Free chapter · Read without an account

YADDA IYAYE ZA SU IYA SANIN ABINDA 'YA'YANSU SUKE YI A SOSHIYAL MIDIYA

by AREWA MEDIA WRITERS · RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA

Dandalin Soshiyal midiya ya bai wa matasanmu wata sabuwar hanyar fadakarwa da karantarwa

da tunatarwa.

A duk inda aka ce samari da ’yanmata sun hadu, a yanayin da ba a ganin juna, a yanayi mai jefa hankali da zuciya wata nahiyar nishadi mai girma, to, dole a samu ’yar karkata.

Don haka ya zama wajibi ga iyaye manyan yayye, 'yan’uwa, da su saka ido ga rayuwar 'ya'yansu, 'yan’uwansu a soshiyal midiya don su san da su waye suke mu'amala.

Abin da iyaye ya kamata su kara sani, Dandalin sada zumunta wata sabuwar duniya ce da ba mu gama sanin hakikaninta ba, duniya ce mai cike da annashuwa da raha da saukin sadarwa da saukin rayuwa da saukin mu’amala da saukin abota da hanyoyin samun fadakarwa da gabatar da harkokin rayuwa.

Haka zalika hanya ce da ke saurin lalata tarbiya, dagulawa matasa tunani, canza masu manufofin rayuwa daga rayuwa mai kyau zuwa marar kyau, koya musu Cuta, Yaudara, Karya, Maula da sauransu.

Soshiyal midiya rayuwa ce mai kama da ta hakika, kai ba kama ba ne rayuwa ta hakika ce, wanda hakan ya sa dole iyaye su kula da 'ya'yansu da kyau.


Abin da ya kamata iyaye su fara sani game da 'ya’yansu shi ne, susan sunan da yaronsu, yake amfani dashi a kowacce kafar sadarwa ta soshiyal midiya.

Iyaye su dinga bin diddigin duk wani fostin din 'yayansu don tabbatar basu yin fostin din da bai dace ba. Akwai samari da 'yanmata da dama, da suke boye kansu, ba su bari 'yan uwansu ko wani makusancinsu ya san sunan da suke amfani dashi a soshiyal midiya.

Wasu suna yin hakan ne don boye kansu irinsu ne masu yin rayuwar boye, akwai wadanda rashin gaskiya ke hana su bayyana kansu walau sunansu na asali, hotunansu da sauransu don abun da suke aikatawa ba mai kyau ba ne.

A yanzu babu manyan kafofin sadarwa da matasa suke hawa sosai kamar kafar Facebook, Whatssap, Instgram da Tiktok, dan haka zan yi bayani a iya wadannan kafafen sada zumunta da yadda iyaye za su bi domin su kula da 'ya'yan su.

Na farko Facebook kafar sada zumunta ce da ta ke amfani da lambar waya da lambobin sirri wanda idan ba ka da su lallai ba zai bude maka ba, don haka kafin ka samu damar sanin me mutum yake yi a wannan kafar sai ka mallaki wadannan abubuwa nashi guda biyu.

Domin iyaye su binciki yaran su ta wannan kafa sai sunyi abu biyu zuwa uku.


Na farko, zasu karbi wayar yaron, ko yarinyar su hau kan Facebook da tasu wayar ba wayar yaran ba, da zaran uba ya hau sai ya dora lambar wayar yaron a Facebook wurin "password" kar ya saka komai sai ya je kasa ya yi "forgot password" domin samun damar da za su turo "code" ta wayar yaron, suna turowa sai uban ya dauka ya dora shi a wayar shi, yana budewa a wayar zai bashi zabi guda biyu, shin yana so duk sanda ya zo shiga "Account" din kawai da ya taba "account" ya bude ko kuwa yana so sai ya saka "password", to sai mahaifin ya dauki zabi na farko, shikenan "account" din zai bude.

Sai mahaifin ya koma ga wayar yaron ya goge "code" din da aka turo a wayar saboda kar yaron ya gani, sannan hakan ba zai hana yaron hawa "Account" din ba, da zaran ya baiwa yaron wayar, zai iya hawa "account" din lafiya lau ba tare da ya gane an yi wani abu ba, shi ma kuma mahaifin zai hau Facebook din yaron ba tare da yaron ya gane ba.

|angare na biyu, shi ne bangaren WhatsApp wato WhatsApp "Monitoring Hack", idan kana son binciken WhatsApp din 'yarka ko don ka domin ka ga abin da suke yi matakin farko shi ne wannan za ka yi amfani da "Application" mai suna "Whats Web" za ka shiga "Application" mai suna "PlayStore" ka yi "Download" din "Application" mai suna "Whats Web" bayan ka dauko shi sai ka bude shi, kana bude shi, zai


bayyanar maka da abubuwa da yawa sai ka danna wurin da aka rubuta, "Whats Web" kana danna wa za ka ga yana "Loading", sai ka dan jirashi ya gama.

