Miskili da Sha'awa 🔥📖Free

ArewaPen original

RomanceFreeOngoing

Miskili da Sha'awa 🔥📖

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

❤️‍🔥LOVE LEET HEATE ❤️‍🔥 Sun hadu ne da ƙiyayya… amma ƙaddara ta zaɓi soyayya. Dana ba ta taɓa tunanin za ta iya ƙaunar mutumin da zuciyarta ta rantse za ta ƙi ba. Shi kuwa mahabub, mutum ne mai tsauri, girman kai da sirrin da bai taɓa bari kowa ya shiga cikinsa ba. Haduwars...

More from @angelbossauthor

Sample · Chapter 1&2

chapter 1& 2 ABUJA NIGERIA MAI TAMA Hafsa ba ta taɓa yarda cewa mace za ta iya rayuwa cikin farin ciki ba tare da ta kula da kanta ba. Tun tana ƙarama take da son kwalliya, turare da gyaran jiki. Ba wai don tana son nuna wa mutane kanta ba ne, amma tana jin daɗin yadda take ji idan ta kalli kanta a madubi ta ga yarinyar da ta so ta zama.Da sassafe ta tsaya gaban doguwar madubi a ɗakinta tana gyara dogon gashinta. A kan teburinta akwai turare iri daban-daban, man shafawa da kayan kwalliya da ta tara a hankali. Ta ɗauki ɗaya daga cikin turaren ta fesa a jikinta, sannan ta yi murmushi.“Yau kam zan yi kyau sosai.”Ta koma ta zauna a gefen gadonta tana kallon wayarta. Saƙonni ne suka cika screen ɗin, amma babu wanda ya fi ɗaukar hankalinta kamar saƙon da mahaifiyarta ta turo mata tun da safe.Ki shirya. Za mu tafi yau.Hafsa ta dafe goshinta.“Tafiya kuma?”Ta san wannan tafiyar ba irin sauran tafiye-tafiyen da ta saba yi ba ce. Mahaifiyarta ta daɗe tana magana game da wani gida da za ta je ta zauna na ɗan lokaci, amma Hafsa ba ta taɓa ɗaukar maganar da muhimmanci ba.Sai dai a yau komai ya bambanta.Ta mike ta buɗe akwatinta, tana zaɓar kayan da za ta ɗauka. Ta ɗauki riga, ta ajiye. Ta sake ɗaukar wata, ta girgiza kai.“Wannan ma bai yi ba.”Ta ci gaba da zaɓe har sai da ta cika kusan rabin akwatin da kaya.kanwar ta mariya ce tashigo tana kare mata kallo Aunty har yanzu ba ki shiya ba?Hafsa ta kalleta. “Ina zan je da kayan da ba su yi min kyau ba?”“Ke dai kin fi son kaya da yawa fiye da komai.Hafsa ta yi dariya. “Kayan kyau ne fa. Ai mace ta kula da kanta.”ita fa a jikin ta takeji wannan tafiyar ba alkari bace,Ba ta san irin rayuwar da ke jiranta ba.Ba ta san dalilin da ya sa aka tura ta wannan gidan ba.Bayan tagama shirya wa ta dauki kimono ɗinta pick colour ta daura akan pencil jeans dinda ke jikin ta sai 'yar top karamin veil ta sanya ta yane gashin kanta dashi wanda ya fito da ainihi kyawun ta,hafsa bata cika son full makeup ba shiya iya lips dinta take gogawa man baki saitayi brush eyelashes da jigara wayar ta tadauka da handbag ɗin ta wacce tayi match da kayan taa hankali take jan trolley tana tafiya ta latsa wayarta a parlourn ta zauna tana dannawa mommy kira.good morning dear tafada tana karyar da wuya okay ina parlourn tayi reaject call cike da nutsuwa farar matar da akalla zatayi shekaru 53 take taka step ɗin kyakkyawa ce ajin farko kasance war hafsa Asali kyawun mahaifiyar ta ta ɗauka amma ita ba fara bace kasance War mahaifin ta ma ba fari bane launin fatar sa da ɗauka amma kyau babu abinda ta bari a mahaifiyar tatashi tayi tana huge din mommy yar albarka kinshir yane yeah dear na shirya kinsan banaso nayi dare a hanya okay kije driver na jiran ki papi yace zai same ki acan okay mommy thanks bey tasake huge ɗinta tana...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play