Free chapter · Read without an account

BUDEWA

by AREWA MEDIA WRITERS · RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA

Dandalin sada zumunta wata sabuwar duniya ce da ba mu gama sanin hakikaninta ba, duniya ce mai cike da annashuwa da raha da saukin sadarwa da saukin rayuwa da saukin mu’amala da saukin abota da hanyoyin samun fadakarwa da gabatar da harkokin rayuwa ce, a wani tsari mai kama da hakika, kai ba kama ba ne rayuwa ta hakika ce.


Sabbin kafafen sadarwa na zamani sun zame mana jiki a rayuwarmu ta yau da kullum, har ma ya kasance jama’a ba su cika kallonka a matsayin wayayye wanda ya san me ya ke yi ba, idan har ya kasance ba ka amfani da daya daga cikin shafukan sadarwa na zamanin.


Kai har ma kamfanoni da ma’aikatu sun kasance suna amfani da kafofin sadarwar zamani wajen tallata hajojinsu ko ayyukansu ga al’ummar duniya.


Duba da irin yadda kafofin sadarwar zamani suke da tasiri a wannan karnin, ya sa muka rubuta wannan littafin domin sanin ha}i}anin hakan da kuma Fadakarwa, wayar da kan al-umma, da jan hankali ga masu amfani da ita, jan hankali ga iyayenmu, jan hankali ga shugabanni game da halin da samari da 'yanmata suke ciki, yadda suke gudanar da rayuwarsu.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.