FreeArewaPen original
SOYAYYAR ZUCI
- 1views
- 26chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
MY BEST FRIEND'S DAD
Sample · Chapter 1&2
💖💖SOYAYYAR ZUCI💖💖 (love and Romantic) Written By DeeyamerhPage 1&2" Hey plz ki kula" taji saukar murya a bayanta . Cikin sauri ta juyo saboda " Hey " da taji an sake ce mata . kyakkyawan saurayi ne sanye da bakar jallabiya,wacce ta amshi fatar jikinsa, matashin saurayin fari ne sosai , me dauke da bakin saje da lallausar gashin kai.meko mata wayarta yayi,da sauri ta kalli jakar ta domin tasan ta sakata a jakarta,hannun da ya Miko mun wayar nake kalla,shin a ina ya samu wata?ko me yankan Aljihu ne?duk wannan tambayar a xuciyarta takeyi.“Ta faɗo daga jakarki ne” ya ce ganin yadda fuskanta ta nuna alamar tambaya A hankali tasa hannun ta karba, Domin abin yabata mamaki, yadda rayuwar nan ta lalace waye zai tsinci waya, ya baka sai me tsoran Allah.“Thank you.”ta fada cikin siririyan muryantaYa yi murmushi kawai."Suhaima" ya anbaci sunanta . cikin mamaki ta daga idanuwanta,ta kall kalle shi ganin yadda ya ambaci sunanta kai tsaye sai kuma kawai taiyi murmushi ba tare da tace masa komai ba.gira daya ya dage yana kallon ta, kallo ne da takasa gane me yake nufi.“Eh.” ya furta da murmushi akan labbansa“Daga ina" ta sake tambayarsa""hmmm idan lokaci yayi zaki sani,domin nasanki Fiye da yadda kike zato.”kallonsa tai na yan mintuna , kamar ba zatayi magana ba sai kawai ta furta " Okay ," Sannan ta juya ta bar wajan. batare da ta bari ya sake magana ba " Hey bakiji ba." yayi kokarin dakatar da ita . " Please, jira na ake a gida , bazan iya tsayawa a hanya ba, ina magana da kai ba sabida za'a mun fada a gida .""Haka ne na fahimta , amma idan ba damuwa anjima zan iya zuwa gidan ku? Saboda akwai maganar da nake so mu yi."" No Please " ta fada cikin sauri , sannan ta bar wajan ba tare da ta bari ya sake magana ba .dan tsayawa yayi jim , yana kallan wucewar ta , kafin ya sosa kansa kadan yana murmushi shi kadai. Suhaima kuwa har sauri sauri ta dinga yi saboda karya tsayar da ita ga xuciyarta da take faman bugu ba tare da tasan dalilin hakan ba .--------------------------Wa shegari da safe, da wauri suka shigo makaranta,domin suna da lecture kuma gashi malamin har in dai kabari ya shigo cikin class din, to sai ka jirashi a wajen har ya gama.tana zaune a aji tana duba Assignment din da akaba su,sai taji Muryar kawarta Fatima akan ta tana fadinq"Ahh Suhaima da wuri haka? ko da yake wanda yace bayaji,ai Sir Ridwan shine maganinsu..""wllh Fatima baki da mutunci ko banza ai na ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.