Free chapter 路 Read without an account

Page 3

by Rahama muh'md Rufa'i Nalele 路 FITO NA FITO AKAN SOYAYYA TA

*Fito na fito*

*AKAN SOYAYYA TA*

Labari da tsarawa RAHAMA MUH'MD RUFA'I NALELE

*Haske writer's association*


Shafi na uku 03


Ban yarda wani ko wata ya d'ora min labari na akan shafinsa ba, ban amince ba, duk Wanda yamin hakan ya d'ora haramun tunda ba amincewa ta.


Sannan makaranta na, z na baku dama zaku iya tura labarin nan duk Inda kukaga dama, Ku Kan na yarje muku Dan nasan karanwata ne kawai naku bazaku Dora min Shi dan kasuwanci ba, babu hakan a tsarina.




Tunda Aliyu yake bai tab'a ganin gari me kyan Abuja ba, musamman gidan iyayen Dadynsa ayanzu.

Lokacin da suka iso gidansu ba qaramin gigicewa yayi ba, ganin irin daular da Dadyn nasa ya zuba a gidan, wani daki suka Kaisa sukace mai nanne d'akin sa..

Wato ciki da falo sai toilet da wani qaramin gu irin wajen ajiye mahimman abubuwa, komai akwai, dangin kayan gado katifa durowa TV kafet komai dai da kuka sani na amfanin rayuwa ba abin Dadyn nasa bai saka an saka masa ba daidai na amfanin yaro kamarsa tun kafin tafiyarsu daukosa.


Nan ya zaunar dashi Akan gado Yana cewa, HaYdaR nan shine dakinka shine Inda zaka dinga kwana, shin komai yayi maka ko akwai abin da kake so..

Rungumarsa yayi da cewa, "komai yayi Dady nagode sosai..

Yace ba godiya tsakaninmu HaYdaR yanzu tashi muje na nuna maka gidan kasan ko ina ko..

Toh yace Mai.

Nan suka fitto ya dinga nuna masa gidan lungu da tsak'o, kasance warsa babban gida ya tara ma'akata masu yima gidan hidima, duk sanda ya nuna musu Aliyun Yana ce dasu ga HaYdaR Yarona wannan shine babban d'ana, Dan haka Kusan dawa kuke tare, nan suka dinga kulasa cikin nuna qauna da soyayya..

Bayan yakaisa Shashinsa ya gani ya Kaisa na Laila nan ma ya gani, sai suka dire a dakunan ReeYA da Usman, daga nan sallah sukayi suka hade a daining, nan sukaci abinci cikin farin ciki da annushuwa..


Har dare suna tare da juna Inda Aliyu yake ta basu labarin karatunsa da abokansa da qanwarsa RaHinAT, komai sanda ya gaya musu a wannan rana.


Aliyu bai tab'a baccin nutsuwa ba irin na wannan rana, Abu d'aya yakema kewa shine yanzu ba gari d'aya suke da RaHinAT dinsa ba, shin yaushe zasu qara had'uwa da juna?, shine tambayasa.




Agefe guda kuma tunda Lailah taga yanda iyayen mijin nata suka karb'i Aliyu HaYdaR cikin so da kaunarsa nan taji hassadar hakan da tsanarsa ta kamata, nan taji tana San Haihuwa Kota halin k'ak'a, dan bazata tab'a yarda Aliyu HaYdaR ya samu wajen Zama agunsu ita bata Haifa nata ya samu ba, ta qara jin tsanar Aliyun ne lokacin da sukazo gidan nasu taga yanda mijin nata yake nuna masa qauna, tabbas tayi imani idan bata San nayi ba to zata Zama me bauta ce kawai agidan, sam baza ta dauki hakan ba, dolan dole tad'auki mataki...


