Free chapter · Read without an account

Episode 7

by Na'ima sulaiman Sarauta · TSINTACCIYA

🌈TSINTACCIYA🌈



FITATTU HUƊU🔥



EPISODE7️⃣


Idanunta tayi saurin kullewa tana jin yadda haɗaɗɗan Baccarat rouge (Maison Francis) parfume ɗin sa ya wani daki hancinta, al'amarin daya haddasa mata lumshewar idanunta, jikinta na wani irin rawa domin this is the best time a tsayin rayuwata da wani ya riƙe ta har ya sanyata a jikinsa so close to him, abin sai ya zama wani Extraordinary to her.

Ajjiyar zuciya ta sauke a hankali ta ɗaga hannunta da suka sauka a saman ƙirjinsa tana wani motsawa saboda zafi da zugin da ƙafarta ke mata yasa sam ba zata iya jure tsaiwar ba, a hankali ta fara yin ƙasa zata zille naman jikinta na wani irin motsi gaba ɗaya jijiyoyin ƙafarta har bawa suke saboda tsananin ciwo..

A karo na biyu Akeem ya ƙara ware gajiyayyun Maraitattun idanunsa tare da sauke su akan Akeela, wani irin lumshe idanunsa yay yana taune bakinsa ji yake kamar ya shaƙe ta ya wuta dama ganinta baki ɗaya a gidan.

Buɗe idanunsa yay yana jan wani mugun tsaki shi dai Abbunsa ya gama dashi, ganin yadda take ƙoƙarin zillewa daga jikinsa ya gently ya gyara tsaiwarsa, tare da ɗaga left hand ɗinsa ya wani manna shi a saman waist ɗinta slowly kuma ya haɗa ta da lafiyayyan jikinsa a hakan yana jin yadda naman jikinta ke rawa na tsananin azaba, cikin nutsuwa kuma ya fara murza Nightgown ɗin dake jikinta da sauri ta buɗe lumshasshun idanunta for the frist time ta sauke idanunta akan kamilalliyar fuskarsa.

Wani irin ƙyakƙyawan bugawa Zuciyarta tayi, zata iya cewa bata taɓa ganin Mutum mai mugun kyau kamar Abdul-hakeem Bukar Bello ba, ƙwayar idanunsa kaɗai zata zautar da mace dalilin daya sanya koshi karan kansa ba kowa yake kalla da idanunsa ba, fuskar nan kamar tai tsartuwar jini saboda wani irin fari da yake da shi, ga wani haɗaɗɗan kewayayyan ƙwantaccen sajansa wanda ya taho da sumar kansa ya ke waye fuskarsa dashi da wani gashin baki amma akwai gemu da saje mai ɗaukan hankali.

Ga bakinsa kamar na mace Ƙarami laɓɓansa masu kauri jajaye wani yirrrrr dasu very cute and softness.

Da sauri ta rufe idanunta domin ba zata iya ci gaba da kallonsa ba wani mugun tsoransa ta keji, laɓɓanta ne suka shiga rawa gaba ɗaya suka jiƙe da yawo a karo na farko ta fisgi kalmar "Uhm..dan Allah kada kayi min zan mutu uhm" ta faɗa tana runtse idanunta sosai bugun Zuciyarta na ƙaruwa.

Taɓe bakinsa yay irin ko a jikinsa ɗin nan kima mutu waye yay asara, gumi ne ya shiga tsastsafo mata a tsakiyar goshinta tsakaninta da Allah take gudun allura, jin yaci gaba da murza rigar jikinta yana son fito da ass ɗinta waje yasa ta matse jikinta domin bata taɓa ganin sabon iskanci irin haka ba sai yanzu ko hannu ba'a taɓa riƙe mata ba, da sauri ta sanya tattausan tafin hannunta wanda ya jiƙe da gumi ga wani irin ɗumi da yake da shi ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kanta kamar wacce take shirin shiɗewa tace.

"Dan Allah banso, kaji...uhm kada ka kalli jikina"

Wani zaro idanu waje yay wato saboda jikinta take wannan abin jikinta ɗin banza yay uwar me dashi, village gal like her ma harta san wani ɓoye jiki.

Wani cije lips ɗinsa yay yana ƙara haɗata ta da jikinsa domin bai zo nan dan kallan wani part of her body ba, banda ɗoyi Meye ma jikin yake yanzu ma sai yaje yay wanka ysin.

Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware dukkan hannayenta ta wani zura su ta tsakanin hammatar sa ta wani irin ƙanƙamesa sosai lokacin daya caka mata allurar cike da zallar mugunta.

