FreeArewaPen original
BLACK DAGGER❤️🔥 THE SHADOW OF THE BLACK
- 1views
- 3chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
🔥💋 DUNIYAR BARIKI 💋🔥 Daniel Khalid attajiri ne mai shekara 42, wanda ya shahara a Najeriya saboda kuɗinsa, kasuwancinsa da matsayinsa a cikin manyan mutane. Duk da dukiyarsa da ɗaukakarsa, bai taɓa yin aure ba. Wannan al’amari ya daɗe yana damun mahaifiyarsa, Hajiya Mariya, ...
Sample · KUROSHIO FOREST
Page1️⃣ &2️⃣ KUROSHIO FORESTPARISDajin Kuroshio ba kamar sauran dazuzzuka ba ne da mutane suka saba gani. Wuri ne da ake lulluɓe da duhu mai tsanani, inda manyan bishiyoyi masu shekaru ɗari suka haɗe rassansu a sama, suka hana hasken rana ko wata ratsashi yadda ya kamata Ko da kuwa da rana nane, dajin yana kasancewa mai tsanani duhu cike da sanyi da kuma tsittsit da ke tsoratar da duk wanda ya kuskura ya taka ƙafarsa zuwa kusa da iyakarsa.A cikin wannan daji, babu wata hanya ko alamar mutane. Tsarin wurin ya kasance kamar wani rami ne na halitta wanda ya keɓe kansa daga cunkoso da hayaniyar mutane. Bishiyoyinsa masu girman gaske da kuma manyan tushensu da suka zagaye ƙasa sun zama gida da mafaka ga Alexandre da ƙaninsa Kian.Haɗarin da ke cikin Kuroshio ba ya ƙarewa. Dajin cike yake da mummunan haɗari na namun daji masu cutarwa, macizai masu guba, da kuma wani irin yanayi mai sauyawa ba tare da an sani ba. Duk wanda ya shiga dajin ba tare da sanin makamar aikinsa ba, ba zai wuce sa'o'i kaɗan ba kafin ya zama abincin dabbobin da ke yawo a ciki ko kuma ya ɓace har abada cikin duhunsa."Grrrrrhroooooooh...""WOUROOOOOH!""Hh-r-r-r-h...!!!"haka Damisar take wani irin gurnani mai kaɗa hantar matsoraciya!Wani irin girgiza tayi wutsiyar ta na wani irin kaɗawa tana ware jajayen idanuwan ta akan wanda ke gabanta,Tsaye yake tamkar an da sashi. babu riga a jikinsa, Dogon gashinsa yana daure a bayansa yayin da blue eyes suke fitar da wani irin haske mai ban tsoro sautin fitar numfashinsa kadai ke tashi, yayin da murɗanɗan tsokar jikinsa suke glowing ta dalilin zugar da take sauƙa ajikinsa hannun sa riƙe da kwari da baka wacce ya riga ya ɗanata domin shirin ko ta kwana "Damisar ta yi tsalle da ƙarfi, tana nufar inda yake tsaye. Bai yi ƙoƙarin harbinta ba, sai dai ya kauce mata da sauri, ƙafafunsa suka taka ƙasa mai cike da busassun ganyayyaki. Damisar ta sauka a gefe guda, ta juya gare shi cikin fushi, wutsiyarta tana kaɗawa yayin da take fitar da wani irin ƙara mai firgitarwa. ya ɗan karkatar da kansa,"You are quite annoying," ya furta cikin huskey voice, yana kallon Damisar.A hankali take ja da baya har tayi nisa da wajen da yake sannan ta buga wani uban tsalle ta yo kansa cike da kwarewa ya sanya ƙafarsa ɗaya a ƙasa sannan ya sake saita bakarsa seda ta kusa sauƙa akansa ya saki wannan kibiyar a dede maƙogaronta ai kuwa ta saki wani irin gurnani da ya karaɗe dajin gaba ɗaya Tana zubewa a jikin sa kwanciya yayi itama Damisar ta kwanta a faffaɗan kirjinsa yana sauƙe numfashi babu abinda ake iya gani a fuskar sa face 👀 blue eyes ɗinsa masu firgita firgita ce!!!Cikin zafin nama ya yunƙura yana da ita a jikin sa yana yayi wurgi da ita sunkuyawa yayi ya ɗauki Bakarshi sannan ya ɗauki abubuwan da ya ɗauko a cikin wata jaka wacce aka saƙa da wani kalar ita...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.