Free chapter 路 Read without an account
8
by Sadik Abubakar 路 SAHURA 馃挅
Sadik Abubakar
Lafazi Writers
Wattpad @sadikgg
*SAHURA 08*
To bayan sati daya ke nan da komawa hutun zangon karatu na farko, Faruk ya yi shiri ya 蓷auki Sahura, kai tsaye ya nufi makarantar da Hafsat take zuwa, wato '*NUSAIBA ACADEMY*'. Office 蓷in Principal ya nufa kai tsaye, da yake da ma shike zuwa biya wa Hafsat kudin makaranta a duk lokacin da bu茩atar biyan ku蓷in ta taso.
Bayan sun gaisa da Principal din, Faruk ya ce, "Ranka ya da蓷e sabuwar 蓷aliba ce na kawo maka."
Principal ya kalli Sahura ya ce, "Ya sunan ki?"
"Suna na Sahura." Ta fa蓷a tare da sunkuyar da kai cike da kunya.
Faruk ne ya karbe zancen da cewa, "Ta yi primary school a garinsu kafin wani iftila'i ya rutsa da 茩auyensu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar iyayenta. 'Yar kanwar mahaifina ce."
"Allah Sarki, Allahu Akbar! Allah Ya yi musu rahama Allah Ya shafe kura-kuransu. Ashe marainiya ce?" Principal ya fa蓷a yana mai nuna tausayi ga Sahura.
"Ranka ya da蓷e to yanzu wane aji ne zai fi dacewa da ita?" Faruk ya tambaya.
"Za ta kai shekara nawa yanzu?" Principal ya fa蓷a tare da duban ta.
"Ina tunanin za ta kai shekaru goma sha biyar." Faruk ya ba shi amsa.
"Ok, za a yi mata gwaji mu ga yanayin kwazonta. If she's good, we'll place her into SS 1."
Faruk ya ce, "To ba matsala Ranka ya da蓷e."
Principal ya fa蓷a masa duk abubuwan da ake bukata gabadaya har da kudin uniform, ya biya suka yi sallama suka nufo gida.
*_MONDAY_*
Safiyar ranar litinin din farko bayan kai Sahura makaranta, 茩arfe 7:15am Sahura ta gama shiri, ta saka uniform din makarantar, ya hau jikinta sosai gwanin sha'awa, tamkar da ma can 蓷aliba ce a makarantar. Misalin 茩arfe 7:30am, sun gama breakfast. Umma sai hararar Sahura take. Ita kuwa ko a jikinta domin idan da sabo kam to ita ai ta saba, don harara ma karamin abu.
To sai dai da alama Sahura ta dan fara samun sauki tun bayan zuwan Baba Abu, domin yanzu haka ma Umma ke yin girki, amma 'yan kananun aikace-aikacen gida wannan takan yi su duk da cewa Umma ta yi zuciya, ta daina saka ta, amma ita kuwa takan yi abin da ta ga ya dace, tunda da ma ta saba.
Faruk ne da kansa ya tusa su a gaba, tiryan-tiryan har zuwa makarantar, Hafsat ta wuce ajinsu, yayin da Faruk da Sahura suka nufi ofis din Principal a karo na biyu domin a ba wa Sahura aji. Sallama ya yi, suka shiga, Faruk ya zauna kan kujera, ita kuwa Sahura durkusawa ta yi a kan gwiwowinta, ta gai da Principal din. Shi ma Faruk mika masa hannu ya yi suka yi musabaha.
Nan Principal ya yi wa Sahura wasu 'yan tambayoyi tare da ba ta wani dan gajeren rubutu ya ce ta karanta masa, ba da bata lokaci ba ta kar蓳a, ta gyara zama ta fara karantawa daki-daki har 茩arshe. Faruk da ke zaune yana saurare, mamaki ne ya kama shi, yadda ya ji yarinyar sai zuba karatu take kamar saukar ruwan sama.
*_(Nima Sadik mamakin ne ya kamani hade da jin kaunar Sahura ta ziyarci Qalbina 馃挅馃槝)_*
Tana gamawa ta mi茩awa Principal takardar cikin nutsuwa da ladabi, shi ma din mamaki ne ya tamaimaye shi, an ce masa primary school kawai ta yi, kuma ma ta da蓷e da gamawa, sannan uwa uba ma makarantar 茩auye ce, amma kuma ga shi tana karatu tamkar wacce take SS 1 ko SS 2? Kai ko da ma a SS 3 蓷in ba kowacce yarinya ba ce za ta iya karatu fluently kamar ta. Babu shakka tana da 茩o茩ari sosai, tubarakAllah Ma Sha Allah!
Nan take Principal ya 蓷auko admission register ya rubuta sunan Sahura, sannan ya rubuta sunan a jikin wata 'yar takarda, ya kira masinjan sa ya ce ya kai ta SS 1A. Sannan ya juyo ga Faruk ya ce, "Yarinyar tana da 茩o茩ari, zai fi kyau kawai ta fara daga senior secondary school, ba sai ta yi junior ba. Ka dai ji yadda ta karanta wannan passage 蓷in, ba kowacce 蓷aliba ba ce a SS 1 zata iya yin yadda ta yi yanzu."
