KOMAI Na RAYUWAFree

ArewaPen original

RandomFreeCompleted

KOMAI Na RAYUWA

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · Chapter one

*KOMAI NA RAYUWA**By ABDULHAKIM UMAR ƊAN BUGAJE*Gajeren labari mai taɓa zuciya Sadaukar wa ga Hadiza Bara'u Gidan IkoKhadijah Abubakar Alƙali ( Khadijah candy)Salis Adam s RezaHusain YusufRiƙayya Yusuf IbrahimSayyid lagendBilin AbdulMuntasir ShehuMubarak idiris jikamshiRufa i Abubakar Adam---Babi Na Daya: Mafarki Da GishiriA garin *Bugaje* da ke kusa da jibiya akwai wani saurayi mai suna *Sulaiman*. Sulaiman ba wai bashi da kudi bane, yana da arziki - shaguna uku gare shi a Katsina babura biyu, da gida mai kyau. Amma duk da haka, kullum zuciyarsa na cikin damuwa. Yana ganin rayuwa tamkar takarda ce babu komai a ciki.Mahaifinsa, *Alhaji Umar*, mutum ne mai hikima. Wata rana yace dashi:"Sulaiman, ina ganin kana neman komai na rayuwa a ɓangaren kudi da ababe jin daɗi . Ina so Zamuje muje gona."Suka tafi gonar citta. Alhaji ya dauko gishiri, ya zuba a kasa. Yace "Ka dandana."Sulaiman ya dandana, yayi kyam.Alhaji ya dauko gishiri kadan ya zuba a ruwan kofi, ya bashi. Ya sha, Da sauri sulaiman ya furzar da ruwan bakin nasa yana ta tofin yahu tub ! tun !! .Sakamakon kama bakin nasa da gishiri ya yi zaiAlhaji yace: "Ka gani? Rayuwa kamar gishiri ce. Idan ka tara ta a wuri daya - kudi, kudi, kudi - zata zama mai daci ta kashe ka. Amma idan ka watsa ta - ka bawa makwabci, ka taimaki maraya, ka yi dariya da mutane - komai zai yi dadi."Babi Na Biyu: JarabawaSulaiman bai dauki maganar da muhimmanci ba. Har sai wata rana abokin kasuwancinsa ya yaudare shi. Ya kwashe masa kusan miliyan biyar. Shagunansa suka rufe. Abokansa duk suka guje shi. Wanda yake ba su bashin kudi a da, yanzu idan ya kira su basu daukan wayarsa.A cikin dare daya, Sulaiman ya koma talaka.Ya koma Bugaje yana zaune a gida babu abin yi. Sai ga *Malam Audu*, makwabcin su wanda yake sana'ar gyaran takalma. Malam Audu bai da komai, amma kowace yamma gidansa cike yake da mutane suna dariya, suna shan shayi.Sulaiman ya je wajensa yace: "Malam Audu, kai baka da kudi amma me yasa kake farin ciki haka? Ni na rasa kudi kadan amma ina cikin duhu da damuwa gami da bakin ciki."Malam Audu ya yi murmushi yace:"Sulaiman, saboda ni na san *Komai na Rayuwa ba kudi bane*. Komai na rayuwa sune abubuwa hudu:*1. Lafiya:* Ka tashi da safe kana iya numfashi ba tare da bututun asibiti ba - wannan arziki ne da miliyoyi ba sa iya siya.*2. Iyalai da abokai na gaskiya:* Mahaifiyarka da take kawo maka koko da safe duk da baka da kobo - wannan ita ce rayuwa.*3. Nutsuwa da yarda da kaddara:* Wanda Allah ya bashi nutsuwa, ya bashi komai.*4. Taimakon juna:* A al'ummarmu ta garin jibiya da Bugaje suna da kirki da taimakon juna , idan gonar daya daga cikin mu ta kone, duka kauye sukan zo su taimaka ta sake tsiro. Wannan zumunci ya fi zinare kuma wannan ita ce rayuwa ta zahiri ."Babi Na Uku: Komawa GonaWannan ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play