Cije bakinta tayi jikinta na rawa kafin ta wani fashe da maraitaccen kuka mai ratsa zuciya tare da kifa kanta a ƙirjinsa, ba taɓa sanin akwai mugunta irin haka ba, ana faɗin zafin allura bata taɓa sanin haka allura keda mafifaffan zafi ba sai yanzu, ji tayi ta ƙara jin haushinsa bata sanshi ba amma daga jiya zuwa yanzu yay mata abinda ko maƙiyinta ba lallai yay mata shi ba.

Ajjiye emtyn injection ɗin yay tare da sauke fuskarsa a tsakanin wuyanta cikin wata kasalalliyyar murya mai ratsa zuciya yace.

“I would rather waltz with the devil of loneliness than tango with a devil like you. I hate you.” ya faɗa yana wani jan numfashi tare ƙara sauke kansa a wuyanta cikin wata husky voice idanunsa na wani ruwa ruwa yace.

“Do you know the real meaning of the world Selfish? Take a look into the mirror and you will find out. I hate you, ke selfish ce kin kashe min ƙani ke gaki nan You still alive kina shaƙar iskar duniya, You killed my brother wallahi na tsane ki bana son ko buɗe idanu na ganki I hate you.. I hate you, I hate you! You stupid gal witch!!!

Ya faɗa yana wani cilli da ita tare da hankaɗata baya Allah yasa da bed kusa da ita gaba ɗaya tai bed ɗin ta faɗa saman sa "Auchhhiiii!!" Ta faɗa tana tura ƙaramin bakinta gaba saboda zafin burgewar da tayi, abinda bai sani ba tunda yay mata allurar bacci yay gaba da ita, gyara kwanciya tayi wani nauyayyan bacci ya ɗauke ta.


Cike da zallar ɓacin rai yake taka ƙafafuwansa a nan Parlo ya samu Abbu da Ummi da Mami harda Didi wacce bacci ya ɗauke ta a saman carpet bakinta ɗauke da ƙashi tana tsotsa.

Kai tsaye upstairs yay yana wani irin fitinannan taku kamar wani ɗawisu, kai tsaye bathroom yay tare da zame jallabiyar jikinsa akan wannan Village girl ɗin yay late a wajan aiki.

Wanka yay ya fito ɗaure da towel kafin yay ɗauki handrayer ya fara gyara sumar kansa, lotion mai ƙamshi ya shafa a saman fatarsa kana ya ɗauki body spray ya fesa, nan da nan sumar kansa ta kwanta luff har wuya jan laɓɓan nan suka ƙara yin yirrrrr dasu.

Wajan closet ɗinsa ya nufa ya ɗauki Sunset Suit Nevy blue ya sanya kana ya ɗura jacket a sama kafin ya sanya white necktie.

Wani half cover shoe ya sanya black kafin ya ɗauki briefcase ɗin sa, wayoyinsa ya ɗauka ya sanya a aljihu gently ya fita daga part ɗin yana tafe yana duba Rolex ɗinsa na Companyn Patek philippe.

Lokacin daya fita bai samu kowa ba sai Didi wacce take bacci kai tsaye fita waje yay dai-dai lokacin da P.a ya shigo bai tsaya amsa gaisuwar P.a yau da kansa ya buɗe ƙofa ya shiga back seat ganin hakan yasa P.a yiwa motar key ya fita da gudu.

Kai tsaye Audi baƙo way suka nufa inda AKEEM BETTER FARMING INSTITUTE A.B.F.I Babban waje ne babba babu mai iya ganin girmansa domin makaranta ce guda ta kuyar da aikin noma, da kuma taimakon mutane, kai tsaye sashin ma'aikata yay tun daga reception aka fara gyarawa ga Hero nan, ga Hero nan hannu kawai yake ɗaga masu har ya isa Elevator yana tsaye kafin ta buɗe ya shiga lift ɗin ya danna 8floor a dai-dai 8floor ɗin ta tsaya ya fito ta office ɗin Md Adnan ya fara shigewa yana wani irin runtse idanunsa sosai.

Kafin ya nufi office ɗinsa wanda aka rubuta Ceo haɗaɗɗan office ne mai kyau da tsari domin hadda ƙaramar cineme da deep frizer ga wasu a.c masu kyau.

Kujera yaja ya zauna a hankali ya buɗe System ya fara aiki.

Ya jima yana dannawa kafin ya ɗauki telephone line ya danna wasu Numbers ɗagawa akai cikin girmamawa akace.

