CANJIN BA ZATAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

CANJIN BA ZATA

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Marubuci ba makaryaci ba ne

More from @maryamlitee

Sample · Babi na farko

🌟🌟CHANJIN  BA ZATA🌟🌟ByMARYAM IBRAHIM LITEE MALUMFASHI Babi na ɗaya Da sunan Allah me rahma me jin kai Kwashe tuwo nake a cikin kicin idona duk ya yi ja  saboda hayaƙi dan gidan yawa ne,  kowa ya hura murhun sa, amma duk da haka hankalina na can wurin sauraron hirar da Baba Ladi da Baba Gambo suke yi, waɗanda ke ƙarƙashin baranda daga yamma. Yayin da Mahaifiyata Fatima wacce muke kira Innarmu mu ƴaƴanta, take daga na ta kofar ɗakin, itama a ƙarƙashin baranda amma ita  a ɓangaren gabas take, kenan suna kallon juna, wanda na tabbatar itama tana sauraren su suna tattaunawa ne kan bikin wata yarinya a makwabtanmu na irin mahaukatan saitin da aka dan ƙara mata da kayan kicin ɗin da aka yi mata sai da aka maido ma uwar da saura. Gara kuwa da aka soma loda ta sai da aka cika store har ma ya yi kaɗan. Baba Ladi kenan take faɗawa Baba Gambo, Baba Gambo tayi tsaki cikin nuna damuwa. "Ai wallahi kallo ya bar ni, duk wannan mayataccen tarin ne da ya sani gaba shi ya hanani zuwa dankin nan, amma in Allah ya yarda da ni za'a ranar bikin in je  in kashe kwarkwatar ido". Tsam Innar mu tayi ta shige ɗaki, nima na kammala kwashe tuwon cikin wata babbar cooler na kai ɗaki  na komo na ɗauke tukunyar miyar na aje a kofar ɗakin mu. A ɗaki na samu Innar mu tana zaune kan ƙaramin gadonta na katako ta dora kanta jikin gadonta, ganin har na zauna bata ɗago ba ballantana tayi min sannu da sanya albarkar da ta saba a duk sanda aka yi mata abinda ya faranta mata, na san abinda ke damunta dan haka  sai na  ƙara matsawa kusa da ita Innar mu " na kira sunanta firgigit ta yi alamar tayi nisa cikin tunani. "Me ya same ki? " Na tambaye ta shiru tayi na cigaba. Innar mu kwanan nan, kin tsangwami kan ki, tun randa su Baba Ramu suke hirar auren Jamilar Alh Babajo har suke cewa wasu sai dai aukin tara yaya mata amma ba a da   zuciyar da za a huce takaicin kai masu kayan ɗaki, tun daga nan kika rasa walwalarki. Na sani auren Anty Ummu kike tunani, wanda ko shi mijin naga ai yasan halin da muke ciki, har kuma ɗakin nan ya zo ya ce kar ki damu kanki, abinda Allah ya hore shi za'a kai mata, kuma arzikin bawa ai  yana goshin sa Malamin mu ma ce mana yayi duk  wanda ya dogara ga Allah ya isar masa sai ki ga abinda ba'a zata ba, kofofin Allah ai yawa gare su". Zuba min ido tayi ganin yarinya ƴar shekara sha biyar ce da wannan zurfin tunanin, duba na tayi sosai sannan ta ce duk na sani Shuhaina abinda ke damuna duka yau saura kwana ashirin da hudu bikin nan ga gonar mahaifinku wacce kuka ci gado na ce a sata a kasuwa amma dillalan sun ƙi mata sayen daraja, kuɗin su ɗan yi auki, dan nufina a raba kuɗin biyu ayi mata hidima da rabi rabin sai a adana maki a banki  tunda ke ma idan muna da rai kwana nawa ne? " Jin ban amsa ba yasa t...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play