Free chapter · Read without an account

PAGE 5

by Malik al-Ashtar · AYDANATU

AYDANATU 🧕🏽 



By ✒️ Malik al-Ashtar


_Love 💓 and very sad 😰 story_ 📖



On Wattpad : ***



*PAGE 5*


⚖

*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*

_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._

***


*[📝I.W.A📝]*


Yau Maryam bayan ta aje yara a school, ta shirya zata je Kutiala domin nemo Aydanatu. Tana jin tayi karantawar da zata yiwa labarin domin ta fahimci Aydanatu na bukatar taimako. Tana so kuma zata yi komai ganin ta kai mata dauki, idan ma ta kama zata dauko ta ta dawo da ita wajen ta da zama.


Tana jin kaunar yarinyar har cikin zuciyar tana kuma daukar ta ne tamkar yar uwar ta duk da bata taba ganin ta ba kuma bata santa ba. Wata kila saboda tasha wahala ne sosai, shi yasa Maryam ke son taimakon ta.


Ba zata iya tafiya ba, ba tare da ta sanar da Mahmud ba. Kamfanin da yake aiki ta nufa, ba tare da tasan me zata fada masa ba, bata taba yi masa zancen Aydanatu ba, ko zancen littafin ta da ta tsinta. Tasan Mahmud zai ga wautar ta, wata kila ma ya hana ta zuwa. Duk da haka taje wajen aikin nasa domin sanar dashi tafiyar ta, sai dai da zuwan ta, aka sanar da ita yana meeting kuma babu alamun zai fito yanzu. Ba zata iya jiran sa ba, domin a ganin ta duk wata dakika zata wuce daidai take da rasa Aydanatu. Kiran wayar sa tayi amma a kashe, bayan jira da ta kara yi na rabin awa, ta yanke shawarar yi masa text tare da yi masa bayanin zata je Mali, kuma tafiyar gaggawa ce ta taso ba tare da ta fada masa dalili ba ko yi masa kwakwaran bayani. Tasan zai yi mamakin tafiyar, da jin haushin ta na tafiya da tayi ba tare da sun yi magana ba, kuma da boye masa labarin tun farko.

Komawa tayi gida ta fara hada kayan ta na tafiya, kofa taji ana konkwasawa, taji tsoron ko Mahmud ne. Sai dai tana budewa ta ga Aminatu ce yar uwar ta. Rungume ta tayi da murnar ganin juna.


"Shikenan sai kika manta da ni?" Cewar Aminatu tana mai shigowa daga ciki. "Kin daina zuwa gida na, ga wahalar daukar kirana da kike yi kuma ma idan na kira ki sai in ga kamar hankalin ki yana wani wajen! Meke faruwa ne sis?"


Rufe kofa Maryam tayi bayan ta shigo.

"I'm so sorry yar uwa! Eh da gaske hankali na yana wani wajen, amma kar ki damu ba wani abu bane babba, kuma kin san ba yanda za'a yi na manta da yar kanwata. Kina raina kuma nayi missing din ki nima, koda ban cika nunawa ba."


"Ah please Maryam, kar kema ki fara amfani da kalaman Ibrahim!" Cewar Aminatu tana kokarin hawan stairs. "Haka yake fada domin kara yin nisa da mu, ba tare da muna jin duriyar sa ba, ko sanin dalilin sa ba! Please ke ma kar ki fara hakan, kinsan zaki iya fada min komai, ni aminiyar ki ce kuma yar uwar ki..."


Zata iya boyewa kowa amma banda Amina. Dakin ta ta kaita domin ta bata labarin komai, da shigar su abinda Amina ta fara gani shine akwatin kayan Maryam.


"Shi kuma wannan akwatin? Ko tafiya zaki yi?"


"Ummm ni ban ma san ta ina zan fara miki ba." Maryam ta fada tana sosa kai.


"Toh ai ki fara kawai tun daga farko."


Labarin yanda ta tsinci littafin ta bata, kuma ta bata irin labari mai ban tausayi dake ciki, sannan kudirin da ta daukarwa kanta na nemo Aydanatu.


"What? Kina da tabbacin kin yanke shawara mai kyau na zuwa neman yarinyar nan?" Cewar Amina da mamaki. "Ina nufin... Baki san yarinyar nan ba, ko inda zaki ganin ta a Kutiala! Sis, baki sani ba ko har yanzu tana cen Mali ko kuwa, tunda littafin anan Niamey kike tsince shi, kuma ba wata hujja gare ki ba na cewa wannan ba kagaggen labari ba ne.