Gashi bata isa fittowa ta nunama Aliyun tsana ba kasancewar alkawarin data daukarma mijin nata.. shuru tayi nad'an wani lokaci tana tunani, can tayi murmushi dan wani tunani da tayi, dole ta IYA TAKUN TA, sam bazata yarda ta nuna ma duniya cewa bata San Aliyun ba, zata bar hakan acan cikin ranta dan tasamu cinmu burinta.





Cikin wata hud'u, kauna da soyayya ta Shiga tsakanin Aliyu HaYdaR da Dadynsa da qannansa biyu da iyayen Dadyn nasa da qanwar Dadyn nasa wato aunty Khadija, ga kuma Y'ar ta SafiYYA Aliyu Yana qaunar yarinyar kamar yanda yake qaunar ReeYA da RaHinAT da Usman, duk suna qaunarsa sosai haka Shima yake qaunarsu, tabbas Aliyu ya samu komai daya Rasa, ga momynsa Laila, ga Dadynsa Alhaji Ahmad, ga kakarsa Hajjiya Binta mahaifiyar dadyn nasa da mijinta, ga Auntynsa qanwar Dadynsa Aunty Khadija, Yana kiransa da Auntyna ga qannansa biyu ReeYA da Usman..
















Yau shekararsu guda Kenan da rayuwa waje guda, har sun Saba da juna, Daga wannan lokaci ne kuma Dadyn nasa ya gama mai shirye shiryen tafiya skull zuwa kasar England Dan ya qarasa karatunsa acan kasancewar Aliyu HaYdaR akwai kwakwalwa, Yana San ya Zama cikakken d'an kasuwa, Inda zaije ya fara karatun nasa tare da yaron k'anin Dadyn nasa Wanda suke uba daya acan qasar England, sunan Yaran NajEEB, sa'an Aliyun ne, dake Shi Mahaifin NajEEB din Yana aiki acan England dinne hakan yasa Aliyun zai samu kulawa sosai acan din.. Mahaifin NajEEB din yazo ganin mahaifinsu ne kasancewar Shi mahaifiyarsa ta rasu yanzu mahaifiyar wansa Ahmad d'in yake gani a matsayin mahaifiyarsa kasancewarta abokiyar zaman mahaifiyar tasa, to zuwan nasa ne yaga nutsuwar Aliyu HaYdaR shine ya tambayi yayan nasa mezai hana ya bashi Aliyu ya tafi dashi can England ya qarasa karatunsa acan tare da d'ansa NajEEB, Jin hakan yasa yace zaiyi nazari ya bashi kwana biyu, to bayan ya gama nazarinsa sai yaga dacewar hakan, nan ya kirasa yace Mai ya amince.


Laila taji baqin cikin hakan sosai, tazo tacimma burinta kafin hakan.


Aiko da kuka sosai Aliyu HaYdaR ya rabu da Dadyn nasa da qannan nasa a falin jirgi, bayan Dadyn yayimai nasiha sosai akan karya kuskura yayi wasa da karatun nasa, domin shine rayuwarsa, musamman karatun addini, sannan ya kwantar da hankalinsa dole Shi da momynsa zasu dinga zuwa kawomai ziyara akai akai..

Toh yace mai.. haka sukayi bankwana da juna. 




Ashe lokacin Laila na dauke da cikin wata biyu da sati biyu, gane hakan da kowa yayi nan murna da farin ciki ta kama kowa, nan mahaifiyar mijin nata take gaya mata dama wani iko na Allah saika dauki dan rik'o sai kaga naka raban yazo maka..



Aiko hakan ce ma ta kasance da Habiba matar Zakari wacce suke rik'on RaHinAT, itama tana dauke da cikin wata biyu.

 Sai fatan Allah ya saukesu lafiya.




Bayan saukar Aliyu ya yaba da tarbiyan gidansu NajEEB, Yama Yaba NajEEB din Dan Yana da nutsuwa sosai kamar Shi, ga mamansa me San mutane ta nuna murnarta da farin cikinta na zuwansa, NajEEB Yana da qanne biyu Mata biyu, Seeyama da Shamsiya, haka dai Aliyu yaji mutanan sun kwanta mai arai..









