Free chapter · Read without an account

02

by Rahma Kabir · KAZAMIN TABO

ƘAZAMIN TABO


02


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir



Momy ganin halin da yake ciki sai ta isa wajensa ta kamo hannunsa ta ja shi zuwa dakinsa dake sama, suna isa ta zaunar da shi a gefen gado ta tsaya a kansa tana cewa.


Anas dan Allah ka rika dawowa gida da wuri, kaga Abbanku har yanzu dukanka yake bai lura da ka girma ba, haka yake maka hukunci a gabansu Nabeel, shiyasa wlh ko kunyi min abu nake tsoron fada masa domin irin hukuncin da zai yi muku.


Amma Momy kema kin san bana yawo, meyasa Abba zai rika yi min haka? Yasan fa yanzu na kawo girma bai dace ya rika yi min irin wannan hukuncin ba, sai ka ce dan goye.


Ya fada yana fidda kwalla.


Hakuri zaka yi tunda haka Allah yayi shi, Kai dai ka rika kiyayewa kawai ka zauna lafiya ba tare da ka shiga tarkonsa ba.


Hmmm kawai ya ce yana girgiza kai irin zafin zuciya na kunno shi, ya mike ya cire rigarsa ya wuce toilet, Momy da kallo tabi shi cike da tausayinsa ta fice daga dakin. Anas ya shiga shawa ya sakarwa kansa ruwa idonsa a bude sai hura iska yake daga bakinsa, shi mutum ne me tsananin hakuri amma fa fushinsa bai da kyau, Abbansu wani irin mutum ne mai matukar zafi shiyasa ko sun yiwa Momy laifi bata fada masa saboda tana tsoron irin hukuncin da zai yi musu, Hatta Leema da take auta bai raga mata ba, in sunyi laifi ko da kuskure ne gani yake dagangan ne hade da iskanci, shiyasa yake jibgarsu kamar ya samu fulawa, hakan ya kawo rashin shakuwa a tsakaninsa da yaransa, sai mugun tsoronsa da suke kamar sunga kura, da zarar ya dawo daga kasuwa ko wanne zai na natsu, basa iya kwakkwaran motsi gudun kar suyi laifi.


Alh. Habeebu Maitama asalinsu fulani ne dan katsina, Maitama inkiyar Family dinsu ne, shi kadai ne a wajen iyayensa aiki ya kawo mahaifinsa Ahmad garin kaduna daga nan suka kafu a nan, sunan mahaifiyarsa Aina'u wacce suke kiranta da Kakus, Mahaifinsa ya kwanta dama tun yama matashi, Kakus tayi wani auren ta cigaba da rikonsa wanda Allah be bata wani haihuwar ba, shima mijin ba jimawa ya rasu, hakan yasa ta hakura da aure ta daura Habeebu kan dukiyarsu da yake mahaifinsa ya bar masa makudan kudi, sannan ta kara samun tumunin takaba a rasuwar mijinta na biyu, sai Habeebu ya hade kudin ya cigaba da juyawa tare da zurfafa karatunsa a harkar kasuwanci. Har Allah yasa yayi aure ya samu zuri'a.


Haj. Kausar su uku ne wajen iyayensu Rahma ita ce farko Allah ya yi mata rasuwa, sai Kausar sannan Kamal Wanda yanzu ya kammala karatunsa yana koyarwa a primary dake unguwar sarki, asalinsu mutanen kaduna ne daga karamar hukumar kubau, aikin mahaifinsu na gomnati ya dawo dasu kaduna, in da suke zaune a unguwar sarki, mahaifinsu Alh. Tasi'u ya rasu sai mahaifiyar su Binta wacce suke Kira da Hajja Mama ita ce ta rage musu, shiyasa ko da yaushe su Bushra suna zarya zuwa wajenta, saboda yadda take matukar ji dasu, sabanin Kakus da bata cika sakar musu fuskan wasa ba.


Anas shine babba Wanda yake da shekara ashirin a duniya, ya kammala secondary sai dai result dinsa be yi kyau ba, ya zana har sau biyu ba nasara yanzu ne yake kokarin sake zana wani, ya yi saukar Al-Qur'ani. Sai Nabeel ke bi masa yana da shekara sha bakwai wanda yake a ss2 yana aji biyar a islamiya. Sai Bushra yar shekara sha hudu tana jss 3 tana aji biyu a islamiya, sai auta Ikileema tana da shekara sha biyu a matakin primary 6 tana ajiya daya a islamiya.