"Ki daina fadar haka please Amina." Cewar Maryam.


"Toh ai gaskiya ne, gashi kuma so kike kiyi tafiyar ba tare da sanin mijin ki ba."


"Na yi masa text."


"Sako ba zai wadatar ba, kuma kema kin sani sarai."


"Ni fa na fada miki labarin nan ne, da tunanin kin goyi baya na."


"Kwarai ma kuwa ina goyon bayan ki, kuma na fahimce ki. Labarin wannan yarinyar (idan har da gaske ne) akwai ban tausayi sosai."


"Toh dan haka ki fahimci cewa ina son na taimaka mata ne." Maryam ta fada tana rufe akwatin kayan ta.


"Eh abu ne mai kyau taimakon ta da kike son yi. Amma kina nufin ke daya zaki je?"


"Eh daga ni sai direba." Cewar Maryam.


Sai da Amina ta ja dogon numfashi kafin tace :

"Shikenan zan biyo ki muje tare."


Murmushi Maryam tayi "Dan Allah da gaske kike?"


"Eh! Ai kin san ba zan barki ki tafi wata uwa duniya ke kadai ba."


"Kar ki damu, mun dade muyi kwana uku." Maryam ta fada tana mai jan akwatin ta zuwa waje. "Na fadawa mommy ta dauko yara a school, zasu zauna a wajen ta na kwana biyu."


"Nima yanzu na biyo na aje Yasir a gidan. Kuma ko ki fadawa mom da dad zaki yi tafiya."


"Sorry, kuma kema ya kamata ki fadawa Adam kafin muje dan yasan da tafiyar. Ba zan so ki samu matsala da mai gidan ki ba."


"A'a kar ki damu yana da saurin fahimta, zan yi masa bayani daga baya."


"Ni da zaman ki ma kika yi nayi tafiya ta ni daya."


"Wasa kike, ba zan barki kiyi tafiya ke daya ba. Kuma tunda kika bani labarin nan zan taimaka miki wajen cikar burin ki. Bari na kira Mom na fada mata ba zan samu damar dawowa daukan Yasir ba."


"Ok. Ki gaishe min da ita!" Cewar Maryam tana kokarin shiga mota.


Bayan Amina ta gama wayar ita ma ta shigo motar tana cewa : "Yanzu naga Ibrahim ya turo min sako."


Murmushi Maryam tayi "Dan duniyan me yace miki?"


"Wai «Sis sorry na rashin samun damar reply na messages din ki, ina busy ne sosai, amma insha Allahu yau zan kawo muku ziyara ke da sis Maryam idan ba damuwa. Ina jiran amsar ku.» "


"Ayya sorry bro, mu ma yau busy muke ba zamu samu dama ba." Cewar Maryam tana dariyar keta.


"Eh gara shi ma yaji yanda muke ji, dan haka ko reply ba zan masa ba."


"Wannan gaskiya ne, dan haka ina goyon bayan ki!"


"Kina tunanin saboda aiki ne kadai yayi mana wannan nisan?"


"Eh, abun ba sauki gare shi ba na zama lauya kuma yanzu haka nasan akwai mutane da yawa da zai taimakawa, aikin shi ne ba zamu takura shi ba har haka. Mu kan mu wani lokacin ai aikin yana cin karfin mu."


"Eh, na fahimta cewa aikin sa ne duk ya tauye shi, amma kauracewa mutane, da rashin daukar calls, ke hakan baya baki mamaki?"


"Eh ina mamakin hakan! Matsalar baya fadawa mutane halin da yake ciki." Cewar Maryam.


"Baya dai fada mana, amma nasan yana fadawa mommy, domin yana ziyartar ta ba kamar mu ba."


"Hakane! Kenan mommy tasan abinda ke damun Ibrahimu."


"Kin san wani abu, ina tunanin ko soyayya ya fara?"


Dariya Maryam tayi tace "Mace dai? A'a ban yarda ba. Ibrahim tun Ramlat, ban sake jin yayi zancen soyayya ba.. Toh ban dai sani ba ko mu ne bamu da labari."


"Allah dai masani, idan fa ba shi ya fada mana abinda ke damun sa ba, ba sani zamu yi ba."


