccen addini fiye da muslunci domin kuwa shi ne haƙiƙanin addini na gaskiya ba tare da sirki ba, duk zuciyar da ta shaƙu da musulunci zai yi mata matukar wahala ta iya fita cikin sauki,kuma duk idanun da ya yi tozali da hasken musulunci ba zai taɓa iya bari ya rufe idanunsa ba domin komawa duhu ba,duk da cewa na wahaltu na azabtu kuma ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters18
premium8
11

CHAPTER 11

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
12

CHAPTER 12

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
13

CHAPTER 13

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
14

CHAPTER 14

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
15

CHAPTER 15

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
16

CHAPTER 16

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
17

CHAPTER 17

Premium
Updated 2 months agoAvailable now
18

CHAPTER 18

Premium
Updated 2 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play