INA KUKE MAKARANTA HAUSA NOBEL , GA SABON LITTAFIN DA ZAI GIRGIZA DUNIYAR ADABINFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

INA KUKE MAKARANTA HAUSA NOBEL , GA SABON LITTAFIN DA ZAI GIRGIZA DUNIYAR ADABIN

  • 1views
  • 2chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

GIDAN IKOBABI NA ƊAYASHAFI NA FARKODa misalin ƙarfe huɗu da rabi na asubahin ranar Alhamis, ƙarar harbe-harbe ta tashi a ƙauyen tsafe da ke cikin jihar Zamfara.Mutanen ƙauyen sun riga sun saba da jin labarin hare-haren ƴan bindiga, amma wannan karon abin ya zo musu da mamaki, domin ba wanda ya yi tsammanin za su sake dawowa cikin ƙanƙanin lokaci.Saboda an zauna da su kuma an yi sulhu.A wani gida da aka gina da tubalin laka, wata budurwa mai suna Haneefah ta tashi daga barci sakamakon ihun da take ji daga waje yana karaɗe ko ina na garin.Ta zauna a gefen gadonta, tana sauraron hayaniyar da ke fitowa daga ƙofar gidan."Umma! Umma!!"Ta kira da ƙarfi.Daga ɗakin da ke kusa da nata, wata mata ta fito da sauri. Tana sanye da doguwar rigar barci, fuskarta cike da firgici."Me ya faru, Haneefah?""Umma, ba ki jin harbe-harben nan ne?"Matar ta yi shiru na wasu daƙiƙu. Ta kalli 'yarta, sannan ta ce:"Ki yi shiru, Haneefah. Ki shiga ciki. Kada ki kuskura ki fita.""Amma Umma, ina Baba?"Kafin ta gama maganar, sai suka ji an buga ƙofar gidan da ƙarfi.Dukansu suka firgita."Haneefah, shiga ɗaki yanzu!""Umma...""Na ce ki shiga!"Haneefah ta koma cikin ɗakin, amma zuciyarta ta ƙi samun nutsuwa. Ta san mahaifinta, Malam Sani, mutum ne mai jajircewa wajen kare mutuncin iyalinsa. Amma a wannan lokaci, ba ta san inda yake ba.A can bayan gidan, wani dattijo ya yi ƙoƙarin taimaka wa maƙwabcinsa da iyalinsa su tsira daga hayaniyar da ta mamaye ƙauyen.Wannan dattijo shi ne Malam Sani.Sai dai akwai wani abu da ya sa wannan hari ya bambanta da sauran hare-haren da suka gabata.Domin a wannan karon, ba kawai neman dukiya aka zo yi ba.Akwai wani mutum da suke nema.Kuma wannan mutumin yana da alaƙa da wani sirri da ya daɗe yana ɓoye a cikin ƙauyen.*****A gefe guda kuwa, a babban birnin ƙasar, wato Abuja wani katafaren gida mai hawa biyu da ke unguwar Asokoro ginin manyan mutane masu faɗa aji a ƙasar ,Gidan yana da faɗin fili, lambuna masu kyau, motoci masu tsada a gareji, da jami'an tsaro a ƙofar shiga gidan , duk inda kyau da tsarin haɗuwar gida ya kai to wannan gida ya kai tsabar kyau da tsaruwarsa yasa ko gittawa kai ta wajan gidan sai hankalinka ya tashi tsabar dukiyar da aka zuba kamar a ƙasar Amurika.Wannan shi ne gidan Alhaji Abubakar Rimi.Gida ne da mutane da yawa suke mafarkin shiga, domin duk wanda ya san iyalin Rimi ya san cewa iko, ilimi da arziki suna cikin wannan gida.A babban falon gidan, Alhaji Abubakar yana zaune a kan kujera mai laushi, yana karanta jaridar safiya.A gefensa akwai ɗan autansa, Alhaji Isma'il, wanda yake kallon wasu takardun kasuwancisa da yake ƙoƙarin gabatarwa a ƙasar Dubai "Abba," Isma'il ya kira.Alhaji Abubakar ya ɗago kai."Na'am, Isma'il.""Ina ganin ya kamata mu sake duba maganar wannan sabon aikin da aka kawo mana.""Wane aiki?""Maganar kwangila...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters2
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play