A wannan lokacin ne kuma Zakarin ya samu canjin aiki zuwa Abuja, aiko Ahmad yaji dad'in hakan zasu kasance tare da juna, nan ya basa kyautar wani gidansa dake nan cikin unguwarsu, yace ya zauna abinsa anan, har kuka sanda Zakari yayi Yana mamakin halin Ahmad din.


Ganin girman gidan nan ya dawo kadunan ya d'auki kakanninsa wayanda suka rikesa ya dawo dasu gidan yace hakan zaifi mai nutsuwa da kwanciyar hankali idan duk suna tare awaje d'aya. wannan shine dalilin dayasa duk suka zama Yan Abuja..











Bayan shekara goma sha biyar. 


***     ***     ***     ***      



Kyakkyawar Budurwa ce ajin farko, bata cika k'iba ba Sannan baza'a sakata a Samun sirara ba, tana da dogun hanci da baki matsakaici, tana da Ido matsakaita irin na masu Jin baccin nan masu kyan kallo, tana da shape da diri na daukar hankali, jar macece irin wannan farin me matuqar kyau, atakaice dai tana da wani sanyayyan kyau Wanda ana kallanta kyahun Yana qara bayyana kansa.


Wacece Kenan? SafiYYA, sunanta SafiYYA, tana da matuqar shagwab'a ga rawar kan tsiya, Saidai akwai ta da fad'in gaskiya, Wanda hakan ya kasance tarbiyan mahaifiyarta ce, ta nuna Mata mutun ya ginu akan fad'in Gaskiya RAYUWA CE, idan kuma ya ginu akan qarya Zama yake kamar matacce


Tana cikin supermarket ne tana siyayyan kayan make-up, dasu turarurruka, nan taji wani sanyayyan kamshi ya bugi hancinta daga bayanta, ta juyo da sauri tana mamakin wannan sayyanyan kamshi daga ina haka.


Wani kyakkyawan saurayine yake duba turarurruka shima..


Saurayin ya hadu ne ajin farko, Wanda tunda SafiYYAH take a duniya bata tab'a ganin saurayin da yayi mata 馃挴 irinsa ba, ya had'a komai ne Wanda ba duk d'a Namiji ba... Bai cika tsayi ba sannan baza'a kirasa da gajere ba, Bai ciki k'iba ba sannan baza'a kirasa da siriri ba, ga zubi na halitta Wanda dole saika shagaltu wajen kallan wannan zubin nasa, uwa uba kyansa na musamman ne, ga wani lafiyayyan fari da yake shinfide a fartarsa, wato Jan fari irin nata, kallo daya zaka masa kace dashi kyakkyawa. Riga da Wando ne irin kayan turawa a jikinsa, sai wata jaket wacce tazo Mai har gwiwa wacce ta qara masa kyau, kafarsa dauke take da takalmi irin na turawa me sadar gaske..


SafiYYA daskarewa tayi a tsaye, ita gani take tafi kowa had'uwa, sai gashi Tayi gamo da d'a Namijin daya tafi da komai nata.


Tunda ta zuba Mai Ido ta kasa dauke idon nata akansa, candai ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya tace... _Tsarki ya tabbata gareka Allah daka halicci wannan bawa naka, *La'ilaha'illahuwar rahamanurrahim Allahu la'ilaha illahuwal hayyul k'aiyum,* Ya Ubangijina Yayi min dari bisa dari, idan ya kasance Shi musulmi ne Wanda yake da kyakkyawar ZUCIYA to nikam ina sanshi ina San kamin kyautarsa a matsayin mijin aurena, ina sanshi ya Rabbu kabani Shi albarkacin wannan addu'ar da zan qarayi ta La'ilaha'illahuwar rahamanurrahim, Allahu la'ilaha illahuwal hayyul k'aiyum, Ya ubangina kasa ya Soni ya qaunace ni fiye da yanda naji sanshi da qaunarsa ayanzu, kasa ya Zama alkairi na nima na Zama Alkairinsa, duk iya wiya murayu da juna cikin so da qaunar juna...._ Tana kawowa nan cikin addu'ar tata nan ta d'aga hannuwanta biyu ta tofa addu'ar tare da shafata da bama Kanta tabbaci Allah ya jita kuma ya Amsa mata... 


