Free chapter 路 Read without an account
PAGE 3
by Malik al-Ashtar 路 AYDANATU
AYDANATU 馃馃徑
By 鉁掞笍 Malik al-Ashtar
_Sabon labari daban da sauran_ 馃憣馃徑
On Wattpad : ***
Domin samun wannan labari na saurare sai ku ziyarci channel din mu 馃憠 ***
PAGE 3
{Yau muna talata biyu ga watan sha daya, rana mai cike da zafi. Yau tsawon makonni kenan ban bude littafi na ba nayi rubutu, kuma ba wai bani bukatar yin hakan ba ne, a'a lokaci ne da ban samu ba.
Kwanakin nan na baya abubuwa da dama sun faru, kamar irin su aikace-aikacen gida da nake yi kullum, kin ko in kula da baba na ke min sai kuma bata dare da nake yi in shige lungun gidan mu nayi ta kuka. Babu wani lokaci da nake da free da zan zauna har na iya cigaba da rubuta halin rayuwar da nake ciki a wannan littafin.
A yau tun da hantsin safiya, na riga kowa tashi daga bacci. Duk da tsoron da nake ji, domin duhu bai gama yayewa ba, na fito daga gida, ya dace nayi hakan, ya dace na ganta ko nace inyi mata magana. Domin nasan ba zan kara ganin ta ba, ina fata ko jin abinda zan ce ta iya.
"Mama!" Na fada idanuna cike da hawaye, lokacin da na zo kan kabarin ta. "Mama me yasa kika tafi? Me yasa kika tafi kika barni ni kadai? Mama, ko kin san wuyar da 'yar ki take sha bayan tafiyar ki? Shin daman kin san da me zai faru da ni, tun kafin ki tafi? Ko saboda hakan ne kika roki Allah, bayan kin idar da sallar rannan?" : 芦Ya Allah, kai ne madaukakin sarki, ina jin wani abu zai faru, wani abu da zai ruguza wannan ahali, ya Allah kada ka taba bari 'yata ta dulmiye cikin wannan kazamtar ta duniya, ka bata juriya da yalwar imani. Ka biya mata mafi tsada daga cikin bukatun ta. Ya Allah...禄
Wata kila saboda irin wannan ranar ne, yasa ta roki Allah ya saka min juriya. Taji a jikin ta cewa rayuwa ta zata canza daga dadi zuwa wahala, cewa wani mummunan abu zai faru, to amma ko tasan dama zata bar duniyar nan?
"Yau sati uku kenan da komawa school, idan da kin san kuncin da nake fuskanta yayin da na fito ina shara da wanke-wanke alhali sauran yara aji na sun shirya sun tafi makaranta, da ba zaki barni ba mama, ni da aka zaba daga cikin mafi hazaka saboda scholarship zuwa jami'ar kasar waje bayan cin exam dina da nayi tare da maki mai kyau. Kin tuna muna yawan yin maganar, har kika ce ke zaki raka ni rana ta farko?
Mama abubuwa da dama basu faru ba yanda muka so kuma muka yi mafarki. Bayan hana ni cin moriyar scholarship da baba yayi har da ma karatun ya hana ni! Kin tafi kin barni gashi yanzu na dawo tamkar yar boyi-boyi a gidan mahaifina. Wurin da ya kamata ya zame min wurin da zan fi samun farin ciki, shi ne wuri mafi kunci a gare ni. Kuncin da ya zamar min dole ba tare da nayi kwakwaran motsi ba dan kar baba ya kore ni daga gidan...."
Na dade sosai a kabarin mahaifiya ta ina kuka, wanda da kyar na iya dainawa. Ban kwana nayi mata, na juya zuwa gida.
Nasan da Hassatu tana cen tana jira na, Allah kadai yasan me take shirya min, amma ina da tabbacin tana tsaye bakin kofa tana jira na.
Bude kofa kawai nayi, ta hau kaina da zagi da tambayoyi marasa kan gado.
"Ahan yanzu yarinya tayi karfin da zata fita tun shiddan safe!"
"Yanzu kuma sa ido kika fara min?"
