FreeArewaPen original
DAREN ALKHAIRI
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci ba makaryaci ba ne
Sample · Chapter 1
Ina cin abincin muna waya da Yusuf da ya shaida mini saura kaɗan ya shigo gida. Sai dai har na kammala bai shigo ba, ina son fita in jira shi a waje hakanan sai nake jin tsoro. Wayata ta yi kara na duba shi ne ya ce ya biya gidan Mama, har na fara tura baki ina kallon agogo sai na ji muryarsa yana kiran suna na. Na saki wayar na kwasa a guje na bude ƙofar. Sai na yi arba da shi yana tsaye rataye da jakarsa bakin bafulatani siriri dogo mai dogon hanci da Kanannaɗaɗɗiyar sumar kai. Na kai masa runguma, ya yar da jakar ya sa duka hannayensa ya rungume ni. Mun daɗe a tsaye yana kissing dina kafin na yi ƙoƙarin jan shi ciki sai sannan ya janye, ya ɗauki kallo na daga sama har ƙasa ya fara fadin irin kyan da na yi cikin sansanyar muryarsa da ke ƙara hura mini wutar son sa. Sai da na ga abin nasa ba na ƙare ba ne na kamo hannunsa zuwa Toilet sai da na tura shi na rufe, na koma bakin gado ina jiran shi. Ya fito daure da towel na taya shi ya shafa mai ya fesa turare sai ya sanya riga da *** na barci muka fita ya ci abinci. Muna hira ta tafiyar tasa da hasashen nasara da muke, ina ta hamdala don nasan yana fara aiki shi kenan ƙarshen matsala ta ya zo. Yana gamawa na fara hamma don na matsu mu isa gado don sati biyun nan a daddafe na yi su ina cike da bukata, ga kwaɗaita mini da ya yi ya samu kanshi na matsalar saurin kawowa da ƙanƙancewar gaba. Muka nufi daki ya hau gado ni kuma na tube kayan jikina na sauya da wata riga ta barci mai ruwan hoda iyakar ta gwiwa. Na shiga Bathroom na wanke bakina na fito na kashe hasken dakin na hau gado. Sai dai me ina jira Yusuf ya taɓa ni shiru sai numfashinsa na fara ji shedar ya samu barci. "Kan banten baƙin biri. Na tashi zaune na rasa me ma zan yi kai ba zai yiwu ba. Na miƙa hannu na fara shafa shi kafin na kwanta bayan sa na kankame shi ina sakin wani numfashi da zai ja hankalinsa. Sai dai me, cikin muryarsa mai sanyi ya ce "Bari mana Zee. Kin san na kwaso gajiya. "Kawai na zare jikina na fashe da kuka. Ai kam ya tashi da sauri ya kunna fitilar wayarsa. Ya ruɗe da tambayar abin da ya same ni, cikin kuka don na ma manta da zancen kunya na ce "Ka gama kashe mini jiki da kwaɗaita mini wannan dare, sai kuma ka dawo ka kwanta mini har kana kiran daren da daren alkairi. Wannan ne alkairin? Ya jawo ni jikinsa " Sorry my happiness my princess. Ki yafe mini amma wlh ina rungumar ki farkon dawowa ta sha'awa ta ta yi karfin da na kasa rike kaina kawai na ji na kawo. "Kan babbar butar mai shayi. Na tattakura na ture shi na fashe da kuka. Dai dai da jin takun mutane ni da shi gaban mu ya ce ras! "Leka ki ga mene ne? "Muryar sa ta ratsa shirun da ya gifta.Ban motsa ba aka haske mu da wata fitila mai haske tare da bayyanar w...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.