Free chapter · Read without an account
Page 9
Aasim gudu yake shararawa a saman titin tamkar zai tashi sama, Allah ne kaɗai ya kai shi gida. A waje ya yi parking bai tsaya shigar da motar ba ya sauka ya wuce cikin gidan. Cikin falon ya shiga tare da fara ɗaukar throws pillow na saman kujeru yana wurgi dasu, tsananin ɓacin rai ne ya bayyana a fuskarsa, zuciyarsa zafi take yayinda ƙwaƙwalwarsa ta kasa tsaya mishi tunani ko ɗaya.
Wurgi ya yi da throws pillow na hannunsa guda ɗaya da ya rage, da ƙarfi ya sauka saman plasma falon wanda yake ajiye a saman tv stand, ai kuwa tuni ya faɗo kasa cikin rashin sa'a, rass ƙarar fashewar screen ɗin jiki ya cika falon na daƙiƙa.
Aasim zubewa ya yi saman kujeran falon yana dafe kansa, idanuwansa da ya ji suna yaji-yaji ya runtse, a hankali ya furta.
"Why? Why?"
Mintuna hamsin da shida da suka wuce.
Aasim ganin Jabeer ya yi shuru ya zuba mishi ido yasa ya ɗaga yatsunsa biyu ya kaɗa, gira ya ɗaga mishi ya ce.
"What's up buddy."
Jabeer numfasawa ya yi, yana cigaba da kallon Aasim sannan ya ce.
"Aasim kai da Fatima ba ku dace ba sam sam, yes ta haɗa duk abin da kake buƙata but ita ba irinka ba ce wacce take da buri a rayuwa, as i think ko yadda Wife ta faɗa min Fatima ba ta da buri a rayuwarta sai neman wanda zai sota ya kula da ita tsakani da Allah. So..."
"So what? Ce maka aka yi ba zan kula da ita ba ne? To wallahi sai na aureta ko tana so ko ba ta so."
Faɗin Aasim cikin sauri cikin tsawa yana katse Jabeer.
Shuru Jabeer ya yi yana kallon Aasim ganin yadda ya daddage, har da su tada jijiyar wuya. Girgiza kai ya yi tukun ya ce.
"Ka tsaya ka ji me zan faɗa ko? Za ka wani daddage."
"Mene ne? Idan ma cewa za ka yi Fati bata da ilimi ba zan yarda ba, don wannan zamani kowa burinsa ya zama educate one. In kuma arziƙi ne ba ta da shi nawa ya ishemu rayuwa."
Aasim ya faɗa sai lokacin ya farga da yadda ya yi.
Numfashi ya sauƙe yana kallon Aasim ya ce.
"Fatima ba ta yi karatu ba iya Secondary School ta tsaya shi ma government, sai karatun Alkur'ani da take yi, ƴar talakawa ce gaba da baya, ba wayyaya ba ce tamkar yadda kake tunani, ba ta da komai bayan kyau wanda watan watarana zai gushe, sai tarbiyya da kunya abin tunkaho. Na faɗa maka haka ne ba don komai ba sai don Allah, idan da gaske kake sonta ka sota yadda take, idan kuma za ka bi burin ranka to ga fili ga mai doki za ka iya rabuwa da ita Allah zai haɗata da wani."
Aasim ji ya yi wata duhu ta ziyarci zuciyarsa, wani kululun baƙin ciki ne ya tokare mishi wuya ya ka sa faɗin komai, duk buri da ya ci akanta zai tashi a banza, duk abubuwan da ya hango tattare da ita zai rasa, a baya ya ce da zaran ba ta da abu biyun da yake nema zai iya rabuwa da ita tamkar kowa, amma yanzu ji yake ya ka sa tunanin komai.
"Me ka ce?"
Jabeer ya ce yana karantar Aasim.
Aasim ɗago idanuwansa ya yi da suka canza launi, numfashinsa yana fita da sauri sauri.
Tsaye ya miƙe duk da yadda idanuwansa suka rufe haka ya daure ya juya ya bar falon. Da kallo Jabeer yabi shi har ya fice.
...
"What's wrong with me?"
Aasim ya faɗa ya buɗe idanuwansa da ƙyar tuna abin da ya faru tsakaninsa da Jabeer. Fatima ba ta da ilimin boko na kirki, ƴar talakawa ce gaba da baya, ba ta da wayewa, kyau ne da ita sai dirin jiki wanda ya fizgeshi, sai ƙarancin shekarunta.
Aasim ya ma rasa wani irin tunani zai yi akan Fatima, da kanshi ya ce zai rabu da ita idan ba ta da abu shida da yake buri, kuma yana jin yanzu ma dole hakan zai yi wato rabuwa da ita.
***
Biki ya yi biki a cikin gidan Baba Khamis. Ƙarfe sha biyu na safiyar Asabar aka ɗaura auren Ummi da Rayya tare da angwayen su cikin sadaki mai albarka.