Sun taso cike da so da kaunar juna saboda Momy tana kokarin hada kansu, sai dai ita mace ce me sanyi wanda yasa bata iya hukunta su in sunyi mata laifi sai dai ta hadasu da Abbansu, shiyasa take koyar dasu duk wanda ya ci zalinsu su rama. Abba mutum ne me tsantseni akan haram, yana da riko da gaskiya shiyasa bai yarda da cin hanci ba, muddun yaro yaki maida hankali a karatu ba zai taba asarar kudinsa ba wajen siya masa jarabawa, a kullun fade yake sai dai kokarinsu ya tsiratar dasu, shi yasa ya kasance mai matukar tsauri da tsare gira saboda baya son wasa da sakarci, a ganinsa yin hakan ga yaransa shi ne zai sa su zama mutanen kwarai masu riko da gaskiya harma suyi ko yi da shi a nan gaba.


Asalinsu kenan a takaice. Cigaban labarin...

_


Da safe.


Anas ya shirya da wuri domin yau yake son biyan kudin special class na lesson, kamar yadda Momy tayi masa alkawarin zata ba shi, ko da ya sauko ya samu har su Nabeel sunyi breakfast sun tafi hadda, sai kawai ya zauna ya zuba abinda zai ci ya gama da sauri sauri, sai ya mike ya wuce dakin Momy, ya shiga da sallama ya same ta tana irga kudi, ya zauna kan carpet ya gaisheta ta amsa fuska sake da tambayarsa.


Da fatan baka yi zazzabi akan dukan da Abbanka ya yi maka ba jiya?


A jiyan dana fito wanka nasha panadol banyi wani zazzabi ba.


To madalla, sai ka kiyaye, kaga dai Abbanku baya raga maka duk da ka girma.


Hmmm, momy batun 5k da Kika ce zaki bani na registern lesson, shi ne nazo amsa.


Anas ya ce tare da kaucewa zancen Abbansu, Momy ta hade kudin da suke bandir din dubu dari ta sanya musu robali ta bude drower ta ajiyesu, kana ta dawo ta zauna tana cewa.


My son ban manta ba ina sane, kayi min hakuri zuwa ranar talata sai na baka, kaga wannan kudin na kungiyarmu ce wanda muke hadawa duk wata, ba zai yuwu na taba musu ba saboda za a iya nimansu ko da yaushe, gobe Insha Allah zan kaisu banki. Zan yi kokari ko a wajen Abbanku na samu na baka, saboda kasan na hade kudadena akan odern kaya dana bayar wanda nake sa ran next week zasu zo. 


Mom in ban bada ba wlh ba zasu barni na shiga ajin ba, tun last week fa suke mini alfarma.


Ka kara basu hakuri Insha Allah talata zaka kai musu kudin.


Haba momy ki bani mana a cikin kudin kungiyarku in ya so kya yi musu bayanin kin ranta, common 5k ace ya gagara ki bani, wlh inna fadawa abokaina sai sun karyata ni, duba ga irin daular kudin na suke ganin Mahaifinmu na da shi, wannan fa yawa ne.


To ba zan bayar din ba in ba zaka jira zuwan talata ba ka barci, duk iya kokarina da nake maka baka gani, inda ta mahaifinka ne ai ba zaka yi lesson din ba, dan haka ba ce min da gani.


Anas ya mike yana kumburo baki da kunkuni ya fice daga dakin. Momy ta bude murya tana cewa.


Ka zo ka rufe ni da duka shi ne zan gane kayi fushi, mara hakuri kawai, idan naga dama sai na hanaka kudin kaje wajen ubanka ka amsa, sai muga in zai baka.


Anas dai yana jinta be ce komai ba ya wuce dakinsa ya dauki takardunsa ya fice abinsa, dama yana da dari uku zai isheshi kudin mota zuwa makarantar da suke yin lesson din, a ransa yana jin haushin irin yadda Abbansu ke nuna ko in kula da karatunsa, yasan ko nawa ne yanada kudin da zai biya masa yayi jarabawa a makaranta me kyau da tsada, amma saboda rikakken ra'ayinsa yana nuna ko in kula da shi, kullun fade yake kudinsa nasa ne ba nasu ba, suyi kokari suyi karatu su tara nasu kudin, bayan in bai kula da karatun nasu ba taya zasu samu har su yi abin arziki, da tunani barkatai ya karasa makarantar ya sauka a napep ya biya kudi ya shige ciki.


