Free chapter · Read without an account
Rayuwar Amal 3&4 na A'isha Abdullahi Yabo
Wata biyu kenan da haɗuwarsu da saurayin da bata san sunansa ba, tunaninsa ya ka sa fita a ranta, har wata 'yar rama tayi, ita ba ƙawaye ba ba tada abokiyar shawara da zata tunkara da maganar kodan samun mafita. A ɗaya ɓangaran kuma shirye shiryen bikinta ake tayi har an kawo lefe an sanya rana sha biyar ga watan Rabi'ul Awwal, Wanda dai dai lokacin za za ayi bikin hardarsu, wannan damuwar ta taru tayi mata yawa sai rama take yi a tsayi,
Ranar dai Umma gajiya tayi ta rutsata ɗaki tana tambayarta "wai Amal me yake damunki?
kwana biyun nan na rasa gane kanki duk da ba mai surutubace ke amma yanayinki ya sauya, damuwarki tayi yawa, kin rame sosai me ya ke damunki"?
Amal ta dubi Umma tana murmushi da ƙoƙarin ɓoye damuwarta ta ce; "Umma ba abunda ke damuna"
"ban yarda ba Amal zurfin cikinki dai bazai barki ki faɗa ba"
"Da gaske fa Umma ba komai"
"Ai shi kenan tunda kinƙi faɗa Allah ya sa hakan ne" ta miƙe tana faɗin "zan shiga maƙota na yi barka idan su Nafisa ('yan-uwanta) suka zo ki ce su jirani ba daɗewa zanyi ba"
"To Umma sai kin dawo, Umma ta fita Amal ta koma ta kwanta tana tunani.
*******************************
Tafi suki ita da Hansa'u da suke aji ɗaya, sun fito makaranta za su gida suna kawowa daidai wani ƙofar gida Hansa'u ta ce; "Amal ni kam na kawo gida sai mun haɗu da yamma"
" to Hansa'u ki gaida Iya"
"za taji" Hansa'u ta faɗa tana shigewa gida,
taku ɗaya zuwa biyu tayi taga mutum agabanta, ƙafafunta suka dinga rawa bugun zuciyarta ya sauya, bata taɓa tsammanin sake ganinsa ba, zuciyarta na umartarta da ta tafiyarta sai dai ta kasa bin umurnin zuciyarta, tayi ƙasa da kanta tana wasa da zoben hannunta, murmushi yayi ya na faɗin "kiyi haƙuri na tsorataki ko"?
shiru ta masa, ya riƙi kai "kin fiya yin shiru-shiru, ko kuma ni ne ake yiwa ban sani ba, da fatan kina lafiya"? "Lafiya kai," ta amsa ma sa can ƙasan maƙoshi"
"Alhamdulillah hakan ake so, na sha wahala sosai wajan neman inda zan sake ganin ki, da ya ke ni mai sa'a ne na zo wajan abokina tun kan na ƙarasa gidan sai na hangoki kuna tahuwa ke da wata sosai na ji farin ciki ya lullubeni"
murmushi ta yi sai dai ta kasa yi masa magana, shima murmushi ya yi kafin ya ce; " ba zaki ce dani kumai ba ko? Oh ni Ahmad wannan rashin magana haka, to ki taimaka ki faɗa min sunanki, ki kuma bani kwatancin gidan ku, an jima sai na zo mu yi magana a tsanake kinga bai kamata na tsayar da ke muna magana kan hanya ba"
a tsoraci ta kalleshi, cikin mamaki ya ce; "me ya faru na ga kin tsorata"? Cikin sanyin murya ta ce; "kayi haƙuri ba abarinmu zance, Kuma... Sai kuma ta yi shiru ta kasa ƙarasa maganar, Cikin fargaba ya ce; "kinyi shiru ki ƙarasa maganar ki" ta buɗe baki za ta yi magana idanunta su ka sauka kansa ta ɗora hannu a kanta cikin tsananin tsoro ta furta "Innalillahi Baba shi kenan ni yau tawa ta ƙare"
"Me ya faru?" Jikinta ya dinga karkarwa kamar an kiɗa gandi Ahmad ya kai dubansa wajan da take kallo ya hango wani tafe ya sake juyowa da kallonsa zuwa wajanta shi kansa a tsoraci ya ke ba wai dan ganin mai tahuwar ba a'a abinda take son faɗa masa ne ya ke ci ke da fargaban me za ta faɗa masa.?
Fulani