FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Hot Love Dark Romance
Sample · SARTSE!
*SARTSE* -Amanar-Janafty- *Sayyid Legendspen* MAH/2026/001 FUTURE WRITERS ASSOCITION (FUWA) Sadaukarwa. RAMLAT ABDULRAHMAN MANGA (Mai Dambu) Gaisuwar SARTSE zuwa gareku Iyalan Fam. Alherin Allah Ya kai muku a duk inda kuke. Shafi na ɗaya (01) Labarin Sartse ƙirƙirarren Labari ne, ban a rubuta shi dan cin zarafin wani ko wata ba, idan akwai wanda ya yi shige sa yanayin labarinsa muna neman yafiyarsa akan hakan. Haƙƙin Mallaka nawane ni kaɗai. Kamar ko yaushe Book one zai kasance Free, Two da Three kuma zasu a paid, akan ƙaramin farashi. Shimfiɗa *Jihar Jigawa , Nageriya.* Jihar Jigawa tana daya daga cikin jihohin da aka kirkira a karkashin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a ranar 27 ga watan Agusta, 1991. An ciro jihar ne daga tsohuwar Jihar Kano, inda aka ba ta sunan "Jigawa" wanda ke nufin kasa mai tudu ko yashi, yanayin kasar da ya shahara a yankin. Jihar ta kunshi hadakar manyan masarautu guda biyar (5) masu tsohon tarihi, wadanda suka hada da: Hadejia, Kazaure, Gumel, Ringim, da kuma Dutse. Wannan ya sa jihar ta zama matattarar al'adu daban-daban na Hausawa da Fulani da kuma Mangawa. Ana yi wa jihar lakabi da Sabuwar Duniya saboda burin da aka sa a gaba na gina ta a matsayin jiha mai dogaro da kanta ta fuskar noma da kasuwanci. *ƙaramar Hukumar Dutse* Dutse birni ne mai dadadden tarihi a kasar Hausa. Asalin sunan garin ya fito ne daga manyan duwatsu da suka mamaye yankin. Kafin kafuwar jihar Jigawa a shekarar 1991, Dutse tana karkashin jihar Kano ne kuma tana daya daga cikin tsofaffin gundumomi masu daraja. Birnin na da sarauta mai karfi wato Masarautar Dutse, inda sarkin garin ake kiransa da "Sarkin Dutse." Tarihi ya nuna cewa mutanen farko sun zauna ne a kusa da wadannan duwatsun domin samun kariya daga makiya a lokacin yake-yake. Yanayin Girman Garin a Taswirar Nigeria Dutse tana nan a Arewa maso Gabashin Najeriya. Haka A taswirar jihar Jigawa, Dutse tana tsakiya zuwa kudancin jihar. Ba birni ne mai matukar fadi kamar Kano ko Kaduna ba, amma yana bunkasa cikin sauri sakamakon zama babban birnin jiha. Yanayin garin akwai zafi sosai a lokacin rani, sannan akwai hunturu mai ratsa jiki saboda duwatsu da kuma kusa da hamada. Haka a bangaren Sana'ar Mutanen Garin Mutanen Dutse galibi Hausawa ne da Fulani, don haka sana'o'insu sun hada da • Noma: Shi ne babban jigo, musamman noman gero, dawa, wake, da kuma shinkafa a wuraren da akwai ruwa. • Kiwon Dabbobi: Ganin cewa akwai Fulani sosai a yankin, kiwon shanu da awaki sana'a ce mai matukar muhimmanci. • Kasuwanci: Akwai manyan kasuwanni inda ake hada-hadar amfanin gona. • Aikin Gwamnati: Kasancewar sa babban birnin jiha, akwai ma'aikata da dalibai da dama (musamman saboda Jami'ar Tarayya ta Dutse - FUD). Takur Site unguwa ce da ke z...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.