"Eeh lallai har kin yi kwarin da zaki min irin wannan tambayar?" Dariya tayi na wasu sakonni kafin ta taume fuska ta cigaba "Ki san wani abu karamar marar kunya, a gidan nan ni ce ke yin tambayoyi!" Ta fada da daga murya.
"Ban aikata komai ba, so dan Allah kiyi magana a hankali kar baba yaji!"
"Eh ai abinda nake so kenan, ya jimu din!" Ta sake fada da daga murya da wani murmushin mugunta a labbanta.
"Meke faruwa ne anan!?" Cewar baba da ya karaso wajen mu. "Me ya faru ne, kuma me kuke yi a wannan lokacin?"
"'yarka zaka tambaya!"
"Baba, naje..."
Saurin katse ni Hassatu tayi "Wani sabon tsirku 'yarka ta fara na fita daga gida cikin duhun dare ba tare da kowa ya sani ba, kuma Allah kadai yasan me take yi a wajen!"
"Aydanatu da gaske ne abinda take fada?"
"Baba zan iya maka bayanin..."
Wani azababben mari ne ya sauka akan fuskata.
"'Yar iska! Yanzu yar titi kike son komawa? Karuwa?"
"Aha abinda nace kenan, domin idan ba haka ba me take yi a waje! Wai ma tambayar me kake yi mata ne? Bukari nasha fada maka, ba wata tarbiya ke ga 'yarka ba!"
Sunkuyar da kai baba yayi jin abinda Hassatu tace, sannan ya kalle ni cikin bacin rai da tsana.
"Baba ta yaya zaka iya wannan tunanin a kaina? Ni fa yarka ce kuma kasan irin tarbiyar da ka bani, kasan abinda zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba."
"Yimin shuru, kar na sake jin muryar ki!"
"Baba dan Allah ka saurare ni."
"Maza ki wuce dakin ki!"
Dariya maganar sa ta bani, cikin takaici nace "Daki na? Ko dai kana nufin cikin wancen lungun na falo? Ai bani da daki baba, ka amshe min komai. Eh komai, kuma kafi kaunar wannan makirar da 'yayan ta a kan ni tilon 'yarka."
Wani marin ne ya sake sauka akan fuskata, sai dai wannan karon daga hannun Hassatu ya fito.
"Baba, haka zaka cigaba da barin ta tana muzguna min? Zaka barta ta cigaba da cutar da ni lokacin da take so?" Rai a bace nayi wannan maganar. "Me yasa ka daina cewa komai? Har yaushe zan cigaba da jure zaluncin da take min!!?"
"Har zuwa karshen rayuwar ki a gidan nan!" Hassatu ta bani amsa tana mai kada kugu.
"Bace min da gani!" Cewar baba na rai a bace tare da kauda idanun sa gefe.
Share hawaye na nayi kafin nace masa: "Wata kil zunubi ne abinda zan fada, amma yau babu wanda na tsana sama da kai baba." Na fada cikin kunar zuciyar tare da juya masa baya.
"Ta yaya zaka bari tana fada maka irin wannan maganar? Ita ta haife ka ko kai ne ka haife ta? Ehh wai kuma kai ne namiji a gidan nan, ai ban san sullutu na aura ba!"
"Kada kice haka please my dear.. Ke kin sani sarai.."
"Kai ni sake ni! Bana son kara jin wani abu daga gareka idan har ba zaka dau wani mataki ba akan 'yarka."
"Fada min abinda kike so, ni kuma zan yi shi a yanzu amma dan Allah kar kiyi fushi."
"Hum toh shikenan! Amma zaka barni da 'yarka, zaka bari ni na tarbiyantar da ita da kaina kuma bana bukatar jin wata kalma daga bakin ka akan duk wani abu da zan yi. Kawai ka yarda da ni kuma kasa a ranka saboda goben ta ne zan yi hakan."
"My love kin san a duniyar nan yanzu ke kadai ce wadda na dauki yarda ta na baiwa, dan haka zaki iya yin komai na baki dama."
Oh Allah na meke faruwa ne da mahaifi na? Ban taba ganin sa yana kaskantar da kan shi har haka ba, kuma akan mace. Shin duk ina ya kai izzar nan tashi, ko dai ba mahaifina bane da na sani kuma naso a baya? Yau gashi ya sallama ni ga wannan muguwar! Me kuma zata aikata min nan gaba?!!
