FreeArewaPen original
BAKİN ALKALAMI…….
- 1views
- 43chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
"Life is short, break the rules, forgive quickly, kiss slowly, love truly, laugh uncontrollably, and never regret anything that made you smile."
Sample · Chapter 1
BAƘIN ALƘALAMI..... {Mai Rubuta Ƙaddara} Chapter 1 Warning ⚠️ (Ban yarda wani ko wata su juya mini labari ko sakawa a wani kafar sadaukar ba! Idan haka ya faru akwai mummunar mataki da za a ɗauka.) ©️ Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu 2024/2025 TikTok:Marubuciya Mai_Dambu ***:Rammy ***:Mai_Dambu Facebook:Ramlat Abdülrahman Manga Handle din na social media kenan😻 *Bismillahi rahamanin Rahim 2018 *Shimfida* Numfashinta ne ya kusan ɗauke wa sakamakon jin sautin muryar Ummu-Sulaim da take sak da sak da muryan Ya Adam. Wani irin abu ta ji a jikinta wanda ya tilasta mata fara rawa zuciyarta tana wani irin bugawa da ƙarfi take ta ji duk wani tsoro ya kamata. Sulalewa ta yi daga cikin jama'an da suka cika gidan domin taya su murnar sauƙar Alqur'ani mai girma da yarinyar su take yi. Dusu-dusu take gani a gabanta, da ƙyar ta yi nasarar samun shiga cikin gidan ta ƙofar baya wanda ba mutane sosai, ta wuce can ɓangaren mai gidan ta samu wani wuri ta zauna a hankali. Zare medical glass ɗin idanunta ta yi tana me share ƙwallar da take zuba mata. Shekaru goma sha takwas masu muhimmanci! Shekaru goma sha takwas masu daraja! Shekaru goma sha takwas na kuka! A hankali ta ji wani irin kuka yana zuwa mata, a yau madadin miyagun mafarkai da ta saba yi, yau ta wayi gari da farin ciki. Madadin tsoron da ke bijiro mata ta tashi da wani irin yanayi da ta tsinci kanta da shi. A shekarar da ba zata taɓa manta wa da shi ba a rayuwarta. *Shiru wani yare ne mai girma* *Shiru tarbiyyar Africa ce* *Shiru wata duniya ce da ba a son furta kalma* *Shiru na ɗauke da wa'azi mai zaman kansa* *Shiru wani al'amari ne da ke nuna cika ta mizanin hankali.* *Ki gani, ki ƙi gani.* *Ki ji, ki ƙi ji* *Idan yana abu ba ruwanki.* *Kada ki zama mai tuno sirrin miji.* _Ki zauna a ɗakin Mijinki shi ne rufin asirinki_ _Rayuwar mace a cikin nahiyar Afrika. An riga da anyi Manipulation ɗin Mata da cewa Namiji yana da right na yin abin da ya so, an riga da an nuna mana shi namiji duk abinda ya yi ba kome bane face Ado a gare shi. Namiji zai yi komai amma ba za a gani ba, asali ma cewa za'a yi ai idan aka aurar da shi mace zata sauya shi! Ta ya za ayi mutumin da ya zama wani addiction akan wani abu ace suddenly mace za ta iya sauya halinsa? Taya za ayi a ce wanda bai ji maganar iyayensa ba, kawai sai ace akwai wata 'yar yarinya za ta sauya shi? Kun san sharrin zamanin da muke ciki kuwa? Abubuwan da yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa, amma ku biyo Baƙin Alkalamin, mai rubuta ƙaddara mu ga ƙaddaran su waye ya rubuta mana, idan zuciyarki tana da rauni kada ki ƙaranta labarin nan, ina kira ga masu fama da cutar hawan jini, Anxiety discords da masu depression, m...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.