"Toh yanzu dai mu bar wannan zancen, idan muka dawo sai mu je wajen sa, in yaso mu matse masa lamba sai ya fada mana abinda ke faruwa."


"Yes, ina tare da ke!"


"Adam zai fahimta idan na fada masa dalilaina na binki, kuma nasan ba zai dau lokaci ba zai sauko. Ke kuwa ki san yanda zaki yi ki kwaci kanki daga yanayin da mijin ki zai shiga idan yaji tafiyar ki."


"Bari wannan maganar dan Allah, ni kokari ma nake kar in tuna hakan, dan kuwa ina iya canza shawara."


Biyawa suka yi ta gidan Aminatu, dan ta dauki abubuwan da zata bukata kafin su dau hanyar Kutiala garin su Aydanatu.


Tana zaune a cikin mota, tana kallon manyan bishiyun da suke ta wucewa, tunani take kan daukar dala ba gammo da ta sawa kanta.


Tunawa tayi da Aydanatu, da sauri ta bude jakar ta ta fiddo littafin.


Tsoron karanta littafin take a yanzu, tana tsoron ta buda ta sake haduwa da wani kuncin da yafi na baya.


Bayan dogon tunani da tayi, ta yanke shawarar cigaba da karantawa daga inda ta tsaya.


[..., Kwanaki hudu sun shude bayan wannan daren, daren da babana yayi min barazanar korata daga gida, kuma abubuwa da dama sun faru. Abubuwan da zan so ace mahaifiya ta ce zan baiwa labarin ta yanda ina kuka tana share min hawaye.


Na kasa fahimtar yanda aka yi duka kayan tsafin Hassatu suka bace, alhali bata fita daga dakin ba. Hatta wannan yar karamar akwatin bata nan! Yanzu babana yana kallona ne a makaryaciya kuma na kirkiri wannan kazafin ga Hassatu dan na kare kaina ne daga fitar dare da nake! Ta yaya ya iya wannan tunanin a kaina, ni 'yarshi? Kuma ta yaya ya iya yimin barazar korata daga gida? Ya fada kuma baida alamar wasa! Babana a shirye yake yayi waje dani akan wannan matar!


A daren ban iya runtse idanuna ba, haka na zauna har gari ya waye nayi aikace-aikacen gida, sannan na dora abin karin kumallo.


Kowa na gidan ya hadu bisa dinning table domin karyawa banda ni da bani da wannan ikon. Babana bai taba komai ba daga abinda na hada masa, sai Hassatu da yacewa ta hada coffee. Har yanzu ransa a bace yake, ko ido bai son hadawa dani.


Yayin da Hashim da Safiyya ke shirye-shiryen zuwa school, ni ina cika thermos da ice cream. Da zuwana bakin school din, kamar yanda na saba, na bawa mai gadi thermos din ya ajiye min, ya amsa da murmushi kamar kullum.


"Toh yaya kin shirya?" Cewar Safiyya dake jirana bakin kofar class.


"Shiryawar me?"


"Muna da exam yau, kuma dake nayi kwance domin samun maki mai kyau."


"Kar fa ki manta ni bar yar makarantar nan ba ce, kuma bani da ikon zana exam bare na taimaka miki." Na bata amsa.


"Ai wannan tsohon zance ne. Ki sani jiya bayan mun yi yarjejeniya dake, na kira Malam Khabir na fada masa ya rubuta ki. In fada miki dai ni na taimaka masa wajen rubuta ki." Ta fada tana murmushi.


"What? Baki tsoron mahaifiyar ki ta gano abinda kika yi?"


"Wannan matsalata ce! Zo mu je." Ta fada tana jan hannuna. "Waje daya zamu zauna a baya."


"Toh naji sake ni, zan iya tafiya ni kadai."


An fara jarabawar kuma topic din kamar ruwa yake a gare ni. Na kare cikin mintunan da basu wuce 40 ba, daga nan na jira Safiyya ta gama sauyewa.


"Kin san dai ba kyau abinda muke yi ko? Haramun ne cheating!" Na fada da kokarin nuna mata kuskuren yin hakan.


"Ke ni yimin shuru kuma ki juya min takardar na kwashe."


Numfashi naja tare da girgiza kai kafin na juya mata takardar.


Bayan an gama, Malam Khabir yace na same shi a office din sa.


"Ka rubuta ni ba tare da amincewa ta ba." Kalmar da ta fito daga baki na kenan lokacin da na shigo office din sa.


