FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 2.
KATANGA!HADIZA D. AUTA.BIYU. Tsam na yi da raina saboda tuno halin Iya da matsalolinta. Jiki babu kuzari na kira ta a waya, aka yi sa'a tana kusa ta ɗauka, saɓanin wasu lokutta da take jefar da wayar ta yi ta sabgoginta, ko an kira ba ta sani. "Hello, Iya."Na faɗa ina ƙoƙarin danne kukan da yake turnuƙe mini zuciya. "Lafiya? Na ji muryarki wata iri." Ta tambaye ni cikin muryar faɗa. "Abban yara ne ya sake ni." Na yi maganar cikin kuka duk da jarumtar da na so yi kada na yi kukan amma sai da na yi shi. Shiru kawai ta yi mini tana sauraron sautin kukana kamar ta rasa abin cewa. Kafin ta ja numfashi cikin fusata ta yi magana. "Ya sake ki fa kika ce? To kansa ya yi wa don ke ba ki saku b..."Cikin sauri na katse ta ina cewa, "Wallahi Allah Ya sake ni Iy...." "Na ce ba ki saku ba!"Tsawar da ta buga mini kenan kafin ta ɗora zancenta da cewa, "Ko ba ki jin yaren da nake magana da shi ne? Wallahi daga ke har shi ba ku isa ba! Ki hanzarin share wuri ki zauna zama daram, babu inda za ki je kuma ko da wasa kada na ji labarin kin bar gidan nan." A take na ji kukana ya ƙaru, babu shiri na yi magana cikin sautin kukan ina cewa, "Ya fa sake ni Iya, kuma kin san babu sauran igiyar aure a tsakaninmu yanzu duka sun ƙar..." "Don na sani sai me to? Ai duk abin da ya faru ke kika jawo. Tun da kin kasa yi masa biyayyar da zai zauna da ke lafiya, duk da kyautatawar da yake yi miki ba kya gani, wadda yake yi mana mu ma ba ki godewa. To, ki sani ko auren ya mutu babu inda za ki je, don ban ga gidan uban da za ki zauna da yara uku ba. Idan ma zaton kike za ki ji daɗi don kun rabu; to babu mai aurenki a wannan lokacin da waɗannan yaran. Saboda haka zama gidan ubansu ya kama ki ko babu aure, don duk inda za ki je bai kai gidansu ba."Kit ta kashe wayar ta bar ni da sharar ƙwalla wata bayan wata, don na kasa sauke wayar daga kunnena ballantana na yi wani abin kirki. Saboda takaicin mari da tsinka jakar da Abban yaran yake yi mini tana ƙara masa ƙaimi. 'Ni kam ya zan yi da rayuwata ne wai?' Na tambayi kaina don na kasa sarrafa tunanina ballantana na gano mafitar rayuwata da ta yarana. Na yi ƙuri da ido ina kallon jakar da nake haɗa mana kaya tsawon mintuna ban iya motsawa ba. 'Duk na kalli ƙirjinki, ji nake yi tamkar na mutu tsabar baƙinciki. Kowace mace tana da *** a ƙirjinta amma ke komai ya shafe kamar allo. Ta ya zan ci gaba da zama da ke a haka ina kallon ki raina yana ƙara ɓaci?' Kalaman Abban yaran kenan da suka faɗo nini a raina, waɗanda ko don su ya dace na yi nesa da shi kada na sake funkantar wani sabon tozarcin da wulaƙanci ya zarce wanda ya saba yi mini. Daidai lokacin 'yata ta fari mai shekara bakwai ta shigo ɗakin tana kawo mini ƙarar Fahat ƙaramin yarona. Tana faɗin, "Mama kin ga Fahat ya ƙi bari a saka masa rig... innalillahi me k...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.