AMINCIN RUHIFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

AMINCIN RUHI

  • 1views
  • 30chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

DREAM • BELIEVE • ACHIVED

More from @maikwai

Sample · AMINCIN RUHI CHAPTER 1

*** RUHI💥💖    ~By~KHADIJAH SALEES    (MAI KWAI) YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)  DEDICATED TO MY BELOVED FAMILY🥰 Follow MAI ƘWAI...✍️❣️OFFICIAL CHANNEL on *** *** Ruhi ƙirƙirren labari ne idan yayi kamanceceniya da labarin wani ko wata ina fatan za'amun afuwa banyi da niyya ba🙏)     _MAI ƘWAI...✍️❣️_Bismillahirrahmanurrahim PAGE 1️⃣ ROYAL CRESCENT SPECIALIST HOSPITAL Babban private hospital ne dake da hawa biyu, su na da tarin ma'aikata, masu aiki cikin ƙwarewa, ƙwazo da hazaƙa. Zaune yake cikin office ɗin da yasha gyara tsaff tsaff, ga ƙamshin air freshener, da sanyin AC ɗin da ya haɗu, ya bada wani yanayi mai daɗin shaƙa.Paper ce a hannunsa ya ƙurawa rubutun da yake jiki ido, fuskarsa ta nuna tsantsar tashin hankalin da yake ciki, ga zufar da yake haɗawa duk kuwa da ac ɗin da take a kunne. Zai iya cewa tunda aka haifesa, bai taɓa jin makamancin tashin hankali irin wannan ba. Ya karanta takaddar yafi sau shirun masaki amma amsar dai ɗaya ce, abu daya yake ƙara gani, ba wani banbanci da abinda ya gani da farko, amsar dake ruguza zuciyarsa, rintse takaddar yayi a hannunsa, ji yake gaba daya duniyar tana juya masa.  "innallilahi wa'inna ilaihir'raji'un"Ya furta cikin wani irin tashin hankali, yana dafe kansa, dake sara masa kamar zai rabe gida biyu, wata iriyar zazzafar iska ya furzar daga cikin bakinsa, tashi yayi ya fara zagaye office ɗin, har lokacin hannunsa riƙe da takardar, yana yi yana karantawa, ba tare da gajiya wa ba, gaba ɗaya ya kasa yarda, zuciyarsa ta kasa gazkagata masa abin da yake gani a jiki.Buɗe ƙofar akayi, wani matashi ne ya shigo... "bro ka duba message ɗin dana tura maka kuwa"... shiru yayi ganin yanayin da yake ciki.    Da ɗan sassarfa ya ƙarasa inda yake..."lafiya kuwa na ganka a haka, ko wani abun ne ya faru?" Ya tanbayeshi, yana matsowa kusa dashi, kafaɗarshi ya dafa, yana leƙa fuskarshi, daga tsayen da yake..."wai Hakeem, bazaka fadamun abinda ya faru ba".shiru yayi masa bai iya cewa komai ba sai ajiyar zuciya da yaketa saukewa, bakinsa ya masa nauyi, ƙirjinsa ji yake kamar an ɗakko dutse an ɗora masa. ganin hakan yasa, ya riƙo hannunsa, ya miƙar dashi tsaye...tashi shima yayi baiyi musu ba. Jan hannunsa yayi, shima kamar karamin yaro haka yake binshi.Wajen sofa's ɗin dake cikin office ɗin daga ɗan gefe ya kaishi, wanda aka sakasu saboda hutawa, zaunar dashi yayi, a ɗaya daga cikin kujerun, sannan ya koma gurin fridge ya buɗe ya ɗakko ruwa, ko cup ɗin ma bai tsaya ɗauka ba. Yana zuwa ya buɗe murfin robar ya bashi, ya zauna a kus...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “AMINCIN RUHI” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play