"Toh ba abinda muke so ne ba baki daya? Kiyi karatu?"


"Eh amma ba ta wannan hanyar ba! Ina iya samun matsala akan wannan abun."


"Kin ga zauna." Ya fada. "'yar uwar ki Safiyya tace min tayi magana da mahaifin ki kuma ya amince naje na rubuta ki."


"Me? Abinda tace maka kenan?"


Ji makaryaciya!


"Eh, na fahimci kina da yan matsaloli a gida amma ba hujjah bace na kice ba zaki yi karatu ba, kuma bayanin da Safiyya tayi min na cewa ta shawo kan mahaifin ki, naji dadin sa."


Bansan me zan ce masa ba, godiya kawai nayi masa kafin na fito daga office din.


"Oh Allah na kamar nayi hauka!!" Na fada da dan ihu bayan nayi nisa da office din.


"Ayda meke faruwa ne?"

Cewar Faruq da jin ina ihu. Ina son na bashi labarin komai amma tunawa da yarjejiyar mu da Safiyya nayi shuru.


"Ba abinda ya faru. Ni zan wuce ko zaka sakar min hanyar dan Allah?"


"A'a Aydanatu, yau sai kin fada min duk abinda ke faruwa, kuma kin fada min me kika je yi a office din wancen malamin."


"Ka gane ko ina son na fada maka komai ba zan iya ba. Ba zan iya maka magana ba, ko na ganka." Na fada idanuna da kwalla.


"Kamar ya? Me zai hanaki yimin magana? Ko kuma ince waye zai hanaki?"

Yanayin muryar sa ya canza, da alama ransa ya baci.


"Malamin math ne yace ki daina kula ni?"


"Me!?"


"Kin jini da kyau Aydanatu!" Ya fada a tsawace. "Ki gaya min wa ya hana ki?"


"Toh me zai sa malam Khabir yayi hakan?"


"Wa ya sani? Wata kila sonki yake shi yasa zai ce ki daina kula ni dan yana kishi!"


"Wai me kake cewa ne haka Faruq?" Nima wannan karon a tsawace nayi maganar. "Ba abinda ka sani, dan haka kar ka sakawa zuciyar ka wani abun."


"Eh ai dole ki ce haka!" Yace yana kare min kallo kasa da sama. "Ba banza ba kika daina zuwa gani na, kika daina fada min komai kuma kika yi nesa da ni."


"Eh ba banza ba na daina yin hakan, amma kuma ba abinda kake tunani bane!"


"Ai sai ki fada min dalili ina jin ki, wata kila na yarda da abinda zaki gayi!"


"Faruq din da na sani ko nake tunanin na sani, baya bukatar sai na fada masa wani abu kafin ya yarda da ni ko ya goyi bayana! Ta yaya ka iya wannan tunanin a kaina? Kowa zai iya min mummunar fahimta, kasa fahimtata, muzguna min na daure, amma ace kai kayi min?"


"Ba zaki dabaibaye ni da wannan kalaman ba Aydanatu! Na goyi bayan ki, na kasance kullum a kusa dake kuma na yarda dake! Amma ban taba tunanin zaki yi saukin saukowa har haka." Ya fada kamar zai yi kuka.


"A yanda na dauki amintar mu, ba zan taba yi maka mummunar fahimta ba kuma ba zan taba kama zancen wasu akan ka ba, kasan saboda me? Saboda na yarda da kai!.."


"Toh ni kuma Aydanatu, na dade da daina yarda da zancen ki. Safiyya ta dade tana fada min haka amma ban taba kamawa ba saboda na yarda da ke. Kullum cikin fada min ..."


"Ta fada maka me?"


"Duk abinda ya dace na sani game da halin ki."


"Na kasa gasgata cewa ka yarda da karairayin da take ma."


"Ko ba komai ita ta yarda da ni, kuma tana fada min komai alhali ni kuwa kullum cikin hantarar ta nake."


Juyawa nayi da niyyar tafiya, amma ya riko hannu na.


"Ta fada min komai game da malam Khabir. Ayda, karatu bai zama wani abu ba idan har sai kina soyayya da malami kuma yana fasikanci da ke."


Kalaman sa sun kona min zuciya, ta yanda bansan lokacin da na mareshi ba kafin na fashe da kuka.


