Free chapter · Read without an account
03
by Rahma Kabir · KAZAMIN TABO
ƘAZAMIN TABO
03
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
Mami ta shirya da sauri ta hada komai na abincin da zasu kai gida a kuloli, sauran farfesun kayan ciki ta diba nasu ita da Abbansu Amira ta sanya musu magani ta adana a cikin fridge sai ta dauko jug din zobo shima ta zuba musu maganin ta mayar fridge, sauran maganin ta kulle ta adasu a daki, ta sa su Amira suka fitar da kulolin abincin suka wuce, bata dauki motarta ba saboda Abbansu zai daukosu da dare a na shi motar, ta rufe kofarsu ta yi sallama da me gidi suka fita, a bakin gate suka tsaya ta tare musu napep suka hau suka wuce gida.
Minti kusan ashirin ya dauke su suka Kai family house dinsu dake rijiyar zaki, sun samu Baba a rumfar kofar gida tare da wasu daga mutanen unguwa suna cin abinci da alama sun taso sallar juma'a, duk juma'a haka suke yi in sun dawo nan suke yada zango suci su koshi saboda ana yin abincin sadaka a ranar, shiyasa itama Khadija duk ranar suke zuwa gida yini sai dare suke komawa sannan duk zuwa sai ta dafo abinci me yawa ta kawowa iyayensu, haka ma sauran matan yan uwanta da kwantar Auwal duk ranar suke haduwa a gida don sada zumunci, gidan yana cika da iyalinsu tamkar ana wani sha'ani.
Da sauri su Amira suka shiga ciki wanda ita harda gudu ta hada saura kadan ta kifar da kular shinkafar, Mami ta daka mata tsawa ta shiga yi mata fada, cikin fushi suka shiga har falon Inna suka samu duk yan uwa a ciki, Mami ta zauna ta shiga gaishe da su suka amsa, Inna ta kalli Amira tana cewa.
Ke kuma da kika shigo a kumbure kamar an sanyawa fulawa yeast me aka yi miki ko gaisuwa babu.
Rabu da ita Inna ta fashe mana, na rasa irin rashin natsuwa da Amira ta samo kwanan nan, tana girma amma tana kara zama mara hankali komai sai ta sanya kuruciya a ciki.
Me tayi ne haka? Gaskiya ki rika raga mata har yanzu Amira yarinya ce.
Cewar matar Yaya Aminu, Hmmm Mami ta ce ta shiga basu labarin abinda ya faru, duk sai suka yiwa Mamin ca cewar kuruciya ce zata bari, daga nan kuma suka shiga hirar zumunci.
Sai bayan sallar Isha'i Abbansu yazo daukarsu, shima sai da ya zauna suka Sha hira dasu Baba sai wajen karfe goma da kwata suka yi sallama da mutanen gidan kafin suka kamo hanyar gida, tuni Amira da Nura suka yi barci a mota, ko da suka iso Abba ya dauki Amira Mami ta dauki Nura suka kaisu dakunansu dake kusa dana juna, kafin suka fito suma suka wuce dakinsu ko wanne yayi wanka da shirin barci, Mami tana kokarin zuwa dakin Abban sai gashi ya kawo kanshi yace cikin wasa.
Yau dai uwar gidata tabarni da yunwa tun rana rabona da abinci, anya Sweet Kady baki rage sona ba?
Afwan Ruhi nayi zaton ko kaci wani abu kafin kazo daukarmu, amma bari yanzu na kawo maka farfesu kaci da bread hade da zobo me sanyi nima saina taya ka ci. Kuma kasan soyayyarka baya taba raguwa sai dai ya karu, sannan uwar gida nake kuma amarya a gunka, ko ya kace?
Hakkun my dear, yanzu muje ki fara sallamata tukuna.
Sai ya yi gaba ta bishi a baya, ta shiga kitchen ta dumama farfesun ta zuba musu kana ta daura komai a faranti ta fito falo da shi, ta daura a center table ta jawo shi gabansu kana tace.
Bisimillah.
Da kyau khadijatul kubura aikin ki yana kyau.
Murmushi tayi ta zauna gefensa suka fara cika kundunsu, sunci sun koshi sosai kafin ta kwashe kayan ta wuce da shi kitchen, ta fito ta samu ya wuce dakinsa sai kawai ta koma nata dakin ta wanke baki ta kwanta rigingine, a gajiye take bata so ya kusanceta domin maganin jikinsu bai fara aiki ba, dan haka ta yi kwanciyarta ba jimawa barci ya dauketa. Shi kuwa zama yayi yana tunanin wani abu a cikin ransa da alama kunshe yake da damuwa, sai dai ya danne hakan har ita Mamin Bata hango ba, maganar daya tattauna da wani abokinsa dazun Alhaji. Abba yake tunawa daya ke ce masa.
