FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 2
Suna zuwa asibitin suka nufi emergency, sun tarar da su DSP a tsaye, daga gabansu kuma likitoci ne suka yi cirindo a kan Hussaina, sun mata ƙawanya. "Ya a ki ciki ne?" ASP ya yi tambayar, idanunsa a kan DSP. "Tun da muka zo dai suna a kanta har yanzu ba su ce komai ba." "Ina ita uwar?" DSP ya buɗe baki zai yi magana, karajin Aisha ya karaɗi emergency ɗin, wanda hakan yasa bai iya furta ko da kalma ɗaya ba. Suka nufi wajanta da sauri. Hankali tashi, Abdul ya riƙo hannunta. "Ina 'yata? Don Allah ku ce mini babu abin da ya sameta. Mafarki ne nake, ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin!!" Rungumeta ya yi, jikinsa ya kasa cewa ko da uffan saboda ji yake bakinsa ya bushe, yawon bakinsa sun ƙafe tamkar an sa gum an datsi laɓɓansa. Ƙwaci jikinta ta yi daga riƙon da ya yi mata, ta sauko daga kan gadon da sauri tana faɗin, "Ina 'yata!!!" Nus suka tasu suna ƙoƙarin riƙita ta, yi saurin ja baya ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.