Wani lokaci za ka ga yana sakar maka talla haka, kuma yana "Loading", to kana iya "Exit" din tallar, bayan ya gama "Loading" zai bayyanar maka da wani shafi da alamar "Scanner", to anan za ka samu wayar shi wanda kake so ka bincika cikin yaran naka sai ka hau WhatsApp dinshi ka bude wani wajen da za ka ga yana da alamar "Scanner" "QR-Code" sai ka yi "Scanning" din wannan alamar "Scanner" din na wayarka.

Daman kuma Data dinka a bude take, daga nan za ka ga wayarka ta fara "Loading", zuwa wani lokaci kawai za ka ga gaba daya WhatsApp dinshi ya bayyana a wayarka.

Za ka ga dukkannin "chatting" dinshi da komai, za ka dinga la'akari da duk lokacin da ka lura ya hau WhatsApp to kai ma a lokacin sai ka hau, kana hawa komai na WhatsApp dinshi zai sauka a wayarka za ka ga komai yana saman WhatsApp dinshi kai ma kana saman shi, ba zai taba ganewa ba.

Idan ba ta hanyar fasahar zamani ba, yana da wahala ka iya gane me yaronka yake ciki a soshiyal mediya, kasancewar duk wani soshiyal mediya yana amfani da lambobin sirri wanda idan ba mutum ya fada maka ba, ba za ka iya gane me ya ke ciki ba, sai dai idan za ka bude "account" da sunan mace ka bibiyi yaron naka idan kana zargin sa da bin mata, idan kuma mace ce ka bude "Account" da namiji da sauransu.

Bugu da kari, a kullum kamfanin "Google" suna cikin kokarin ganin sun kirkiri "Applications" masu amfani da ban sha'awa wadanda suka san lallai jama'a za su ji dadinsu, wannan "Application" din da zan yi bayani yanzu, "Application" ne da kamfanin "Google" suka kirkira na musamman saboda iyaye su kula da yadda yaransu suke gudanar da wayoyinsu na hannu da kula da tarbiyarsu, da rayuwar da suke yi a soshiyal Midiya, don wannan dalilin ne suka kirkire ta ba don wani dalili ba, kar ka yi amfani da ita wajen cutarwa wani idan ka yi haka, to kai da Allah kuma ni ma kaina ba zan yafe maka ba.

Kamar yadda na fada maku a farko akwai "Application" da ya zo daga kamfanin "Google" mai suna "Google Family Link" kamfanin sun yi shi ne don ya taimaka wajen samun damar hada mahaifi da yaransa, ta hanyar wannan "Application" za ka iya hade dukkan wasu da kake so ka bibiya.

"Application" din na kyauta ne. sannan yana bayyana komai yana da dadin aiki kuma yana da dadin sha'ani na tabbata duk wanda ya yi amfani da shi zai burge shi sosai matuka.


Amma "Application" din kala biyu ne akwai wanda za ka saka a wayarka a matsayin mahaifi sannan akwai wanda zaka saka a wayar da kake son bibiya a matsayin wayar danka.

Naka a matsayin mahaifi shi ne; "Google Family Link For Parent" na yaronka kuma "Google Family Link for Children" idan ka turawa yaron naka ko kuma wanda ka ke so ka bibiya zaka iya boye "Application" din ta yadda ba zai san akwai ta a cikin wayarshi ba.

Amfanin wadannan "Application" na asali, an yi su ne kawai don su taimaka wajen mahaifi ko mahaifiya su kula da tarbiyar 'ya'yansu namiji ko mace misali wadannan "Application" za su baka dama ka iya bibiyar duk inda danka ya ke ko kuma ina ya je ko daga ina yake ko ina zai je.

Amfanin dukkannin "Application" din guda biyu a takaice shi ne;

Misali na farko daga amfanin su shi ne sanin su zai sa ka iya kare kanka daga wanda yake son cutar ka.

Na biyu zaka iya amfani dasu wajen gane duk wanda kake so ka bibiya uwa ko da, miji ko mata da sauransu har ma'aikata a wajen aiki dukka ana iya bibiyar su.

Na uku zaka iya amfani da wadannan" Application" din don ka iya bibiyar wayarka saboda ko da Allah ya sa ta fadi ko kuma wani ya yi kokarin sace


ta kai tsaye za ka iya ganinta cikin sauki sannan koda

barawon ya yi kokarin "format" din wayar bai isa ya yi ba.


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.