"Kar ki manta fa yana da aure, kuma yana da ƴaƴa. Kada ki bata goben ki kuma kada ki janyowa kanki fushin Allah."


"Kada ka sake fadar wani abun Faruq idan ba so kake na tsane ka ba." Na fada kafin na juya masa baya.


"Aydanatu!!!" Ya kwalo min kira.


"Ka rabu da ni! Kuma kar ka sake nemana ko yimin magana! Daga yau babu wani abu tsakanina da kai domin ka bata amintar dake tsakanin mu."


Wannan ne kalamaina na karshe kafin na juya.


Zuwa nayi na shiga bus ina kuka. Na dawo gida ba tare da Thermos ba kuma ma ban siyar da ice cream ko guda ba, duk suna hannun mai gadi. Rizgar kukan da nake bai bari naji zagin da Hassatu ke ta yimin ba da taji na dawo ba tare da kudin ta ba.


Babana ya dawo lokacin na gama abinci. Na zuba masa kuma wannan karon yaci, daga nan yace yana tafe da labari mai dadi da zai fada mana.


"Ƴata zan yiwa aure!" Cewar babana.


"Wacce Ƴar daga ciki?" Cewar Hassatu da mamaki.


"Ƴata Aydanatu!" Ya bata amsa da murmushi a labbansa.


Kofin kwalbar dake hannuna na saki kasa.


"Bukar ina fata dai wasa kake?" Cewar Hassatu. "Kamar ya zata yi aure, toh wa zai yi aikin gidan idan ta tafi?"


"Kar ki damu da wannan my love, zan samo yan aiki da zasu dinga wannan."


"Toh da wanne kudin ne zamu dinga biyan su? Ko sai na tuna maka halin da muke ciki ne?"


"Ki yarda da ni Hassatu." Ya fada kafin ya juyo da kallon sa gare ni.


"Za'a daura miki aure da Elhj Tukur."


"Za'a daura miki aure da Elhj Tukur!" Wannan kalmar ta maimaita a kalla sau dubu a kaina, amma na kasa gasgata hakan.


Wai zan auri abokin babana Elhj Tukur da ya nuna min rannan.


"Bukar ta yaya ka iya yanke irin wannan hukunci ba tare ka sanar da ni ba?" Hassatu ta fada a tsawace rai a bace.


"Hassatu, yayi min tayin zai aure ta, kuma idan nayi sakaci nan zai iya fasawa ni kuma ba zan bari irin wannan damar ta wuce ni ba! Elhj Tukur yayi alkawarin siyan wannan gidan, kinga ba zamu sake biyan kudin haya ba, kuma zan rage wasu lokuta na aiki na dan nazo nayi su tare da ke my love. Kin gani kuwa tunani ne mai kyau."


"Shikenan babana ya saida ni." Abinda nake ta maimaitawa kenan cikin kaina. Ya siyar da ni ga wani tsoho da ke da mata uku, da kuma 'ya'ya da ban ma san adadin masu shekaru na da wanda suka fini ba.


"Amma mama Elhj Tukur din nan fah tsoho ne, kuma ya haife mata." Cewa Safiyya.


"Mu ina ruwan mu, ke aka ce za'a bashi ko kuwa ita?" Cewar Hashim.


"Hum wannan kasuwanci ne mai kyau, ka bashi 'yarka ya aura mu kuma da cin dukiya da rayuwa mai kyau." Cewar Hassatu bayan tayi tunani. "Amma me yasa bai ce yana son 'yata Safiyya ba?"


"Nima ban sani ba!" Cewar babana.


"What? Wai mama kina nufin sai ki aurar da ni ga wannan tsohon?"


"Rufe min baki..!"


Ni tuni sarawar da kaina yake yi na daina jiyo abinda suke fada. Daga karshe ma bansan inda kaina yake ba, sai bayan awa biyu na farfado.


Kokari nake na yaki kaina akan cewa mummunan mafarki ne nake, duk wani abu mara kyau bai faru ba, mamata bata mutu ba muna rayuwar mu cikin farin ciki, sai dai katuwar muryar Hassatu ta maido ni duniyar zahiriyya.


"Tashi sakarya ki je ki dora mana girki!"


Babu wani karfi a jikina, na shiga kitchen na cigaba da rera sabon kuka.


(....)



Zuwa wajen karfe ukun dare, ina zaune a cikin lungu ina cigaba da matsar kwalla.


"Yauwa ke nake ta nema tun dazu!" Cewar Safiyya.


