Free chapter · Read without an account
RAYUWAR SAMARI DA 'YANMATA BAYAN KAMMALA KARATUN NCE, DIPLOMA, HND DA DIGIRI
by AREWA MEDIA WRITERS · RAYUWAR SAMARI DA YANMATA A SOCIAL MEDIA
Abu ne sananne a kasarmu ta Nijeriya, samari da 'yanmata masu shaidar karatun NCE, DIPLOMA HND, DIGIRI DIGIRI har da Masters suna rayuwa cikin fatara da talauci bayan kammala karatunsu.
Wannan shahararren abu ne a kasarmu, amma wasu suna ganin hakan yana da alaka da karancin wadatattun ma'aikatu da ake da su a Nijeriya da kuma rashin daidaito a kasuwar daukar aiki.
Sai dai wasu kuma suna ganin kamar rashin samar da kyakkyawan yanayi ne da matasa za su iya tsayawa da kafarsu ke janyo hakan.
Wasu kuma suna gani kamar talaucin matasa yana da nasaba da buri da suke dashi a rayuwarsu, duba da yadda da yawancinsu ba sa yin karamar sana’a saboda suna tinkaho su yanzu sun zama "Graduates" sun fi karfin karamar sana'a.
Gaskiya kowanne daga ciki zai iya zama dalili, amma abun da mutane masu rinjaye suka yadda da shi yana da alaka da rashin daidaito "Equality" a kasuwar daukar aiki.
Misali, a kasar Nijeriya ne dan talaka zai gama jami’a da sakamako na daya "first class" amma ya shekara Bakwai babu aiki saboda ba shi da kowa sai Allah.
A bangaren wasu masu mukami a cikin gwamnati kuwa za ka samu matashi ya gama jami’a da mummunan sakamako amma tun kafin ya gama an ajiye mashi gurbin aiki.
Wannan shahararren abu ne a Nijeriya, don ana samun wasu tun daga jami’a suke sanin irin ayyukan da za a ba su idan sun kammala karatu.
A lokacin da dan talaka mai sakamako mai kyau yake yawo duk takalmansa sun mutu saboda neman aiki.
Da yawa daga cikin irin wadannan matasan suna cikin kuncin rayuwa da fatara saboda sun zama ci-ma- zaune bayan kammala karatu kuma ba lallai ba ne su iya aikin karfi saboda buri irin na "graduates" din Nijeriya.
An dade ana neman hanyoyin da za a bi don warware matsalar rashin aiki a Nijeriya, babban abun da yake bayar da mamaki shi ne, za ka ji ana cewa babu aikin yi, mutane sun yi yawa, kaza-da-kaza, amma gashi kuma samun aikin babu wahala a wajen wasu.
Misali, duk sanda ‘yar wani babban mutum ta jarabtu da son dan talaka sai a kirashi cikin gaggawa a bashi aiki mai kyau don ya rike masa ita da kyau.
Wannan dalilin ne ya sa ‘ya’yan talakawa yin auren jari saboda neman mafita, ga su nan da yawa a Kano, Kaduna da Abuja, kullum fatansu shi ne, Allah Ya hada su da ‘yar wani "Pharm Sec, DG, Senator, Minister" ko wani babban dan kasuwa.
To mene ne mafita ga Nijeriya da wadannan samari?
Na farko, ya kamata gwamnati ta gane cewa, duk gwamnatin da ta kasa samar da daidaito a cikin bayar da dama ga mai rabo "equality of job opportunities", gaskiya tana da matsala.
Na biyu, sai dukiyar Nijeriya ta yi tasiri a rayuwar talaka, ta hanyar samar masa da hanyoyin da zai rayu ba tare da gwamnati ba, a samar da hanyoyi na gaske.
Na uku, dole sai an samu hanyoyin wayarwa da matasan Nijeriya kai don su gane cewa, shi fa aikin gwamnati na mai rabo ne "privilege", su yi amfani da iliminsu wajen samarwa da kansu aikin yi.
Abu na hudu, dole matasa su cigaba da neman ilimi, kada jikinsu ya mutu don suna ganin ‘yan’uwansu sun yi karatu ba su da aikin yi.
Tabbas, rashin ilimi ya fi rashin aiki zama kalubale, tun da sai da ilimi dan adam ya ke rayuwa cikin ‘yanci da mutunci, kuma duk abun da zai zagi mai ilimi, lallai kai jahili idan ya zo kanka kasheka zai yi.
Abu na Biyar, dole matasanmu su cire girman kai su a jiye batun sun zama "Graduates" su rungumi kananun sana'o'i na hannu da na zamani domin samun rayuwa mai inganci.
'Yan Mata kuma, sai ku rungumi sana'o'in da kuka ga zaku iya, da zaran mijin aure ya zo ku yi auranku, koda kun yi aure kada ku daina sana'o'inku domin samun kudin shiga wanda ba sai kin jira kowanne lokaci mijinki ya baki ba, idan yana baki wata rana dole zai gajiya.
Duk lokacin da kuma aiki ya samu sai ki rike hannu bibiyu ko da kina gidan aurenki.