...}
"Hajiya? Hajiya?" Wata matashiyar budurwa ta fada tana mai katse Maryam da ta zurfafa cikin karanta labarin Aydanatu.
"Na'am?" Cewar Maryam tare da jan dogon numfashi, tana mai dago kanta.
"Ah Asiya! Bismillah zauna."
"Sorry na shigowa da nayi ba tare da izini ba, nayi ta konkwasa kofa amma ba amsa. Fatan dai lafiya?"
"Ah lafiya lau, kar ki damu kawai nayi zurfi cikin karatu ne."
"Dama nazo ne na fada miki yallabai na son ganin ki a ofishin sa."
"Yanzu yanzu?"
"Eh Hajiya!"
"Ok nagode Asiya, zaki iya tafiya."
Cike da damuwa Maryam ta rufe littafin. Sosai labarin Aydanatu ya taba ta, ta yanda idan tana karatun bata son ta daina. Tana son ta karance shi duka lokaci guda kuma tasan labarin baki daya. Tambayar kanta take, ko har yanzu Aydanatu na kasar Mali? Wata kila har yanzu cen take, kuma wane hali take a yanzu? Shekaru nawa kenan suka wuce tun lokacin da ta rubuta wannan littafin? Domin a cikin littafin kwanaki da watanni kawai take rubutawa banda shekaru.
Tattare takardun ta tayi da littafin ta saka a jaka kafin ta wuce ofishin mahaifin nata. Tarar dashi tayi yana waya.
Bayan ya gama wayar, yayi mata nuni da kujera ta zauna. Gaishe shi tayi, ya amsa tare da tambayar ta yanda take da kuma su Nuriyya.
"Kace kana son gani na?"
"Eh na kira ki ne domin ina son muyi lunch a tare, dan haka mu je dining table."
"Thanks dad, kamar ka sani ina jin yunwa kuwa sosai."
"Toh yaya hutu, fatan kin yishi lafiya?"
"Humm lafiya lau dad."
"Nayi missing dinki ba kadan ba fa, a office."
"To ai kai ne dad kasan yanda nake son aiki sosai, amma ka bani har 2 days na hutu... Wai tsaya.. Kamar ya? A office kawai kenan kayi kewa ta?"
Dariya dad yayi, ita kuwa ta zumburo baki alamar shagwaba. Yi tayi kamar zata yi kuka sai da dad yayi ta lallashin ta sannan ta hakura.
Abincin suka fara ci, cen dad ya dago ya kalle ta tare da cewa "Naga kamar akwai abinda ke damun ki, fada min meke faruwa?"
Maryam bata san lokacin da tace "Wallahi kuwa dad, tunanin Aydanatu nake kuma..."
"Aydanatu? Wacece ita?" Cewar Mommy da ta shigo offishin daidai lokacin da Maryam ke fadar sunan Aydanatu.
Murmushi Maryam tayi tare da yiwa Mommy barka da zuwa.
Zaunawa Mommy tayi, tana cewa "Ku ce nazo kan daidai, to nima a zuba min naci."
Zuba mata Maryam tayi, Mommy tace "Da na shigo naji kuna maganar wata Aydanatu."
"Eh 'yata muna sauraren ki, wacece ita?" Cewar Dad da zumudin sanin wacece Aydanatu.
Karya Maryam tayi musu "Ehm..eh wata kawata ce?"
"Toh me ya same ta?" Cewar dad.
"Ba wata matsala bace babba, ni kaina zan iya maganin abun insha Allahu."
"Toh Allah ya baki iko my Princess." Cewar Dad.
Maryam ta amsa da
"Ameen Dad!"
"Fada min, nasan wannan Aydanatun kuwa?" Cewar Mommy.
"Bana tunanin kin santa mom."
"Ina jin kamar na taba jin wannan sunan a kwanakin nan, amma na manta ko ina."
"Zai iya zama ko'ina my dear." Cewar Dad. "Zai iya yiyuwa daya daga cikin mutanen da kike haduwa da su ne keda wannan sunan. Tunda kina haduwa da jama'a sosai a rana, ko kuma kin hadu da ita ne a gidan marayu ko a kamfani. Allah dai ya sani."