     ___________


Kano


Malam Adam Uba shi ne mahaifinsu ya kasance babban malami a unguwarsu, asalinsa dan cikin jihar kano ne daga karamar hukumar Kura, Uba inkiyar kakansu Khadija ne wanda suke hadawa cikin sunansu. Ya samu ilimin addini a wajen wani babban malami a maiduguri kuma ya bashi auren 'yarsa Hafsatu, suka dawo cikin kano da zama ya cigaba da malintarsa, yana da makaranta a jikin gidansa wanda yake koyarwa a nan. Yaransu biyar Aminu ne farko sai Abubakar, sai Ahmad sannan Jabir sai Khadija ita ce auta daga kanta Inna bata sake haihuwa ba, Malam Adam Uba yana da yaya Muhammad Nura wanda su biyu iyayansu suka bari bayan sun kwanta dama, Baffa Muhammad yana da mata Safiyya sai dai Allah yayi musu rasuwa dukansu, ciwon sugar yayi ajalin Baffa wata uku baya Safiya ta rasu da tsohon ciki, sun bar yara uku Amina ce farko tana aure a gombe yaranta biyar harta aurar da biyu, sai Muhammad Auwal shi ne na biyu sai kuma Fadimatu wacce take karamarsu tana aure a nan cikin kano yaranta uku. Tun bayan rasuwar iyayensu Malam Adam ya cigaba da kula dasu shi ne ya aurar da Fadima, Auwal Kuma ya cigaba da zama a gidan ya hadasu da sauran yaransa, a hannunsa ya samu karatun islamiyya sannan ya yi karatun zamani mai zurfi, yayyin khadija duk sunyi aure suna zaune a cikin gidansu, sai dai ko wanne ya ware bangarensa da iyalinsa da yake babban gidane, Auwal da Khadija da kansu suka kulla soyayya babu Wanda ya hadasu, har hakan yazo ya kaisu da aure. Akwai kyakkyawar shakuwa a tsakaninsu yarda da aminci, suna matukar son junansu wanda soyayyarsu ta zama abin kwatance ga jama'a, tunda suka yi aure tsawan shekaru basu taba samun sabanin da wani zai zo musu sulhu ba ko Auwal ya kai kararta gida, da kansu suke shiryawa ko sunyi fada, wannan yasa Baba yake Alfahari da aurensu sabanin sauran yan uwansu da yawanci kullun sai sun kai ruwa rana da iyalinsu Baba yayi sulhu, ganin girma ya fara kamasu sun tara iyali yasa suka daina kai karar juna.


Khadija sai da ta shekara uku da aure kafin Allah yabata haihuwa saboda ita irin matan nan ne da take kwashe wata biyar kafin take jinin al'ada, sai da suka yi dagaske wajen zuwa asibiti ana basu shawarwari da kulawa kafin Allah ya amsa addu'ar su suka samu cikin Ameera, lokacin data haihu mace ba karamin murna tayi ba saboda taci burin samun ya mace domin ta sanya mata suna Amira, anyi shagali sosai domin kuwa Auwal Allah ya bunkasa kasuwancinsa daya fara da kudin gadonsa. 


Bayan shekara hudu ta kuma samun cikin Nura wanda a lokacin arziki ya bunkasa sosai, duk cikin dangi Babu Wanda yake da arzikin Auwal, gashi mutum ne me yawan kyauta hakan yasa kullun cikin hidimtawa danginsa yake, shike dawainiya da duk hidimomin su Baba, dangin abinci da kudin kashewa, hakan yasa ya zama zakara dan gaban goshin yan uwansa. Da Khadija ta haihu Baba yace su sanyawa yaron sunan dan uwansa wato mahaifin Auwal, yaci Muhammad Nura, sai suke kiransa da Nura. 


Amira da Nura sun taso cikin gata da kulawar iyayansu, basu taba niman Abu sun rasa ba, a wannan lokacin Auwal ya baiwa Khadija jari ta soma yin business wanda a hankali itama ta kafu da kafafunta, sunje hajji kusan fin biyar, Auwal ya kai iyayensa da yan uwansa makka, a takaice dai shine tauraron danginsu wanda yafi kowa haskawa.


