FreeArewaPen original
RAYUWAR SUBAI'AH Part 5
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Littafan marubuciyar 1-RU'DANI 2-BABBAR HUJJA 3-KWATAR KAI 4-RAYUWAR SUBAI'AH 5-MISTER MASHI 6-WATA SAKAYYAR.... 7-KUN TA'BA JIN AN KAMA MAYYA A GRA? 8-ZUWA LEGOS BA KAJIN TURANCI WATA LUKUTAR MASIFA CR 9-A GASKIYA WASU 'YAN UWAN SUKE BAYAR DA KAI. 10-YO WA YA'KI BANZA ...
Sample · RAYUWAR SUBAI'AH Part 5
*KATA'I**Part 5**FATIMA DAHIRU FUNTUWA BINTA* Misalin ƙarfe goma na dare, Subai'ah na kwance bayan ta saka kayan barci a jikin ta, kawai abinda ya faru tsakanin ta Nazeer ke dawo mata a cikin zuciyar ta, tana kamanta abin da inama ace ni matar shice, Tabbas dana nuna mai soyayya irin wadda ko a mafarki bai santa ba, woyyo Allah ga jikinshi mai masifar laushi, da gashin ƙirjin shi mai santsi, humf! Harna tuna lokacin da nake shafar fatar jikin shi, ya Allah ka mallaka min Auncle Nazeer a matsayin muji na, domin gaskiya bazan iya aikata zina ba. Hannun ta ta kai ta shafi ƙirjin ta, taji kamar sun ƙara ciccikowa, a fili ta ce Allah ka mallakamin Nazzir ya zama mujina, ni kuma in mallaka mashi waɗan nan. Tayi saurin kauda tunanin tare da lumshe idanunta da nufin yin barci. Ƙarar wayar ta yasa tayi saurin buɗe idanun ta. "To waye kuma ke kira na yanzun da dare?" Ganin baƙuwar number yasa ta ɗaga tana sauraron taji waye ya kira. "Badai harkin fara barci ba?" abinda ya fara ce mata kenan. Gaba ɗaya muryar shi ta fara neman ta jefa ta cikin rikici, ta ce "Auncle ina ka samu number ?" Ya ce "Nida nake so harkin yi mamakin inda zanbi in samu number ki? Kedai bakin hanani jikin ki ba, saboda kinga ina buƙata sosai, shikenan tunda haka kike so, ni dai a matsayin ƙanwa na ɗauke ki, ke kuwa bansan a wane matsayi kika ajiye niba,Tamkar baki yarda dani ba, ƙirjin naki da zaki bani in taɓa, shine yasa kawai kiketa wasan ɓuya dani, amma aini na baki nawa har kika kwanta kuma kika shafa shi, hakan ya nuna yadda ni na yarda dake ke baki yarda dani haka ba." Ta ce "Auncle ba haka bane, gaskiya ina jin tsoro ne, kuma yin hakan bai dace ba haramunne. " Ya ce "Subai'ah ni bance zanyi maki wani abu ba, kuma saboda na yarda da kene, kuma ƴar uwata, Subai'ah ba zan cutar dake ba, amma ni gashi yanzun ina cikin wani hali ke kuma kin kasa taimako na, Subai'ah kina so in kwanta ciwo ne? Tabbas yau bazan iya barci ba idan banganki ba, don Allah ya za'ayi in ganki? ".....
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.