"Humm kuma fa haka ne."
"Mu ci kar abincin ya huce." Cewar Maryam da son kawar da maganar Aydanatu.
Bata san me ya kaita yiwa iyayen ta zancen Aydanatu ba. Bata santa ba kuma bata taba ganin ta ba. Kawai diaryn ta gare ta kuma bata sani ba ko ta kyauta da take karanta shi. A zuciyar ta tace
"Wata kila zata ji haushi na idan tasan na karanta labarin ta, ina son na ganta. To amma a ina? Idan na tsinci littafin ta a nan Nijar, to kenan tana nan cikin Niamey? Shin hakan zai yiwu kuwa? Idan kuma har ta riga da ta koma Mali, ta ina zan fara neman ta?
Me ya faru da har ta baro Mali ta dawo nan Nijar?
Ina tunanin wannan amsoshin idan ina son sanin su dole na cigaba da karanta littafin."
Bayan sun gama yin lunch, Maryam ta yiwa iyayen ta sallama tare da komawa ofishin ta, ta rufe domin ta cigaba da karanta littafin.
{...Zuwa karfe goma na safe, bayan na gama aike aiken gidan, na nemi kujera na kwanta domin hutawa. Katuwar muryar Hashim ce tasa nayi saurin tashi.
"Me aka yi kake min irin wannan kiran?" Na tambaye shi lokacin da ya karaso inda nake.
"Me yasa baki shiga kika gyara min daki ba? Ki tashi ki gyara shi yanzu!" Ya umarce ni yana mai zaunawa gaban TV.
Wata dariyar takaici nayi kafin nace "Idan kana mafarkin zan gyara maka daki, to ka farka! Ba'a rubuta Cindrella bisa goshi na ba kuma ka sani ni ba baiwar ka bace."
A fusace ya yo kaina tare da gama ni da bango, ya shake min kwala sosai.
Cikin sigar gargadi ya rada min "Ki kiyaye shiga gona ta, idan kuma ba haka zan koya miki hankali ta inda baki yi zato ba."
"Bana tsoron ka Hashim!" Na fada murya a shake. "Duk abinda nake ji a yanzu da kuma duk lokacin da na ganka bai wuce tsana da kyama ba, ba wai tsoro ba."
Dariya yayi, tare da kara matso fuskar sa daidai fuska ta ta yanda ina iya jin numfashin sa, sannan yace : "Me ya kamata nayi maki ne han? Kece yarinya ta farko da take yimin magana haka?" "My beauty," ya fada yana mai shafa min fuska. "Baki san ko ni waye, da abinda nake iya aikatawa ba, dan haka ki daina shige min kuma ki kiyaye fushi na."
Kokarin fizgewa daga rikon da yayi min nake, shi kuwa ya kara matse ni.
"Kin gyara min dakin ko kuwa?"
"Ko a mafarki, domin ni ba baiwar ka bace! Na fada maka ka sake ni, ko nayi maka ihu."
Dariya yayi "Shikenan na sake ki! Amma ki san wani abu, zaki shigo hannu ko ba dade ko ba jima." Ya fada yana wani dantse lebe kafin ya tafi.
"Me yake nufi da hakan?" Na fada cikin rashin sanin inda maganar sa ta dosa.
"AYDANATU!!" Matar baba na ta kwallo min kira.
Me kuma take so yanzu?
"Na'am gani nan zuwa!"
Ina zuwa inda take ta miko min da manyan thermos biyu shake da ice cream.
"Meye wannan?"
Tsawa ta daka min
"Sakarya idon ki basu gane miki bane ko me?"
"A'a ina nufin me zan yi dasu kuma saboda me kika bani su?"
"Na lura tsabar dakikancin baki iya komai ba banda tambayoyin tsiya. To ki jini da kyau, daga yau idan kika gama aikin ki da safe, zaki dauki wannan ice cream din ki je dashi jami'a ki saido. Kuma ki tabbatar kin siyar duka ba tare da kin batar da ko sule daya ba. Idan kuwa ba haka ba jikin ki ne zai fada miki."
"Me yasa sai a jami'a, ai zan iya siyar dashi wani wurin daban."
