MakomataFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

Makomata

  • 1views
  • 15chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

*MAKOMATA* SADIYA ABDULRAZAK        & ABDUL'AZIZ ABDULLAHI MarubucinƘudan zuma MARUBUCIYAR HawayenmuRigar ƙaya Ku yi mana adalci Dukan Taiki Miji goma Sandar dukan uwargida Aure A Yau Iya ruwa Wani auren. Da sauransuPage 1 A hankali take motsa idanunta a ƙoƙarinta na ganin sun buɗe, domin ta ga makomarta wuta ce ko aljana? Domin Ita dai a iya hasashenta ta mutu ta bar duniya, duniyar da take so ta ci wa burika masu yawa wanda ta so ta cim musu kafin mutuwarta, ashe burinta ba zai cika ba, kodayake dama an ce ɗan'adam da buri yake mutuwa, ita kam ta ga zahiri, sabon tunani ya shigo cikin tunaninta ya yi mata tambayar 'Dama idan an mutu ma ana tunani?' Ba ta gama baje tunanin ba ballantana ta yi sharhinsa, wani sauti ya ba ta tabbacin ba ta mutu ba, muryar wanda ba za ta taɓa manta zaluncinsa a gare ta ba, da sanyin muryarsa ta yaudara ya furta "Noor"Tabbacin da ta samu na ganin tana raye ya sa ta tilastawa kanta buɗe idonta, sun buɗe amma sun yi mata nauyi sosai inda mutum yana iya kallon idanunsa ba tare da mudubi ba da idan ta kalli nata idanun su kaɗai za su saka ta karanci girman bala'in da take ciki, jin ƙarar buɗe ƙofar ya sa ta fara ƙoƙarin tashi zaune, sai dai sam jikinta ba shi da ƙarfin da za ta samu wannan damar, don haka ta fara hawaye, da dashasshiyar muryarta ta ce "Na karaya, na sare, na haƙura na zubar da makamaina, don Allah Nasir ka rabu da ni, ka mayar da ni gidanmu".Wanda ta kira da Nasir ɗin ya ƙaraso inda take ya ɗaga ta ya tashe ta zaune ya jingina ta da bango, yana murmushi ya ce "Idanunki sun yi jawur tamkar gauta, kin sha wahala sosai, na ji tausayinki, shin za ki yarda ki yankewa kanki wahala?""Duk wahalar da na sha ba za ta dame ni ba matuƙar ba ka keta min haddi ba, alƙawari na yi wa Allah na kan ba zan taɓa saɓon shi ba, ba zan taɓa kauce hanya ba a hanyata ta neman shahara, kuma Alhamdulillah ban yi ba har na kawo matakin da nake kai yanzu, in sha Allah saɓonsa ta hanyar aikata zina ba zai zama nuna godiyata a gare shi ba, don Allah ka mayar da ni inda ka ɗakko ni, kar ka kashe ni, ina da sauran burikana".Yana murmushi ya ce "Noor kenan, kamar yadda kike girmama burinki ni ma haka nake martaba nawa burin, a yanzu ke ɗaya ce mahaɗar cikar burina, ke ce kaɗai igiyar da zan kama na kai matakin da nake son cim mawa, don Allah ki amince min ni ma na cika nawa burin mana, na yi miki alƙawarin miliyoyin kuɗi"."Inda kuɗi nake nema da tuni na samu, kuma da ban shahara ba..."Ya katse ta da faɗin "Shahara ai kin gama samunta Noor, babu abin da ba ki samu ba my super star, ni kawai za ki taimaka yanzu ki amince min na samu hawa kan kujerata"."Ba zan taɓa aikata zina ba matukar ina cikin hayyacina""Ni ma ba zan taɓa bari ki bar wajen nan ba matuƙ...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “Makomata” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play