"Mun ɗaga kira daga sashin karɓar ƙorafi Tayaya zamu iya taimakawa maka Dr Abdul-hakeem Bukar Bello Ceo? Lumshe idanunsa yay yana sauke numfashi kamar bazai magana ba sai kuma yace "Uhm Something new?" Cikin nutsuwa matar tace "Yes sir! Mun ƙara samun takardar ƙorafi daga Ƙauyen Wudil akan matsalar ƙwace masu gona, zuwa yanzu Mutanan sun fara yi masu ta ƙarfi"

Tsayawa yay daga danna keyboard ɗin ɗin tare da sauke hannunsa a fuska yana shafa gemunsa cikin ƙasa da Murya yace.

"Uhm! Su waye ne?" "Binciken da mukai ya tabbatar da cewa wasu Manyan shugabannin ƙasa ne suke sun yin kwacan Wannan gonakin domin su kafa wani company kuma an tabbatar da cewa Wannan company na magani za suyi kuma irin haramtattun Drugs ɗin nan masu kashe mutane, suna son yi a Wudil saboda ruwan dake wajan zai hana aji wari da kuma shaƙar hayaƙin maganin"

Miƙewa yay tsaye ba tare da yace komai ba ya kashe wayar baki ɗaya.

Daga 8floor ya sakko zuwa reception a nan ya samu p.a fita yay daga cikin sashin gaba ɗaya ya nufi ɓangaren koyar da ilimin noman.

Tafiya yay mai ɗan nisa kafin yazo ƙarshen wajan wani ƙaton fili ne a ƙalla za'a iya gida sama da ashirin ga wasu ƙanan kurayen ganye sun fara fitowa alamar shukar ta fara huda.

ga yara a wajan da manya hadda ƴan primary school, cikin nutsuwa ya zare takalman ƙafarsa tare da naɗe hannun rigarsa cikin gonar ya shiga tare da ɗaukan Adda ya fara yanke ciyawar da tai tsayi ganin hakan yasa gaba ɗaya yaran suka fara yin aikin da yake.


A can gida kuwa Didi ce ta fito daga cikin gidan zuwan compound da sauri Bala driver ya ƙarasu tana ganinsa tace "Bala maza buɗe min mota" buɗe bayan motar yayta shiga kafin ya tayar da motar gatekeeper ya buɗe masu da sauri suka fita suna fita motar Abbu na shigowa.

A hankali Driven sa yay parking ajjiye jaridar daily trust ɗin hannunsa yay ya fito yana gyara zaman babbar rigarsa kai tsaye cikin babban parlo ya shiga da sauri Amani dake zaune ta riga da wando tana shan chocolate da ice cream ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Grandfa"

Ɗaukan ta yay yana faɗin "eyee matar mai kama da Hero" Murmushi tai masa kafin yace "how was your school?" Tana sauka jikinsa tace "Allahamdulillah Grandfa" ganin babu kowa a Parlo ya san kuma su Aleema basu dawo ba kai tsaye ya nufi part ɗin yaran nasa yana sakin wani irin Murmushi domin ya azabtu da rashin ganin Akeela sosai.


Didi na cikin motar Bala driver yace "Hajiya Didi ina zan kaiki?" Kyaɓe fuska tayi tace "ofishin hisba" jinjina kai yay babu jimawa suka ƙarasa da sauri har tana ƙoƙarin faɗuwa ta shiga ciki tana shiga wajan mutane uku suka miƙe da sauri tace "A'a yaya..nace yaya haka kamar dai ana yaƙi bana son gantali babu ruwana wajan ogan ku nazo" ɗaya daga cikin su yace "Hajiya gani" wani kallo tai masa tace "Malam ogan ku nace yaya zakai min tsaye kamar sandar rake" wani ne yace "shine ogan" haɓa ta riƙe tace "Muhammadur Rasulullah S.a.w a'a babu ruwana akace hisbar malamai ne anya Wannan ya iya fataha ma, Tuf astagafirullah ai karatu kuma dai azuci yake Malam ƙara na kawo" Kallonta yay sosai kafin yace "ok Hajiya tame" fashewa tayi da kuka tace "Ubangiji dai ya haɗani da gantalallan jika abin yay masa yawa ga sata ga maita"

Cikin nutsuwa Abbu ya tura ƙofar ɗakin tun daga door way ya fara jiyo sautin shassheƙar kukan ta, da sauri ya rufe ƙofar tare da shiga ciki.

Tana zaune tayi wanka sanye take da Black Silk short robe sai wata Halter top data ɗura a sama, ta rufke gashin kan nan nata da ribbon ya sauka har baya sai ƙamshi take, wani irin harbawa zuciyar Abbu tayi kamar wanda ake ja da mayan ƙarfe haka ya nufi inda take ba tare da zato ba Akeela ta jita akan....



Me Abbu yake nufi ne😂😂 na kusa gama free pages tabbas daɗi na neman yi maku yawa.







SARAUTAR MARUBUTA

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.