"Ban ce ki min musu ba, cen nake son ki siyar!"
"Me yasa zaki min haka?" Na fada hawaye na barazanar zubo min.
"Toh wai ba ke bace mai burin zuwa jami'a ba? Wannan fa dama ce na baki."
"Kin sani sarai ina son zuwa jami'a amma ba a matsayin yar talla ba. Cen fa, akwai duk tsofin abokai na. Kin yi hakan ne dan ki muzguna min? Kina son su ganni ina tallar ice cream!"
"In muzguna miki? To wai da kina daukar kanki a wa, ni ai baki wuce matsayin baiwa ba gare ni. Eh baiwa ta, kuma sai yanda naso yi dake. Wuce kafin raina ya baci."
Haka na dauki manyan thermos din dakyar na nufi kofar fita ina kuka.
Ba bata lokaci na isa makarantar, da zuwa na na samu lungu na ajiye thermos din domin zagaya cikin makarantar.
Nasha mafarkin son ganin na dora kafata a jami'a. Kyakyawan wuri ne, ga gwanin sha'awa ganin dalibai kowa na yin harkokin gaban sa, wasu na karatu, wasu na motsa jiki, wasu kuma na zaune suna karanta littafai.
Ba tare da na ankara ba, kafafuwa na suka kawo ni cikin library, tuni shaukin son karatu ya kama ni. Akwai littafai kala-kala. Hannu na saka na dauki daya daga ciki, irin yanayin nan na karatu sosai nayi kewar sa, hakan ya tuna min abubuwa da dama ciki har da Faruq. Faruq? Na sake maimaita sunan cikin zuciya ta. Nasan dole yana nan, idan kuma ya ganni da wannan kayan kuma ina siyar da ice cream, me zan ce masa? Na yiwa kaina wannan tambayar.
An dade kenan rabon da na ganshi har muyi magana. Ban samu lokacin ganin shi ba har na bashi labarin halin da nake ciki.
"Nasan zai yi ta min tambayoyi idan ya ganni anan kuma cikin irin wannan shigar." Na fada ina kokarin ajiye littafin dake hannu na.
"A very interesting book!" Naji wata babbar murya ta fada a baya na.
Idanuna na daga suka sauka kan wani kyakyawan mutum da ba zai wuce talatin zuwa da biyar ba.
"Eh, nima yanzu na fara karanta shi." Na bashi amsa ina mai maida kallo na akan littafin.
"Ban cika ganin yan mata masu shekarun ki anan ba. Wane sector kike?"
"A'a ni..ni ina common core ne, ban kai ga zaben abinda zan yi ba." Nayi masa karya domin rashin sanin me zan ce da tsoron kar yasa ayi waje dani.
Murmushi yayi yace "Ke sabuwa ce, kina ajin farko haka ne?"
"Eh, eh hakane."
"Oh sorry ban gabatar miki da kaina ba, sunana Kabeer Usman, malamin math."
"Kai.. Kai malami ne?" Na fada a rikice.
"Eh, ke fa meye sunan ki?"
"Sunana.. Aydanatu!"
"Nice to meet you Aydanatu! Ni zan wuce fatan zamu hadu a class."
Sai da yayi min kayataccen murmushin sa kafin ya tafi.
"Wayyo Allah na, me na aikata haka, me yasa nayi masa karya!?"
A takure na fito daga library da gudu sai dai da rashin sa'a ta, naci karo da Safiyya da kawayen ta.
"Aydanatu? Me kike yi anan, kuma waya baki izinin zuwa nan?"
"Kiyi harkar gaban ki Safiyya! Kin ga ni ba wajen ki nazo ba."
Wucewa naje yi amma kawayen ta suka sha gaba na.
"Toh me kuke so da ni kenan?"
"Ba zaki tafi ba har sai kin fada min abinda kika zo yi nan."
"Allah ko? Toh ai kuwa zamu kwana anan!"
"Sofi 芦Sunan da kawayen ta ke mata禄, ba fa zai yiwu mu dade a nan ba." Cewar daya daga cikin kawayen ta.
"Eh, kin san muna da lecture nan da awa daya." Cewar dayar kawar.