Aiko dai-dai lokacin HaYdaR ya juyo dan kallanta, Dan tabbas yaji a jikinsa akwai me kallansa, karaf ko idansu ya had'u dana juna, wanda nan take gabansu ya buga wanda yake nuna akwai ayar tambaya...


Cigaba yayi da duba turarurrukan Yana daukar Wanda yake so Yana sakawa cikin d'an kwandan nasu, itakam tagama daukar abin da take so Dan haka zuwa tayi wajen biyan kudi ta basu ATM dinta.


Bayan sun dauki kudinsu sun bata kayanta nan ta fitto waje ta tsaya jiran fittowarsa.


Can sai gashi ya fitto zai Shiga cikin mota, da alama ma Yana tare ne da direba ne, Dan baya ya bude dan Shiga...


Ai SafiYYAH na ganin haka nan tayi saurin cewa, Jimana My blood...

Cak ya tsaya da juyowa gareta, bayan ta qarasa garesa taci gaba da cewa "Amincin Allah ya tabbata agareka. 

Yayi murmushi Jin dad'in muryarta, nan ya bata Amsa da cewa, "Tare dake.


Tace Dan Allah kozan iya sanin sunanka... tsaida kallansa yayi sosai akanta, ita dinma kallan nasa take da yanayin shagwab'e, yace "HaYdaR, tace "Gud suna me dad'i, shin a ina kake da Zama, sannan miye aikin ka, kuma Kana da Mata ko Kai saurayi ne, in Kai saurayi ne shin Kana da budurwa..


Shuru yayi Mata itama shurun tayi tana kallansa, ganin shurun nasa yayi yawa hakan yasa taci gaba da cewa.. kaga ni sunana SafiYYA, yarinya Danya shakaf Y'ar shekara ashirin da d'aya, bana Kula samari dan ina da chose akan Wanda ya dace na Kula, qawayena biyu ne a duniya wato RaHinAT da ReeYA, suna cewa na fiya sututu shin da gaske ina da surutun..


 Cikin mamakinta yace, "kad'an haka, tace "toh da sauqi tunda da alama Kai hakan bazai dameka ba, yanzu dai kabani amsa ta, tambayar da nayi maka a farko, yace "meyasa kike San kisan koni waye, aikina da batun sanin ina da Aure ko Budurwa..


Sosa qeya tayi da kallansa kad'an cikin shagwab'a tace "Maganar gaskiya kayi min, ina Sanka ina San KA AURE NI...


Cikin tsoro ya waro ido da cewa "what.. Mene? Aure fa kika ce. 

  Cike da shagwab'ar tace "Yes Aure, ina San Ka Aureni dan yanzu yanzu naji Sanka da qaunarka, kallo daya nayi maka katafi da zuciyata, yanzu Ka Zama farin cikin RUHINA, kawai kayarda da Soyayya ta dan nidai bazan barka ba, saboda... Sai ta tsaya anan tana kif kif da Ido. 


Yarinyar ta Gama bashi mamaki, nan yaja numfashi da cewa, "Saboda.... Nan tayi saurin Katse Shi da cewa "Saboda mun dace da juna, shin banyi maka bane, Ka kalleni fa wata zankad'aziya dani, mutane da dama suna nuna soyayyarsu agareni, ni ko kallo basu isheni ba, ina tabbatar maka bazaka samu wacce zata zarceni a soyayyarka ba..


