FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Waleedarh Abubakar ✍🏽 Marubuciya mai sha’awar soyayyah, sirrika, royal drama da labaran da ke taba zuciya. Ina rubuta labarai masu cike da emotions, suspense da unexpected twists—labaran da ba za su bar ki ki ajiye su da wuri ba. 🖤📖 Welcome to my world of stories. ✨
Sample · CHAPTER ONE
TSAUNIN RANACHAPTER ONE Bismillāhir-Raḥmānir-Raḥīm.Mulki amanah ne. Sarauta hidima ce.Amma duk inda aka kafa kujerar mulki, akwai jinin da aka zubar domin a kare ta… da kuma jinin da aka binne domin kada ya dawo ya nemi hakkinsa.Fadar Tsaunin Rana5:47 na yammaRana ta fara sunkuyawa a bayan tsaunukan da suka kewaye masarautar. Haskenta na ratsa manyan bishiyoyin lambun fada, yana barin dogayen inuwa a kan farfajiyar da aka shimfiɗa da duwatsu masu sheƙi. Daga nesa ana ganin tutocin masarauta suna rawa a saman sandunansu, yayin da jami’an tsaro ke sintiri a ƙofar fada, radio a hannunsu, idanunsu a buɗe. Babu wani motsi da ke wucewa ba tare da sun gani ba. Fadar ta fi girman da ido zai iya ɗauka a kallo ɗaya. Manyan tagogin gilashi suna fuskantar lambunan cikin gida. Motocin sarauta na shigowa suna fita. Daga kitchen ana jin ƙarar faranti da muryoyin masu aiki, duk sun cakuɗe da hayani...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.