Khadija bata sake samun haihuwa ba har zuwa wannan lokacin sun ma cire rai, wata kila sune iyakar rabonsu, hakan yasa suka rungumi 'ya'yansu suka cigaba da basu kyakkyawar kulawa. A iya rayuwarsu ba suda wata matsala bama su santa ba, sun soma rayuwa cikin Budi da wadata basu san mace ce ake kira da kaddara ba, komai suka sanya gaba sai sunyi nasara, hakan yasa Auwal tun farkon gina aurensu ya yiwa Khadija alkawarin bata ba kishiya ita kadai ta ishe shi, ba karamin farin ciki tayi da haka ba shiyasa ta sakankance akan anyi ita kadai dan Auwal haka shima dan ita aka haifeshi, da wannan tunanin yasa take kokarin kyautata masa ga duk bukatunsa musamman dangin shinfida bata taba nuna gazawarta ba, kullun cikin gyara take domin ta kasance da'iman a zuciyarsa, bata ganin asarar kudi ko nawane ta kashe su a wajen kayan mata, duk dan ta kasance perfect a gunsa. Shima kam yasan samun irin Khadija a duniyar nan sai an tona domin yadda yake jinta tamkar kullun sake sabunta masa ita ake, in yaji ta yau zam gobe sai yaji tafi jiya zam zam, shiyasa bai da damuwa a rayuwarsa domin Allah ya bashi daya tamkar da dubu.


Asalinsu kenan, cigaban labari.

_

Mami ta nisa tana kallon Haj. Ma'u cikin murmushi tace.


Yau dai kin ji kadan daga labarin soyayyata da Mijina Auwal. Shiyasa ban taba amincewa da yar aiki ba saboda bana taba gajiya da yin hidimar mijina, domin duk abinda nake yi lada nake samu. Iyakar me aikina wanke wanke da gyaran gida shima ban yarda koda tsokali ne ta wankewa mijina ba Ni ke wanke abinda ya shafi na shi sannan dakinsa nike gyarawa.


Lallai Khadija ba kida wasa akan mijinki, yadda kike yi masa din nan bana tsammanin zai kula wata ya mace da zummar yana sonta domin kuwa kin rufe kofar zuciyarta da kyautatawa, nima kuwa kin kara daurani a layi dole zanje in gyara lamarin gidana duk da Ina da kishiya, amma na kula na sakar mata mijina da yawa, Allah ya kara mana zaman lafiya.


Ameen, gaskiya kam ki gyara domin ya kamata kema ki kasance kina gogayya da ita wajen nuna kin fita sonsa da bashi kulawa na musamman, wannan shine kishi bawai ki sakar Mata shi ba, shi namiji kullun kamar yaro yake in da aka fi kyautata masa nan yake malalewa.


Aiko dai Zan dawo zuwa na musamman, domin ki kara daurani a hanya saboda nasan makarantarki na musamman ne, ina da bukatar sabunta karatu.


Cewar Haj. Ma'u tana dariya,Mami ma dariyar tayi ta mike taje kitchen ta dibo musu abinci kana suka ci tare suna kara zantawa, daga bisani Haj. Ma'u ta mike tayi mata sallama.


Ni kam Zan tafi Dan naga fita za kuyi wani lokacin Zan Zo Miki yini.


Godiya nake Hajiya Allah ya bar zumunci. Batun magungunan nan duk results din da na samu za kiji ni a online, d'an jirani ina zuwa.


Mami ta wuce daki da sauri ta daukowa Ma'u turare fesawa guda daya sai turaren wuta kwalba biyu da humra kwalba daya, ta sanya mata a leda ta kawo mata, Haj. Ma'u ta amsa cike da murna tana godiya.


Lallai dole na kuma zuwa ki gayamin inda Kika samu wannan turaruka, kina fitowa na ji kamshinsu.


Hadi ne na musamman Mamana tasa aka yimin daga can gidansu, kinsan kanuri ce yar maiduguri, in dai kin shirya zan fadawa gaggota da take can a hada miki.


Gaskiya dako nagode, insha Allah zan bada kamar 50k a hadomin.


Zako kisha turaruka harda na turara can wajen.


Mami ta fada tana kanne ido, Haj. Ma'u ta kai mata duka ta goce.


Wlh kawata ba kida dama, Allah ya shiryeki.


Tace tana wucewa, Mami ta bita tana dariya, ta rakata har mota suka yi sallama ta shiga ta wuce,Mami da sauri ta dawo ciki dan su shirya su tafi gidansu Baba saboda kusan karfe biyu sunyi rana sosai. 


Rahma ce

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.