FreeArewaPen original
RAYUWAR SUBAI'AH Part 4
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Littafan marubuciyar 1-RU'DANI 2-BABBAR HUJJA 3-KWATAR KAI 4-RAYUWAR SUBAI'AH 5-MISTER MASHI 6-WATA SAKAYYAR.... 7-KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA? 8-ZUWA LEGOS BA KAJIN TURANCI WATA LUKUTAR MASIFA CR 9-A GASKIYA WASU 'YAN UWAN SUKE BAYAR DA KAI. 10-YO WA YA'KI BANZA ...
Sample · RAYUWAR SUBAI'AH Part 4
RAYUWAR SUBAIAH *Part 4* *FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA* Ya zauna bakin gado ya ɗauke ta ya ɗora kan ƙafar shi, sannan ya ce "Idan har kin yarda dani akan bazan iya cutar dake ba, ni kuma ki bani dama in jiyar dake daɗi ko da na ƙanƙanin lokaci ne, ba abinda zai faru tsakanina da ke, kawai dai wasa zamuyi." ya buɗe mata ƙirjin shi tare da janyo kanta ya ɗora. Jinta da tayi a inda take mafarkin kasancewa, da kuma irin mujin da take burin ta aura. (kyakykyawan muji-mai faffaɗan ƙirji-ga wani gashi da yayi mai luf-luf a ƙirji, irin mujin novel da take son aura😁) Yasa ta ƙara narkewa a jikin shi, tana shafa ƙirjin nashi.Saida taji ya kai hannu yana ƙoƙarin zuge mata zeef yasa tayi saurin dawowa hankalin ta, ta dakatar da shi. "Gaskiya bana so Auncle kada muyi haka da kai, Haramun ne, ni karka jefani a halaka! " Ya ce "Subaiah haka zamuyi dake, niɗin kike tunanin zan iya halakar dake?" Sai kuma ya ƙara marairaice murya "Haba ƙanwa ta ba wani abu zanyi maki ba, ki ɗan jira, wani abu ne kaɗan, yana ƙoƙarin tura hanhun shi a kirjin ta, ta dira daga ƙafar shi da sauri, ya janyo ta da ƙarfi Ta ce "Gaskiya bazan yarda ba! Haba abin ai yayi yawa, ta fita ɗakin da sauri. Tana shiga ɗakin ta ta fashe da kuka, don bata taɓa tunanin hakan zata faru ba, tana ta istigfari. Haka ta wuni a wannan ranar ko haɗa hanya bata ƙara yarda sunyi ba, ta kuma kasa fahimtar shin kunyar shi take jine koko tsoron shi? Ita gaba ɗaya ta đan fara shakku akan shi, dama haka yake? Kar dai ace kyawun ɗan maciji yayo? Duk da ina jin ina son shi har cikin zuciya ta, amma ni ba irin wannan soyayyar nake yi mashi ba, kamata yayi ace shi ɗin muji na ne, shine kawai zan iyayin mu'amala dashi ba tare da fargaba ba. Hakanan ta fara nadamar abin ya faru tsakanin ta da shi, duk da dai ba wai wani abu ne mai muni sukayi sosai ba, amma tana gudun ƙara faruwar haka tsakanin su.Bayan sallar la'asar Ta'iba ta gayyaci Subai'ah zuwa gidan 'kawarta, taso su tafi da Sa'iha, a lokacin Sa'iha najin zazzaɓi, domin kuwa ɗabi'ar ta ce, indai tayi tafiya zuwa wani gari sai tayi masassara, don haka suka tafi su biyu. Tana kwance a falo Nazeer ya shigo ya ce "Sa'iha Auntyn ki ta fita da waya a hannunta ne? "Ta ce "E ta fita da ita." Ya ce "Don Allah bani number ta zanyima Ta'iba magana, na kira number Ta'iba ɗin bata shiga ba, ke me yasa baki bisu ba?" Ta ce "Banajin daɗi ne." Ya ce "Ayya! Alla...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.