FreeArewaPen original
🌷SOYAYYAR DA BAN ZABA BA🌷
- 1views
- 6chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
✨ Welcome to my world of stories! ✨ I’m Ummu khulsum, a passionate storyteller who loves creating beautiful stories filled with love, emotions, family drama, unexpected twists and unforgettable characters. Through my stories, I bring imagination to life, exploring love, heartbr...
Sample · SABUWAR RAYUWA
📖 SOYAYYAR DA BAN ZAƁA BA 🥀 Marubuciya: Ummikhulsum CHAPTER 1 – SABUWAR RAYUWA Ƙarar agogon bango ce ta fara tashi a cikin ɗakin Ameerah, amma kamar ba ta jin komai. Ta jujjuya daga wannan gefe zuwa wancan, sannan ta jawo bargonta ta rufe kanta. “Ameerah! Ameerah!!” Muryar Humairah ce daga bakin ƙofa. “Ke! Kin shirya mutuwar yunwa ne a yau?” Ameerah ta buɗe ido ɗaya. “Humairah, don Allah ki bar ni in yi barci. Ban yi komai ba fa!” Humairah ta shigo ɗakin tana dariya. “Ba ki yi komai ba? To, wa zai yi aikin da aka ba ki? Ni?” Ameerah ta tashi zaune tana kallonta. “Allah Ya baki miji mai son magana kamar ki, sai ki ga yadda za ki yi.” “Ni kuwa Allah Ya bani mai kuɗi, mai son shiru, wanda idan na yi magana zai ce amin.” Dukansu suka fashe da dariya. Ameerah ta sauka daga kan gadon ta shiga banɗaki. Bayan ta gama wanka, ta fito cikin doguwar rigar atamfa mai kyau, ta ɗaure ɗan ƙaramin mayafi a kanta. Ta fito falo inda mahaifiyarta, Safiyya, take zaune tana gyara kayan miya. “Ina kwana Mama?” “Lafiya lau, yarinya. Kin tashi kenan?” “Eh Mama.” “To, zo ki ci abinci kafin ya huce.” Ameerah ta zauna ta fara cin tuwon da aka ajiye mata. Humairah kuwa tana ta magana kamar rediyo. “Mama, yau zan fita da Ameerah.” “Ina za ku je?” “Za mu je kasuwa.” Ameerah ta ɗago kai. “Humairah, ni fa ba kasuwa zan je ba. Ina da interview yau.” “To, ai sai mun je bayan kin gama.” Safiyya ta yi murmushi. “Allah Ya ba ki sa’a, Ameerah. Ina fatan wannan aikin zai yi miki amfani.” “Amin Mama.” A wani ɓangaren na birnin kuwa, Zayd yana zaune a cikin ofishinsa. A gabansa akwai takardu da dama, yayin da Rayyan, ƙanensa, yake zaune a kujerar da ke gabansa. “Yayana, gaskiya kana buƙatar hutu.” Zayd bai ɗago kansa ba. “Me ya sa?” “Saboda tun safe kana cikin wannan ofishin. Ko abinci ba ka ci ba.” “Rayyan, idan ka gama maganarka, ka fita.” Rayyan ya yi dariya. “Wallahi kai mutum ne mai wahalar zama da shi. Wata rana za ka yi aure ka ga yadda za ka sha wahala.” Zayd ya ɗago kansa ya kalle shi. “Wa ya ce maka ina shirin aure?” “To, ai ba sai ka shirya ba. Wata rana zuciya za ta yanke maka shawara.” Zayd ya girgiza kai. “Ka fita.” Rayyan ya miƙe yana dariya. “Allah Ya kawo wadda za ta iya jure maka.” Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya, Ameerah ta isa wani babban kamfani mai suna ZAYD GROUP. Ta shiga reception ta gabatar da takardunta. Bayan ɗan lokaci, aka kira sunanta. “Ameerah Safiyya?” Ta miƙe. “Eh, ni ce.” “Shiga wannan office ɗin.” Ta shiga tana ɗauke da takardunta a hannu. A cikin ofishin kuwa, wani mutum ne zaune yana duba kwamfuta. “Assalamu alaikum.” Ya ɗago kai. “Wa alaikumus salam. Zauna.” Ameerah ta zauna tana gyara zaman mayafinta. Ya ɗauki takardunta ya fara dubawa. “Kin karanta Business Administration?” “Eh.” “Kin taɓa aiki a wani kamfani?” “A’a, amma ina da ƙwarewar amfani da ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.