Yace "Allah ko, tace ko shakka babu..


Juyawa yayi dan shiga motar, nan tayi saurin cigaba da cewa, Kasan Allah kadakata, karkama kanka sakakkiya, idan kayi wasa sai na roki Allah ya ciremin Sanka, daga wannan lokacin ka Shiga uku, danko kazo min da batun soyayyarka nan gaba bazan saurareka ba gwara yanzu kayi na'am da soyayya...


Qara juyowa yayi ga kallanta, zaiyi magana ta rigashi da fad'in.. Kan kace wani abu naci arzikin MANZAN ALLAH kabani aran wayanka na minti daya kawai..


Shuru yayi Mata na secon goma Kana ya zaro wayar tasa daga ajjihu ya miqa mata, ta karb'a tana cewa, Masha Allah.

Nan tasaka mishi numbarta ta kallesa Wanda kawai Shi zuba Mata Ido yayi, Shin zan iya sanin wane suna kake San Kiran masoyiyarka dashi, Yace "me yasa kika tambayeni, tace "nasaka maka numbatace nake San saka maka suna.. shuru yayi, ganin hakan taciga da cewa, koda yake bar sunan naka, bara na saka maka sunan daya dace, Shi dai shurun dai ya qara mata, nan ta save mai da *KAUNA TA* Kana ta Kira numbar, nan wayarta tahau ringing tana Jin hakan ta kashe da miqamai wayar tasa tana cigaba da cewa, karka manta da Sunana SafiYYAH, SaffiYYA matar HaYdaR, shin ya kaji had'in..

Murmushi yayi da cewa "Sam bai had'u ba, waro ido tayi da cewa, "Ni Kam ya had'u, kuma ba masoyan da sunansu zaifi namu dacewa adai wannan lokacin, kaga Shiga motarku ajaka, kamar yanda kadda ta hadamu ayau haka zata qara hadamu gobe, kuma Insha Allah.... Sai tayi shuru da d'aga hannuwanta biyu Sama alamar addu'a, cikin ranta tace, _Allahumma inniy as aluka BI anniy Ash'hadu an la ilaha illa anta, Al'ahadu Assamadu, Allaziy lam yalid walam yulad walam yakun lahu kufuwan Ahad, Ya Rabbi albarkacin wannan addu'ar Ka qara had'ani da wannan bawa naka, Ka kawoshi Inda nake na gansa naji dad'in da nakeji ayanzu da nake gabansa_ 


Tana zuwa nan ta shafa da kallansa taci gaba da cewa, Insha Allah kamar yanda na gaya maka, kaddara zata had'amu gobe kuma Kaine zakazo Inda nake dan haka sai anjima, tana gayamai hakan ta juya da taran adaidaita ta shige tana gayamai Inda zai kaita tabarshi nan tsaye.


Tunda yake bai tab'a had'uwa da mace kamarta, tana da wayewa yarinyar kamar baturiya, girgiza kai kawai yayi da Shiga motar direban yajasu.




Direct gidansu RaHinAT tayi, bayan ta gaisa da momynsu zama tayi akan kujerar tsakar gidan da kallan momyn nasu tace, momy ki tayani murna yau nayi saurayi, Habiba ta kalleta tace "toh SafiYYA na tayaki murna, Allah yasa na Aure ne musha biki nan kusa, murmushi tayi da da cewa Amin aranta, a fili ko cewa tayi, wallahi momy baki gansa ba kyakkyawa dashi fari me hanci ni dai kawai yayi min.. tace Allah yasa ya Zama alkairinki..