"Me kuma aka yi, kin zo ne kiyi min dariya ko me? Abinda kuke so ne ya faru ya faru? Rayuwata ta lalace yanzu shikenan sai ku zuba ruwa a kasa ku sha?"


"Bana kaunar ki saboda dalilai da yawa, amma bana goyon bayan auren nan. Iyayen mu ne suka yanke wannan..."


Dariyar karfin hali nayi wacce ta katse mata maganar da zata yi.


"Wai tausayi na ne kika fara ji ko me?"


Shuru tayi na wani dan lokaci kafin tace :

"Mama ke kiran ki, kuma ina shawartar ki da kiyi sauri ki je dan banga alamar wasa ba a tattare da ita."


"Je ki nemo min thermos dina!" Cewar Hassatu bayan naje amsa kiran da take yimin.


"Babu abinda zai samu thermos din ki, insha Allahu gobe zan..."


"Ke wai yaren China nake miki ko me? Nace ki je ki nemo min thermos dina kafin rana ta fito!"


"Amma yanzu fah karfe uku ne na dare, ta yaya zan iya zuwa daukan thermos din ba tare da bus ba?"


"Ba matsala ta bace wannan!" Ta fada tare da mikewa ta kama gashina ta jani har kofar gida. Ina ihu ina rokon ta da ta barni na shigo amma taki.


Bayan bugun gidan da nayi ta yi taki budewa. Gari yayi duhu sosai, tsoro duk ya kama ni gashi bansan inda zan je ba.


Ba zan iya zuwa gidan su Faruq ba, ga kuma ma abinda ya faru tsakani na dashi dazun.


Tunani yazo min naje kamfanin da babana yake aiki. Wata kila cen ya fiye min nan tsaro, idan ya yarda na tsaya. Yafi min sau dubu akan tsayawa a waje.


A saman hanya, nayi nisa, naji kamar takun sawu a bayana, amma ina waiwayawa babu kowa. Cigaba nayi da tafiya, zuwa cen na sake jin takun sawun amma wannan karon ko tantama bana yi biyata ce ake. Ba tare da na waiwaya ba na falla a guje ina ihun neman taimako.


"Kar ku barta ta tsere!" Cewar daya daga cikin masu biyata.


Su uku ne kowanne sanye da mask, gudu nake ba tare da nasan inda nake nufa ba. Hawayen da ke zubo min suka fara sawa ina ganin dishi-dishi kafin nayi tuntube na fadi.


Daya daga cikin su ne ya kamani, sauran kuwa sai dariya suke, ni kuwa sai kuka nake ina rokon su su kyale ni.


"Kar ku yimin komai dan Allah, ku kyale ni naje gida!"


Sumar da ni yayi ta hanyar wanka min mari. Sai da aka kwashe yan mintuna kafin na dawo hayyaci na, naga daya daga cikin su samana yana kokarin yage min kaya, sauran kuma daya ya rike min hannuwa, dayan kuma ya rike min kafafuwa. Sun taushe ni sosai ta yanda na kasa kwakwaran motsi, anan na fahimci tawa ta kare.


Hannuna dake rike da biro rawa yake, lokaci mafi kunci da bana kaunar tunawa a rayuwa ta. Naso a lokacin mutuwa ta dauke ni, da ganin wannan bakar ranar. Kalamai sun yi karanci wajen bayanna abinda naji da abinda nake ji a yanzu. Sun keta min haddi, sun bata min rayuwa. Naji kamar zuciyata ta wargaje ta zama kura yayin da nake jin nishin sa a kaina. Hawaye kawai na iya bari su zubo min a wannan lokacin.


Bayan dayan ya gama, sauran biyun sun so suyi amma da yake lokacin akwai dokar hana fita yasa jin karar jiniyar yan sanda suka gudu.


Suka barni a wurin bani iya ko kwakwaran motsi, hawaye kawai na iya zubarwa.


....]


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ita ce kalmar da Maryam take ta maimaitawa da har ta kai da tayar da Aminatu da bacci ya fara dauka.


"Me yake faruwa ne Sis!?" Cewar Aminatu.


"Anyi mata fyade? Anyi mata fyade Aminatu." Maryam ta fada idanun ta cike da kwalla.


A tsorace Aminatu tace "Akan wa kike magana?"


"Aydanatu..."


"What??"


"...."


Ku biyo ni...


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.