"Sakarya kiyi magana, mu muna da abin yi!!"
"Daina yimin tsawa, kuma zai fi ki saurari kawayen ki!"
"Ayda?"
"Faruq!"
Murmushi nayi kafin nace "Wata biyu kenan ina nemanka a school dinnan amma ban ganka ba."
Dariya Safiyya tayi tace "Makaryaciya kamar karatun take."
Da mamaki Faruq ya kalle ta yace "Kamar ya?"
"Kaji da kyau guy, baban ta ne ya hana ta yin jami'a!"
"Aydanatu da gaske ne abinda take fada?"
"Ah saboda ni na fada maka, shi ne...."
"Kin ga ba dake nake magana ba." Faruq ya katse ta. "Ayda please amsa min meke faruwa?"
"Eh da gaske ne, nazo nan ne saboda..."
"Idan kina so zamu iya zuwa wani wajen muyi maganar, ba dole sai a gaban su ba."
"A'a, wata kila su shafa min lafiya, idan na fada a gaban su. Ina siyarwa da Hassatu ice cream ne, wannan shine dalilin zuwa na nan."
Dariya suka kwashe da ita yan matan, a yayin da ni kuwa kamar an zuba min garwashi a zuciya.
Safiyya na dariya tace : "Siyar da ice cream, gaskiya mama ta daban ce, shi yasa nake kara sonta!"
Tabawa tayi da kawayen nata suna ta shewa.
"Fahimtar dani dan Allah Aydanatu, me yasa baban ki bai son kiyi karatu, kuma meye ma'anar siyarwa da Hassatu ice cream da kike?"
"Faruq kayi hakuri, yanzu bana yanayin da zamu yi magana. Zan je nayi aikin da ya kawo ni."
"Ayda ya kamata ki tsaya muyi magana!"
"Please Faruq, ba yanzu ba." Na fada tare da juya baya.
"Ayda..!!!"
"Oh ka rabu da ita mana! Ni na kasa gane me ka gani tattare da yarinyar cen, alhali kana da ni gaban ka, kuma kasan ina sonka sosai."
"Bani da lokacin wannan shirmen naki Safiyya."
Nisan da nayi ne yasa na daina jin me suke cewa.
Ban sha wahala wajen siyar da ice cream din ba. Cincirindo daliban suka yi wajen siya da yake ana rana ga kuma zafi hakan ma ya taimaka min.
Haka kuma nayi amfani da tasowar su wajen siyar da wanda ya rage domin na samu naje gida.
"Bani guda daya!" Naji kamar daga sama an fada.
Dagowa nayi dan ganin mai magana.
"Hashim!" Na fada da mamakin ganin shi ne yamin magana. "Idan kana so, to ka sa kudi ka siya kamar kowa."
Dariya yayi, yace "Amma wasa kike ko? Ina ce kayan mama ta ne, so ki bani sannan ki bawa abokai na su ma."
"Ai bansan kai da yan iskan abokan ka ba, ku ma anan makarantar kuke."
Daya daga cikin su, ya yo kaina a zafafe, sai dai Faruq yazo a daidai ya shiga tsakanin mu.
"Gafara karamin dan iska!" Abokin Hashim ya cewa Faruq a tsawace.
"Idan ba haka me zaka yi?"
Shakar kwalar juna suka yi, kafin Hashim yace "Calm down guy! Rabu dashi mu je."
"A'a ka barni na koya masa hankali shi da wannan fitsararriyar yarinyar."
"Ko kayi yanda abokin ka yace, ko kuma ni na koya maka hankali. Domin kafi kowa sanin ko ni waye!" Cewar Faruq.
"Ku je mu je guys!" Hashim ya sake dakawa abokan nasa tsawa. "Ke kuma zamu hade gida!"
"Idan ba yau ba akwai gobe." Cewar daya daga cikin abokan cikin sigar barazana.
"Hashim!" Faruq ya kwalla kiran sa ta yanda zai ji. "Ku kiyaye shiga gona ta, sannan ka fadawa abokan ka akwai banbanci babba tsakanin Aydanatu da sauran yan matan da kuke muzgunawa, domin tana da ni kuma a kullum zan kasance mai kare ta."