Faruk yace, "To shike nan babu matsala ranka ya da蓷e, duk yadda ka ce haka za a yi." Ya yi masa godiya tare da yi masa sallama ya baro Sahura a makaranta.
Misalin 茩arfe 10:40am na safe timekeeper ya ka蓷a 茩ararrawa, alamar lokacin tara ya yi, dukkan 蓷alibai sun fito domin yin break da wasanni.
Hafsat na fitowa ta fara dube-duben ajujuwa ko za ta ga Sahura. Ga tsammaninta JSS 1 za a kai Sahura, don haka 蓳angaren JSS din ta nufa, ta kewaye ajujuwan kaf! Ba ta ga Sahura ba. Sai ta dawo ajinsu domin ta 蓷auki ku蓷in break 蓷inta, tana zuwa daf da SS 1A sai ta hangi Sahura zaune a kan desk tana kwafar rubutu. Kanta ne ya yi wani irin kullewa yayin da wani bakin kishi hade da bakin ciki suka turnu茩e mata zuciya, idonta ya rufe har tuntu蓳e ta yi garin shiga ajin. Kai tsaye ta nufi daidai inda Sahura take zaune, tsayawa ta yi cak! A kanta, ta kasa magana. Sahurar ce ta yi mata magana da cewa, "Ashe kin san ajin da aka kawo ni?"
Murmushin ya茩e kawai ta yi tare da cewa, "A'a kawai dai na fito ne na duba ki sai na gan ki a nan, yaya Faruk ne ya ce a saka ki a wannan ajin ko?"
Sahura kai kawai ta girgiza mata alamar a'a, ta ci gaba da rubutunta.
"To ke ce kika za蓳i wannan ajin?" Hafsat ta sake tambayar ta, yayin da Sahura ta 蓷an dakata da kwafar rubutun ta ce, "A'a ba ni ba ce na za蓳a, Principal 蓷in ne ya ce a kawo ni nan."
Kai Hafsat ta girgiza ha蓷e da ta蓳e baki sannan ta ce, "Ai shike nan."
Nan ta zauna ta jira "yar uwar tata, har ta gama rubutun suka fito tare zuwa wajen da ake break da kuma wasanni. Hafsat ta ha蓷u da 茩awayenta, ta gabatar da Sahura a wajensu, sun yi farinciki sosai, sun kar蓳i Sahura hannu bibiyu da sakin fuska.
Su biyar ne 茩awayen hafsar har ita kanta, wato; Nusaiba ana ce mata Nucy, da Fatima ita kuma Teemah ake kiran ta, da Surayya, Soory shi ne nickname 蓷inta, da kuma Khadija ana ce mata Deejarh sai kuma ita Hafsar nata nickname 蓷in shi ne Hafcy. Sunan kungiyars *FIVE STARS GROUP *. An san su sosai a makarantar saboda tsananin tsokanarsu da neman rigima, idan suka sako yarinya a gaba sai ta ji ta tsani makarantar gaba蓷aya.
Kowacce daga cikinsu ubanta wani ne, ya isa magana, shi yasa suke abin da suka gadama. Idan ka gansu kusan shekarunsu 蓷aya, kansu 蓷aya, yanayin surar jikinsu 蓷aya, marasa kiba ne, tsigalallu ne sai tsiwar tsiya.馃槀
Ba wasu masu 茩o茩ari ba ne sosai wajen karatu, amma abin da zai ba ka sha'awa dangane da wa蓷annan yara shi ne, ba sa kula maza, hakan tasa ma duk saurayin da ya kwana ya tashi a makarantar yana shakkar tinkarar kowacce daga cikin su da maganar soyayya. Haka nan kuma basa aikata wannan muguwar 蓷abi'ar ta kangararrun 'yammatan 茩arshen zamani wato *_LESBIAN_*. Su dai ka bar su da rashin kunya da tsokana, wannan kam halin su ne.
Nan suka yi break tare da Sahura, ta saki jikinta tamkar ta saba da su, babu wani ra蓳e-ra蓳e, ta zama kamar da ma can tare suka fara makarantar. Sahura yarinya ce marar duhun kai, tana da sakin fuska da saurin sabo. Banbanci 蓷aya da ke tsakaninta da su shi ne, ita dai ba ta da tsiwa, hayaniya ko kuma rashin kunya. Sannan ba ta cika shiga sabgar shashanci ba.
Misalin 茩arfe 1:30pm na rana, timekeeper ya ka蓷a 茩ararrawar 茩arshe wacce ta ba su damar komawa gidajen iyayensu. Sahura da Hafsat tare suka dawo gida, yunwar makaranta ta kamo su, Hafsat da kyar take takawa saboda rashin juriyar yunwa.