Amiin tace da kallan ummi qanwar RaHinAT d'in ganin tana Mata dariya, taci gaba da cewa, waini sa'arki ce da zakina min dariya, tace "aa aunty Soffy kawai nayi mamaki ne Dan ban tab'a ganinki da saurayi ba, abin yaban dariya da kikace yau kikayi sauri kuma kina maganar kina sanshi ayau d'in, Anya kuwa bame asiri bane daya Shiga ZUCIYAR KI lokaci guda haka... harararta SafiYYA tayi da tashi ta Shiga d'akin RaHinAT ta fad'a Kan gadanta batare data bata amsa ba...


Ita dai zuciyarta na cike da farin ciki, nan ta kalli RaHinAT tace "Qawata yau nayi gamo da saurayin daya sace zuciyata..


RaHinAT dake Safa hoda ajikin madubi nan tayi saurin juyowa ta kalleta tace dakata kan kiban labari bara na baki labarin mafarkina..


RaHinAT kyakkyawar mace ce itama ajin farko, fara ce sol tana da Ido fuskarta me Dan fad'i ce, tana da wushirya, ta d'an fi SafiYYA jiki kad'an, Amma tsayinsu kusan daya ne, kallo daya idan Kayi mata zakaso qarawa, saboda tana da fuzgaggen kyau, Wanda yake daukar hankalin mutane lokaci daya, ita zaqin murya ne da ita, yayin da ita muryar SafiYYA take da dad'i, gata itama da diri abin kawai sai Wanda ya gani, 

Cikin ita da SaffiYYAH masu sansu Maza ne kawai zasu iya tantance wacce tafi kyau..


Nan taci gaba da cewa, Yanzu na tashi daga bacci, nayi mafarkin Yayana ALIYU, wai munyi Aure harda Yara biyu, gaskiya SafiYYA bazan Auri kowa ba sai Yayana ALIYU, kuma...


"Kuma in bashi kika Aura ba bake ba Aure ko, SaffiYYAH ta kashe Mata maganar tata da fad'in hakan, tana cigaba da cewa, wannan karatun naki mun dad'e da haddace Shi nida ReeYAH. Dan haka please munji Shi kike so kidena damummu da batunsa, Dan gata d'aya zakima kanki shine addu'a, Allah ya sadaku da juna, wannan za kifi bama mahimmanci kafin batun ki ganku matsayin Ma'aurata.. 


Cikin sanyi RaHinAT tace "yanzu shekara goma sha biyar rabona dashi, tabbas babu me qara sadamu da ju sai ubangiji, ko yanzu ya kamanninsa suke Oho, SafiYYA tace "amafarkin naki baki ganin fuskarsa ne, tace ko kad'an nidai kawai gangarjikinsa nake gani...


SafiYAH taja numfashi da gyara Zama ta kwashe komai daya wakana tsakaninta da HaYdaR ta gaya mata..


RaHinAT tace tir miki, Sam ba'ayi Namijin da zanje nace dashi ina sanshi ba, ji abin da kikayi Sam ba tsari, ba aji, kin zubar mana da mutuncinmu Mata.

  SafiYAH tace kinsan Sarai ni ban iya munafuncin barin abu araina ba, da zaran Abu yayi min nan take nake fad'a, imma baiyi min ba, nan nake bayyanawa, Dan haka ke kika San wani tsari da wani aji, idan Yayanki ya bayyana agareki Kar kice Mai ya aureki, haka kina kallon ruwa kwad'o zai miki kafa, nifa banga wani aibu aciki ba, Dan mace tace tana San Namiji, kinga sai anjima karki b'ata min farin ciki na..


Haka bata saurari cewar RaHinAT ba ta ficcewarta abinta.


Binta da kallo RaHinAT tayi, itakam Allah ya sa'ni bazata iya abin da SaffiYYAH tayi yanzu akan HaYdaR ba, In da ace itace kokari zatayi wajen ganin Shi ya Fara cewa Yana Santa Amma Banda ita ta Fara cewa tana sanshi, gaskiya itakam agareta zubar da aji ne yin hakan, sannan zataso taga HaYdaR din, taga ya yake da SaffiYYAN ta rikice akansa har haka....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.