HALINSA!Free

ArewaPen original

HumorFreeOngoing

HALINSA!

  • 1views
  • 4chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

A.k.a Candy 🦋 Student Midwife 🌺 Writer ✍️ Graphic designer🪄 Muslimah 🤲 Proudly Nigerian 🇳🇬 Kuma Bahaɗejia🐎.

More from @salmaahmadisah

Sample · Page 01

HALINSA!© SALMA AHMAD ISAH*SADAUKARWA*Wannan littafin sadaukarwa ne zuwa ga Rabi’atu Abubakar (Pinky) A gift filled with love from your lilly, Thanks for your support prayers and love. ~Gaisuwa~Gaisuwa ta musamman zuwa ga Khadeeja Abubakar Alkali (Khadeeja Candy) a.k.a Oum Namra, Fatima Yakubu, Fatima Ahmad Isah, Amina I. Ibrahim (Nanameera), Jamila Umar (Janafty). Allah ya bar tare.بسم الله الر حمن الر حيم*Page | 01Aure! A 'yan kananan shekarun a take da su duniya, wanda basu wuce goma sha tara (19) ba, idan aka tambayeta menene aure? Za ta ce wata tarraya ce ta mutane guda biyu, bautar Allah shi ne kasudin wannan tarayya, zama ne da an an lokacin da a fara shi, amma sanin ranar da zai kare babu wanda ya sani, ta sani da cewa zaman aure ya gaji kalubale iri-iri. Za ta iya cewa gidan aure tamkar jami'a ce, kowa a fannin da yake karanta, dan haja jarrabawar ko wani fanninta banbanta da ta wani fannin. Ta kuma tabbatar da cewar duk yadda wasu suka kai ga fuskantar kalubale a rayuwar aurensu, wasu suna cikin farin ciki a nasu auren. Sannan akwai wani abu da ta yi imani da shi kan aure, cewar Aure kan sauya mutum!A ɗan ƙaramin hankalin da take da shi, wannan ce ma'anar da ta bawa aure, shin da gaske haka auren yake? Ko ko kallon biri takewa rogo? Shin ita ma nata auren zai kasance cikin masu sa'a? Koko akasin haka ce za ta faru da ita? Duk da waɗannan tarin tambayoyin da suka cika kanta, irin wanda 'yan mata da yawa kan yi gabbanin aurensu, hankali kwance, sannan cike da zumuɗi Rahama take shirin aurenta.RAHAMA POV."Assalamu alaikum!" ta yu sallama tana saka kai cikin dakin mahaifiyarta, Hajiya A'i da suka kiranta da Anti ta ɗaga kai ta kalleta, sannan idonta ya zarce kan ledojin da ta shigo da su."Har kun dawo?"Anti ta tambaya yayin da take rufe kofar lokarta da take tsaye a jikinta, fuskar Rahama cike da annuri irin na sabuwar amarya da ɗaukin aurenta ba ya ɓoyuwa a fuskarta ta amsa da "Eh Anti, Mun dawo!" ta amsa tana ƙarasa shiga cikin ɗakin, ta zauna a bakin gado tana aje ledojin hannunta. A tsanake Anti ta ci gaba da ƙare mata kallo, irin kallon da take binta da shi a kwanakin nan, Rahama yarinya ce da ba ta iya ɓoye farin cikinta, ko damuwarta, nan da nan fuskarta ke fallasa halin da take ciki. Kuma ba Anti kaɗai ba, duk wani wanda yake tare da ita ya san da hakan. Kasancewar Rahama 'yarta ta fari bai sabta mata goyon 'yan fari ba, domin a ganinta yanzu an wuce wannan zamanin, ta ja 'yarta a jiki sosai, ta yanda duk wata damuwatata ba ta iya ɓoye mata, hasali ma duk duniya ita take fara faɗawa.Kuma idan ka gansu sai ka ce Rahaman ƙanwar Antin ce, domin ita ma Antin ba wani tsufa ta yi ba, kuma dama ba shekarun, sannan tana kula da kanta kuma ba ta shan wahala a gidan aurenta, babban abin da yasa jikinta ba ga nuna shekarunta ke nan. Yaranta huɗu ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters4
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play