Kallon sa nayi da idanuna da suka ciko da kwalla.
"Nagode da zuwan ka."
"Baki san irin kewar ki da nayi ba Ayda, a duk lokacin da naje gidan ku ganin ki, sai Safiyya da mahaifiyar ta nake gani, kuma ce min suke kin ce baki son gani na."
"A'a ba gaskiya bane, ban taba sanin kana zuwa gidan mu ba. Ka yarda dani."
"Na yarda, amma na dauka har yanzu kina jin haushi na game da abinda ya faru da mahaifiyar ki."
"A'a bani da ikon da zan tsane ka domin ba laifin ka bane. Haka Allah ya kaddaro."
"Me yasa ba zaki fada min matsalar dake faruwa a gidan ku ba? Wa ya sani ko zan iya yi miki wani taimakon."
"Ta yaya kenan?"
"Ban sani ba, wata kila ta hanyar magana da baban ki. Mutumin kirki ne nasan zai saurare ni."
"Kada kasa rai akan hakan domin baba na ya sauya sosai! Faruq, baba na ba wanda ka sani ba ne a baya, ya canja tun ranar da ya auri Hassatu."
"I'm sorry bansan da duk hakan ba. Ki saurare ni mu gwada zuwa ofishin mahaifin ki muyi masa magana."
"A'a bana tunanin wannan dabara ce mai kyau."
"Ai babu abinda zamu rasa idan muka gwada ko kuwa?"
Murmushi nayi, nace "Eh, mu tafi."
Mun isa ofishin baba na. Yayi mamakin gani na kuma ya rungume ni sosai.
"Me kike yi nan my lil princess, ke kadai kika zo? An jima sosai rabon da ki zo nan."
"A tare muka zo." Cewar Faruq dake kokarin shigowa.
"Oh dana tare kuke?"
"Eh."
"Toh fada min my princess, meke tafe dake kuma na meye wannan thermos din?"
"Um..na..na"
Na rasa abinda zan cewa ko zan yi, domin lokaci guda naga baba na kuma ba a matsayin mugu ba. Gashi ya rungume ni kuma yayi min magana kamar yanda yake min a baya...
Faruq ne ya katse min tunani ta hanyar cewa "Na Hassatu ne, kawu, tana tilasta ta siyar da ice cream a jami'a, ga yarka tana da kokari sosai kuma ba karamin kuskure bane hana ta karatu."
"Kamar ya? Ban gane ba, da gaske baki zuwa school?" Baba ya tambaye ni da mamaki.
"Eh baba, ko ka manta ne? Kai da kanka kace ba zan sake zuwa makaranta ba."
"Ta yaya? A'a ba zan taba yin hakan ba ga 'yata."
"Ta samu scholarship kuma tunda bata tafi karatu waje ba, ya kamata ko nan ne tayi karatun kawu."
"Sosai ma kuwa Dana, sosai ma! I'm so sorry my dear na hana ki karatu da nayi, amma insha Allahu nayi miki alkawarin zuwa gobe na rubuta ki."
"Da gaske baba?" Na fada cike da murna.
Murmushi yayi "Eh, amma fada min meke faruwa na ganki a irin wannan shigar..."
"Hassatu ta kwace min duka kaya na."
"What? Ita a wa zata kwace miki kayan da ni na baki! Mu je gidan ta fada min dalili. Kai kuma Faruq nagode sosai."
Tunani na ya kwance lokacin da muke cikin mota, baba na yayi kamar bai san meke faruwa ba a gida alhali komai akan idon sa ake yi. Amma ta yaya hakan zai yiwu?
Muna Zuwa gida ya ajiye kayan sa tare da kwalla kiran Hassatu, sai dai yana ganin ta ya canza baki daya, ya dawo wani daban.
"Ka kira ni ne honey?"
"Eh my love na dawo." Baba ya fada yana washe mata hakora.
Wani kallo Hassatu ta watso min mai sa in sha jinin jiki na.
Me ya faru da kai baba, ya aka yi ka sauya lokaci guda? Tambayoyi nake ta jerowa kaina a zuciya ta. Sai dai wadda tafi tsaya min a rai ita ce :
Ko dai wannan matar asiri ta yiwa baba na ne?...}
*****