GIDAN DALA(Where Power Rules,Secrets Survive,and Love Becomes a Dangerous Game)Free

ArewaPen original

MysteryFreeOngoing

GIDAN DALA(Where Power Rules,Secrets Survive,and Love Becomes a Dangerous Game)

  • 1views
  • 3chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Am a writer,i dream while awake.

More from @huguma

Sample · GIDAN DALA TEASER 01

꧁༒♛ 𝑮𝑰𝑫𝑨𝑵 𝑫𝑨𝑳𝑨 ♛༒꧂◈━━━━━━━━♛━━━━━━━━◈Written by HUGUMATEASER ONE◈━━━━━━━━♛━━━━━━━━◈"Ki kalli fuskata ayrah" Maganan ta fita da wannan lallausar muryar tasa da bata da hayaniya ko kaɗan. Sai wani irin zurfi a cikinta dake sanya saƙon kalmominsa isa da wuri cikin jini ɓargo da zuciya gaba ɗaya.        ƙin ɗaga kanta tayi kaman yadda ya buƙata. Tana jin zuciyarta na wani irin bugawa tamkar tana shirin jin sautin zuciyartata ne a cikin kunnuwanta."Ba ni da abin da zan tattauna da kai" Ta furta da cikakken CONFIDENCE ɗin nan nata da ɓata bari ya mutu daga zuciyarta ba.         Wani mayaudarin murmushi imran ya saki. Wani ɓoyayyen murmushin gefan baki marar ƙarfi,amma yana da wani irin amo da tarin ma'anoni masu kaifin gaske. Ya sake taku biyu rak da suka zama masu wani irin nauyi da kaifin gaske a gangar jiki da zuciyar ayrah. Har ta dinga ji kamar zuciyarta na shirin jijjigowa daga ainihin mazauninta ta canza muhalli daga kirjinta."Amma kina da lokacin tattaunawa da duk wanda ba ni ba?" Yayi maganan da wani irin zafi cikin murya da amonsa,yana kafeta da nauyayan idanun nan nasa dake da launin zaiba mai ɗaukar idanun me kallonsa.      A wannan karon,da sauri ta ɗago da sauri kanta ba tare data shiryawa hakan ba."Excuse me?,Kana da wata matsala ne?" Dukka lafuzanta a wannan karon itama da zafinsu suka fita. Tana ganin baida wani hurumi ko dama a kanta. Bashi da wani iko da zai mata titsiye. Tana da ikon yin komai a sanda taso a kuma lokacin da taga dama."Eh,ke ce matsalata" Maganan ta tsaya tsakanin harafinsa na ƙarshe da kuma shurun da ya biyo baya a ɗakin.       Shurun ya zarce har tsakiyar ƙwaƙwalwarta. Kalmarsa bata samu kowacce ma'ana a cikin kanta ba. Hakanan bata buƙatar ci gaba da shaƙar iska iri daya ita da shi,don haka ta yanke shawarar wucewa kawai.          Ba zato,ba kuma tsammani taji tsintsiyar hannunta cikin lallausan tafin hannun nan dake da wani irin laushi da ɗumi. Fararen hannayen nan da batasan adadin sau nawa ta harare su ba a lokuta da dama. Sanda yake signing contracts. Sanda yke tabbatar da wasu hukunce hukunce. Sanda yake Approving miliyoyin dalolin da ba wanda yasan iyakacin adadinsu sai Allah."Imran!. ka sake ni" Ta furta da muryarta me zaƙin nan,amma a yanzu cike da wannan tsiwar tata.        Juya hannun nata yayi cikin nada wanda tsaf ya ritsa tsintsiyar hannun nata da yatsunsa. Siririn hannun da baida wani alamun ƙarfi ko ƙanƙani s tare da shi. Tsaf idan ya matsanta da matseshi zai karairayata."Kin san abin da ya fi bani mamaki a tare da ke?" Ya mata tambayar still ba tare daya saki tsintsiyar hannun nata ba. Hasalima yana jin kamar ya ƙarasa matseta ya karya ɗan sauran ƙashin dake lulluɓe a ƙa...

Continue reading free chapter

App exclusive

Continue “GIDAN DALA(Where Power Rules,Secrets Survive,and Love Becomes a Dangerous Game)” in the app

The author limited this story to mobile. Open the app to read, listen, and keep your place.

Download on the App StoreGet it on Google Play