BAYAN HANZARIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

BAYAN HANZARI

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

I am Khadijah Sulaiman, a writer who finds beauty in turning imagination into stories. My pen explores love, betrayal, suspense, family, traditions, and the complexities of human emotions. I write to entertain, inspire, and leave readers with stories that linger long after the fi...

More from @khadijahsulaiman406

Sample · PAGE ONE

BAYAN HANZARIKHADIJAH SULAIMAN  *Labarin "BAYAN HANZARI kirkirarren labari ne,idan yayi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.**Bismillahirrahmanirrahim**Page 1*    Tsaye take a gaban dogon wardrobe ɗin gabanta,gyara kayan ciki take a tsanake,a nutse take aikin nata ba tare da wani gaggawa ba.Ta share a kalla mintuna kusan goma kafin ta maida murfin wardrobe ɗin ta rufe.Ƙara bin ɗakin nashi ta ke da kallo ko da akwai wani abin da yayi saura da za ta yi,ganin babu wani abinda ɗakin ke bukata yasa ta shiga takawa a nutse ta fita.Tana fitowa parlourn idonta ya sauka a tangamemen agogon dake manne mai zanen adon ɗawisu daya ƙarawa parlourn wani kyau da haske.A hankali ta buɗe baki tace"subhanallah,ashe lokaci ya tafi haka?"Da ɗan sassarfa ta wuce nata d'akin,kayan jikinta ta cire ta d'auro towel ta shige toilet.Ta ɗan jima a ciki kafin ta fito ta jawo stool dake gaban mudubin ɗakin ta zauna.Sosai take ƙarewa kanta kallo cikin madubin,kasa haƙura tayi da abinda take gani ta ɗago hannunta na hagu tana taɓa kashin wuyarta.Fashewa tayi da wani kuka mai cin rai,saida ta shafe a ƙalla mintuna goma tana abu ɗaya kafin ta sarara ta mike tare da kokarin barin wurin.Jirin dake shirin zubar da ita yasa tayi saurin komawa ta zauna tana dafe kanta.Saida ta d'an huta na wasu mintoci kafin a hankali ta kara miƙewa ta karasa ta buɗe wardrobe ko gani ba tayi sosai ta jawo wasu silk kayan bacci armless riga da dogon wando.Komawa jikin madubin tayi ta shafe jikinta da turare ta haye gado ta kwanta don wani azababben ciwo kanta keyi tamkar zasu fad'o.Cikin bacci taji horn dinshi tare da buɗe gate ɗin kusan lokaci ɗaya.Juyo da fuskarta tayi ta jawo wayarta dake gefen bed side lamp ta kunna press button tare da kokarin duba lokaci.Karfe sha ɗaya da minti sha takwas lokaci ya nuna mata sai kawai ta maida wayar ta ajiye tare da lumshe ido.Da ƙyar ta miƙe ta zauna tana jin kanta tamkar  zai rabe biyu.A daddafe ta fito daga ɗakin tana ƙara gyara hular kanta.Ɗakinsa ta nufa ganin babu kowa a parlourn illa kamshin turarensa da ya gama cika wurin.Tana murɗa ƙofar tayi sallama a hankali tare da maida shi ta rufe.Yana tsaye yana ƙoƙarin cire links ɗin rigarsa da wayarsa dake dafe da kafaɗarsa dake nuni da magana yake a wayar ya juyo ya mata kallo ɗaya ya kauda kai."Idan na fito daga wanka zan kira ki".shine kawai abinda yace ya kashe wayar tare da  ajiyeta saman gadon dake shimfiɗe da white bedsheet ya cigaba da abinda yake.Bahiyya tayi kokarin danne abinda ke tokare saman kirjinta tace "Sannu da zuwa".Da kyar ya buɗe baki tamkar wadda akayi wa dole yace"Yawwa".Zama tayi gefen gadon ba tare da ta ƙara cewa komai ba har ya gama cire kayan ya wuce toilet, ta bishi da kallo hawaye na kara gangarowa daga kyakywar fuskarta.Ƙarar shigowar sako yasa ta...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play