FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuciya ce mai son rubuta labaran soyayya da darussa. Ina ba da labarin zuciya, hawaye, da farin ciki. Maraba da ku duniyata
Sample · Alhamdulillah
By Maryam Usman. Bismillahir Rahmanir Rahim. Page______1️⃣ 12b Banana island drive, Victoria Island Lagos states Villa serenita.9:00amA hankali take saukowa daga stairs, yayin da hannayenta masu sanye da wasu kalan high fashion rings masu ɗaukan ido, da kuma tsada,suke kan hannayen stairs ɗin, sanye take da doguwar rigar fara tass ta Companyn _Celine_ A shape, da ta ji adon stones sai ƙyalli suke yi, kanta ɗaure da silk scarf na Companyn _Moschino_ hannunta riƙe da ƴar ƙaramar handbag silver color na _Chanel_ ƙafanta sanye da silver color heels shi ma na _Chanel_sanye da agogon _Givenchy_ sai simple jewelries da ta saka, sai ƙamshin _Vuitton oud_ take yi na LV da kuma _crystal Noir_ na _Versace_ doguwace fara tass don kai tsaye zaka iya kiranta da baturiya, saboda yanayin Idonta da suke green, da kuma gashin kanta mai tsawo da ya fito cikin scarf ɗin ta, wani kyau ne da ita sosai ba ma kaɗan, face ɗin ta shi ake kira da model face, saboda yanda take a haɗe tsap.Kuma ba wai, cikin ɓacin rai take ba no haka face ɗin yake, irin face ɗin ake kira da resting bitch face, ahankali take saukowa yayinda idan ta taka stair ɗaya sai ya kawo haske, a haka har ta sauka cikin seating room, wanda ya haɗu da wasu irin luxuries, da kuma styling, don irin zubin turawa ne da shi, yanda aka ƙawata palorn da wasu kalan crystals, ga wasu rich expensive furnitures.TV dake palorn kaɗai abun kallo ne, komai ya haɗu tsap, sak zubin turawa, ga wani ƙamshi dake tashi a palorn, mai saka natsuwa, sai ƙaran ac kawai kake ji Tv a kunne yake don akwai mutane a palorn hakan ya saka ta ɗage ƙafafunta yanda heels ɗin ta baza su yi ƙara ba sum sum zata fita,ta ji an ce “Mami, la zia Anaya sta uscendo senza fare colazione (Mami ga Anty anaya nan zata fita bata karya ba).”Wani yaro da yake zaune nan palor ya na kallon cartoon ya faɗa da ƙarfi cikin yaren Italiya, wata mata ce ta fito daga kitchen riƙe da towel ta na share hannunta tare da ba ma yarinyar side eye "Non abbiamo già parlato del fatto che esci affamata? Non ascolti quando ti si parla, Bella? (Ba mun yi magana akan fita da yunwa da kike yi ba Bella? Baki jin magana koh?)" Matar ta ce cikin yaren Italiya ita ma.Ɗan fari da ido budurwar ta yi ita ma cikin yaren italiya ta ce “Scusa, Mami Non lo farò più, (ki yi haƙuri Mami ba zan sake ba).” girgiza kai Mami ta yi "Lo so che non cambierai (Na san ba za ki canza ba Bella)." Numfashi yarinyar ta sauke "Na sha coffee da safe." Sai kuma ta kalli agogon hannunta zaro ido ta yi.Da sauri ta ƙarasa in da Mami take tsaye ta yi mata kiss a kumatu sannan ta ƙarasa in da ƙaninta yake zaune shi ma ta yi masa kiss a kumatu tare da jan kumatun wanda sai da ya yi ƙara "Gobe ka sake kai ma Mami gulmana." Ta ce da turanci sannan ta yi ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.