FreeArewaPen original
Rayuwar maryama
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I write what hearts feel but words fail to say. 🖋️ Stories woven with love, pain, dreams & reality. — Arewa Pen ✨
Sample · CHAPTER 1 I
CREATED BY AISHA HAMZA* _MUAYSHGRAPHICS_ 22/9/2023 Bismillah da sunan Allah mai rahama mai jin kai wannan 📖✍️ littafi rayuwar Maryama na kirkireshi ne domin abubuwa da yawa duk da cewa zai iya kamanceceniya da rayuwar wani ko wata amma ni ba rayuwar kowa na kwaikwaya ba nayi ne domin fadakarwa da kuma nishadantarwa domin rayuwar Maryama rayuwa ce wadda yawancin abinda yake faruwa kenan a zahiri a rayuwar mu ta yau da kullum a wasu gidajen _Na sadaukar da littafi na ga ƴan uwana mata Anty surayya Anty shamsiyya Anty zainab yaya Ummi yaya Maryam yaya Safiyya sai ƙannena Jamila da ƴargwal rukayya da husna Khadijah da Halimatu_~Book 📚 1~•Bismillah• _RAYUWAR MARYAMA_ *ByY A'ISHA HAMZA**Dukda cewa hadari ya haɗu gari yayi tsit kowa yana cikin gida ba abinda kakeji sai kukan* *tsuntsaye kasancewar angama sallah maghrib cida kawai akeyi amma Maryama tana qasan bishiyar qofar gidan malam sani ta kwanta kanta a cikin cinyoyinta tasa hannu ta toshe kunnenta kana ganinta kasan a matuqar tsorace take da fargaba**Maryama yarinyace da bazata wuce ƴar shekara biyar ba zuwa shida sunan babanta malam habu mahaifiyarta kuma bata kai shekara biyu ba Allah ya amshi abinsa Maryama tanada yayye biyu amma duk maza ne sadiqu da Najib bayan rasuwar mahaifiyarta ne malam habu yaqara Aure ya auri balaraba yar wajen amininsa hadi ita take kula masa da yaransa'''''' tunda balaraba Allah ya azurtata da samun haihuwa a gidan malam habu fitinar yau daban ta gobe daban* *Kullum Maryama saedae ta yini a waje har sai babanta yadawo daga wajen aiki da yake yana gadin wata ma,aikata su kuma yayyennata su ma basa zama a gida Sadiqu shine babba zai kai shekaru goma sha biyu sai najibu da bai wuce shekara tara ba amma ahaka Balaraba tace Dukansu sun isa neman kuɗi saboda haka bamai zaman mata gida saedae ta girka tabasu suci dukda cewa Mahaifinsu ke nemowa ai sangartasu za,ayi badan malam yaso ba da yace tabar Najib sai yaqara girma amma da yake shima malam habu sai yanda tayi dashi haka ya haqura yasa mata ido domin tace sam ita bata yarda da wannan zancen ba*Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman neDa sauri sauri malam habu ya nufi kofar gidan malam sani a inda ya hango yarinya dukda yasan cewa a ranshi ba wadda zata kasance a wajen sai ƴarsa* _Maryama koda ya,iso inda take ya taɓata da sauri ta matsa tana qoqarin yin kuka koda tabude idonta dukda kasancewar duh...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.