FreeArewaPen original
RAYUWAR SUBAI'AH Part 3
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Littafan marubuciyar 1-RU'DANI 2-BABBAR HUJJA 3-KWATAR KAI 4-RAYUWAR SUBAI'AH 5-MISTER MASHI 6-WATA SAKAYYAR.... 7-KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA? 8-ZUWA LEGOS BA KAJIN TURANCI WATA LUKUTAR MASIFA CR 9-A GASKIYA WASU 'YAN UWAN SUKE BAYAR DA KAI. 10-YO WA YA'KI BANZA ...
Sample · RAYUWAR SUBAI'AH Part 3
RAYUWAR SUBAI'AH*Part 3**Fatima Dahiru Funtuwa Binta* Subaiah ta ce "An dai kama ni, Humf! Kedai bari, yau naga irin mujin novel, in gaya maki ɗan uwanmu ne, amma ya daɗe baya ƙasar, ke dai kawai Allah ya ba ni muji irin shi." Asiya ta ce "To aike faɗuwa tazo dai-dai da zama, kice kawai Allah ya baki shi. " Ta ce "Ameen ya Allah. " Haka sukaita firar su, har misalin ƙarfe goma sannan sukayi sallama Washe gari misalin ƙarfe goma na safe, Subai'ah ta fito, cikin falo ta same Nazeer yana ɗaukar wasu kaya. "Barka da safiya Auncle, an tashi lafiya?" Cikin ɗan hanzari ya ce "Yauwa Subai'ah, ɗan taimakamin da kayan nan, zan wuce dasu ɗaki." Ta ce "To, aiko baka iya ɗaukar su gaba ɗaya, da saidai kayi zuwa biyu. " Ya ce "Hakane." dai-dai lokacin da yake miƙa mata na hannun shi. Yana gaba tana biye dashi, har ɗakin shi. Suna shiga ta ce "Waw!! Gaskiya ɗakin ka yayi kyau sosai, idanunta takai kan Television ɗin da yake kunne, rass! Taji gaban ta ya faɗi, tayi saurin kauda kanta daga Television ɗin, sakamakon wani film da idanunta ba zasu iya jurar kallo ba, da sauri ta fara ƙoƙorin ajiyemai kayan. "Miƙo min kayan nan." Ya fađa yana kallon ta, Ta miƙa mashi tana ƙoƙarin fita, ya riƙe hannun ta "Wai saurin me kikeyi? Naga sai wani gudu-gudu kike." Ta ɗaga idanun ta ta kalle shi, da nufin tayi mai magana, sai dai shima ya tsare ta da nashi idanun, hakan yasa tayi ƙasa da kanta dalilin wani kwarjini da yayi mataMotsa hannunta ta farayi daga cikin nashi tana so ta kwace nata hannun, da sauri yasa ɗayan hannun nashi ya riƙe ta. "Wai gudu na kikeyi ne? Ɗago ido ki kalleni mana." Ta ce "Don Allah Auncle ka sakeni." Ta fađi maganar cikin sigar shagwaɓa. Har cikin zuciyar shi yaji kalaman ta sun shigai. Ya ce "Niba yayan ki ba ne? Don na kama hannun ki wani abu ne? " Ta ce "Naji ba wani abu bane, amma dai sakar ni in fita." A hankali ya fara matsa hannun nata da duka hannayen shi guda biyu, yana ƙoƙarin ya saketa, taushi da santsi da taji hannun nashi dashi yasa itama ta ƙara taɓa nashi hannun. "Lallai wannan shine mujin novel komai ya haɗa, ji laushin fatar shi ko mace Al-barka." Take faɗin haka a zuciyar ta, gaba ɗaya ta sakan-kance sai faman shafa hannun shi take har zuwa tsintsiyar hannun. Ganin yadda ta shiga wani yanayi yasa yayi amfani da wannan damar ya janyo ta jikin shi. &...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.