Amare sun yi kyau abin su, haka uwar amare Ammah. Ɓangaren Mama da Fatima suma sun yi wanka sun shirya cikin kayansu masu kyau, Mama tana leƙawa waje minti minti, Fatima ɗaki ta shige ta kwanta ganin yau ranar hutunta ne, ga mutane baje suna aiki. Ana fara raba abinci ta fice da sauri ta karɓo nata da Mama, haka kuwa Mama ta dawo ɗaki suka ci tare.
Ranar Fatima ba taje islamiya ba, don ta bayar uzuri tun jiya. A ɗaki ta wuni har dare, ƙarfe bakwai aka fara haramar kai amare, fit Fatima ta miƙe ta fita duk da Mama tana hanata. Tana fita taga motocin kaɗan ne, da ƙyar ta samu wani ta shiga ciki suka matsa mata ta zauna.
A haka aka fara tafiya suka tafi, motar da ta shiga na abokin mijin Rayya ne, hakan yasa nan taje. Bayan sun isa aka sassauƙa, Fatima ta sauƙa ta gyara gyalenta ta ɗaura saman kanta ta rufe fuskarta yadda ba zasu ganeta ba. Da haka ta shiga ta shiga cikin gidan, suka ga gidan amarya mai kyau flat, bayan sun gani aka ce su fito a mayar su gida, haka suka fita aka mayar dasu.
Suna isa Fatima ta sauƙa ta wuce ciki, dakinsu ta shiga ta samu Mama tana jiran dawowarta, mayafin kanta ta cire ta ajiye ta ce.
"Ga shi har mun je mun dawo babu abin da ya faru."
"To barka. Gidan wa ki ka je?"
"Rayya mana."
Fatima ta ce tana ɓata murya da fuskarta. Hakan ya bawa Mama dariya ta murmusa tana cewa.
"Ɗauko min maganina nasha."
"Gobe zai ƙare ko?"
Fatima ta faɗi cikin sanyin murya, idan ya kare ba ta san ya za su yi ba, tunaninta duk ya ƙare, sai bashi wanda ta rasa ina za ta nufa a bata.
Cikin sanyin jiki ta miƙe ta ɗauko ta dawo, kafin ta mikawa Mama ta duba taga saura na kwana uku, numfashi ta sauƙe ta miƙa mata ta karɓa, a hankali ta zauna kusa da ita ta ce.
"Allah zai mana mafita Mama."
"Haka ne Fatima. Tashi ki bani ruwa."
Faɗin Mama don ta fahimci yanayin ƴarta, ita kanta tunaninta ya tsaya cak, inda za ta nemi bashi take nema.
Miƙewa Fatima ta yi ta fita, ta debowa Mama ruwa ta dawo ta mika mata. Mama ta karɓa tasha ta ajiye kofin gefe.
Suna zaune suna hira sama sama har dare ya shiga sosai suka kwanta. Cikin gida har lokacin hayaniya suke basu kwanta ba.
Washegari wuni aka je gidan amare, Fatima ko Mama babu wanda ya yi gigini zuwa gudun magana, gefe ɗaya kuma tsoron Ammah suke ta ci mutuncin su cikin jama'a, shi yasa suka ƙi.
***
Gaba ɗaya jikinta a sanyaye take aikinta dalilin kukan da tasha tun jiya, duk da mijinta ya yi ta lallashinta sannan ta yi shuru ta barwa Allah.
Tana tsaye a cikin kitchen tana ɗauraye abubuwan da ta ɓata wajen haɗa musu breakfast, ba zato ta ji an rumgumeta ta baya, tasan shi ɗaya ne.
Ba ta yi ƙoƙarin juyawa ba, murya a sanyaye ta ce.
"Good morning."
Kiss ya sakar mata a tsakanin wuyanta ya ce.
"Good morning Wife."
Sakinta ya yi yasa hannu ya juyo da ita, fuskarta ta yi ja. Hannunsa ya kai fuskarta ya riƙo kumatunta, murmushi ya sakar mata sannan ya ce.
"Don't worry Wife, i have a solution."
"Really?"
Ta faɗa da murna tana murmushi.
Kai ya ɗaga mata ya ce.
"Yes, and it's gonna work tun."
Cikin farin ciki ta rumgume shi ta ce.
"Thank you Love."
Rumgumeta ya yi shi ma ya ce.
"Welcome Wife, fatanmu Allah ya bamu nasara."
"Amin amin."
Ta faɗa tana ɗagowa ta kalleshi ta ce.
"Mu je mu yi breakfast."
Kai ya ɗaga mata yaja hannunta zuwa waje suka nufi dining, bayan sun zauna abinci ta zuba musu suka hau ci, da suka gama ta mishi rakiya zuwa waje ya fita sannan ta koma.
Yana tafe yana fatan nasara a hukuncin da zuciyarsa ta yanke mishi. Zai ɗauki nauyin komai kamar yadda ya ɗaura mishi, abin da zai yi shi kaɗai zai sa ya gano illar abin da yake yi, shi zai fargar da shi cewa hanyar da ya nemi bi ba mai ɓullewa ba ce.