RANTSATTSEN RABOFree

ArewaPen original

General fictionFreeCompleted

RANTSATTSEN RABO

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · RANTSATTSEN RABO CHAPTER 1

✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨🦋   BY RABI'ATU KABIR ACHADU (FULANI)YOUNG TALANTED WRITER'S ASSOCITION YOTA  SADAUKARWA GARE KI HALIMA HASHEEM)MIEMIEN HABIBI)❤️& AHMAD JAMIL AHMAD (HABIBI) ♥️    FULANI❣️ ***✨🦋 RANTSATSTSEN RABO ✨ 🦋 PAGE1️⃣Matashiyar budurwa ce yar kimanin shekara 17, take tafiya cikin natsuwa sanye da kayan makaranta, da alama daga makarantar boko ta taso.Da sallama ta shiga gidan, tun a bakin kofa take jiyo irin muguwar ashariyar da wata yarinya take yi, wanda da alama fada suke yi ita da wani yaron a cikin ƴan uwanta.Da shigarta gidan ba ta yi kasa a guiwa ba, ta kai ma bakin yarinyar duka, duka yarinyar bazata wuce shekara 8 zuwa tara ba, a razane ta dago, ta bude baki da niyyar ƙara yin wani zagin, amma ganin wadda take tsaye a gaban ta yasa ta yi sauri ta kame bakinta da hannu biyu tana zare ido.Kunnenta matashiyar budurwar ta ja ta murɗe da ƙarfi tana fadin,“Zainab, me nace miki akan zagi? shi Mukhtar din da kike zagin sa’an ki ne?"Tuni idanuwan ta har sun cika da hawaye na azaba da tsoro cikin rawar murya tace,“Addah dan Allah ki yi haƙuri, shine ya fara ɗaukan min abu kuma na yi masa magana ya dake ni”Dara daran idanuwanta ta dago ta kalli inda yaron yake, dan kimanin shekara 10, wanda tun shigowarta ya sha jinin jikinsa, kallo ɗaya tayi mishi wanda tun kafin ma ta ce wani abu yayi saurin fadin,“Addah wallahi ba gaskiya ba ne, ita ce na aje abu ta ɗauka kuma ba ma nawa ba ne, na sani abokina ne, shi ne ta lalata, na mata magana ta taka min rashin kunya.”“Shi ne sai ka daketa ko?”“A’a” yace yana zare ido.“To sai ka mata mi?”“Addah ki yi hakuri dan Allah,” ya fadi yana ƙasa da kansa.Kwafa ta yi ta saki kunnen yarinyar tana fadin“Kun yi sallar azahar?”Tana binsu da ido alamar amsa take jira. Cikin sauri suka je suka dauko buta a bakin rijiya.Ta ce, “Allah ya shirye ku ku kam”Idonta ne ya fada kan Baba Zainu da take zaune tana faman aika mata da harara, tana aikin awara ta saidawa da suke yi.Ɗan kauda kanta ta yi kadan tace,“Baba sannu da gida.”Dogon tsaki ta ja tana faɗin,“Muguwa, sai bayan da kika gama cin zalin yara sannan kika ganni kenan? To wallahi ni dai ki fita daga ido na dan akan yarana zan iya yin komai, ke fitsarar da kika yi ma da dukan ki akayi ai da baki kawo yanzu ba.”Ta faɗa tana kara banka mata uwar harara.Ɗauke kanta ta yi kawai ta nufi kofar ɗakin su ba tare da ta ce mata komi ba, saboda ba ta da lokacin fitinar matar nan wadda ita komai za'a mata laifi ne, dan ma dai ba yar jarababbiyar tsohuwa bace ta ganta da faɗan ma sai yafi haka tana jin kila bata gidan ko tana can tana baccin asara.Bata kai ƙarshen tunaninta ba ta jiyo muryar Hajja ta ɗaga labule tana fadin,“Zainu wai hayaniyar menene nake faman ji? Lafiya ba za a bar mutum ya yi bacci ba?”Cike da t...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0
01

RANTSATTSEN RABO CHAPTER 1

Free sample
Updated 5 hours agoAvailable now
02

RANTSATTSEN RABO CHAPTER 2

Free sample
Updated 5 hours agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play