Alhaji Auwal lokaci ya yi da ya kamata ka fito fili kasanar da matarka abinda ake ciki, in ba haka ba wlh wankin hula zai kaiga ga dare, ba zai yuwu Allah ya wadata ka sosai ace ba zaka more kudinka ta yadda kake so ba, kadana duk wani sharadi da musulunci ya gindaya da ka kara aure, dan haka mori lokacinka kafin ya kure maka ka daina tsoron matarka.
Alhaji. Abba dole naji tsoron tunkarar Kadija da wannan batun, domin kuwa akwai ajiyayyen alkawari da nayi Mata cewar bazan kara mata kishiya ba, sannan tana iya kokarinta wajen kyautata min, bana son abinda zai gindaya ya farraka farin cikinmu.
To sai ka sanar da Bilkisu cewar ka fasa aurenta, ka cigaba da zama da matarka sai ka ce fasto, ace duk tulin arzikinka yara biyu gareka gaskiya baka more ba.
Ina son Bilkisu bana son alakarmu ya tashi a banza, saboda tsawon wata shida dana yi da ita na fahimci mace ce mai dadin zama.
To in hakane kaje ka sanar da Baba, na tabbatar zai shige maka gaba akan komai, ko da Khadija zata kawo maka matsala shine zai seta ta.
Hmmm na jima da sanar da Baba ya kuma bani goyon baya, yanzu dai dole zanyi masa magana akan turawa gidansu Bilkisu domin a fara maganar aure, Ban son a dauki lokaci a sanya bikin wata guda ya isa, in yaso yau zuwa gobe zanyi kundun bala na rufe Ido na sanar da Khadija.
Kafin nan ka yi Mata abin alkhairi wanda zai sa taji dan dama dama a ranta.
Hakane, dama motarta ta samu matsala yau din nan zan sanya a nimo min sabuwa mai kyau 'yar yayi, sannan sai na bata 500k ta kara jali. Ina ganin in nayi mata haka abin zai zo da dauki.
Da wannan shawarar suka rufe zancen tare da karfafa masa guiwa da Alh. Abba ya yi akan lamarin, shiyasa dazun da yaje dauko su a gidansu ya kebe da Baba suka yi maganar turawa gidansu Bilkisu, inda Baba yace Insha Allah washe gari asabar zasu je tare da wani abokinsa sai Yaya Aminu da zai kaisu, ya ba shi dubu dari biyu akan duk yadda aka yanka musu sadaki, Baba yayi murna sosai tare da sanya albarka a ciki.
Abba ya dawo daga tunanin ya nisa tare da mikewa ya bude Waldrop dinsa, ya dauko kayan daya cire ya dauki key motar da ya siyawa Mami, ya dawo gefen gadonsa ya bude drower da key ya ciro bandir din Yan dubu dai dai guda biyar wanda ya kama dubu dari biyar, ya rikesu tare da karanto Addu'a a zuciyarsa na samun nasara akanta ya nufi dakinta, ya tura kofa da sallama ya hangota ta yi dai dai a gado tana sauke numfashi a hankali, alamun barci ya yi nisa sai kawai ya barta ya fito tare da rufo mata kofa, ya dawo dakinsa ya adana kudin da key din, ya kashe wutar dakin ya dawo ya kwanta tare da addu'ar barci ya rufe ido, da zummar gobe in Allah ya kaimu zai sanar da ita komai.
__________
KADUNA
Momy cikin sauri ta shirya cikin tsadadden leshi orange color Wanda aka yi Mata dinkin doguwar riga tasha aiki, sai ta sanya milk din gyale ta sanya takalmi da jaka baki ta dauki key mota ta fito da sauri ta nufi dakin Abba dake kasa, shi sam baya son hawa sama shiyasa yafi zama a dakinsa na kasa, tana shiga ta same shi zaune bakin gado cikin shirin fita yana duba jarida, ta shiga da mamaki tana cewa.
Na yi zaton zan sameka kana barci.
Hajiya Kausar barci bai ganni ba dole zan fita saboda jiya aka sauke mata tirelan shinkafa, dole zanje naga aikin da yaran nan za suyi wajen jerasu a store dinmu.
Ok nima Zan fita wajen taron nan namu sai zuwa yamma Inna dawo, na bar komai wajen me aiki zata kula da gidan.
Ki tabbatar da ba ita zata yi mana girki ba dan kin san bana cin abincin masu aiki, Kuma ki dawo da wuri saboda yaran nan duk da Hajiya tana nan.
Karka damu abincinmu Ni Zan girka na rana ne kawai zata yi musu su ci. Yauwa ina maka tuni ranar alhamis birthday din Nabeel dan Allah ko kudin cake ne ka bayar a siyo muyi bikin mu kadai, ba sai munyi taro ba a gida.
Kema kin san babu tsarin wannan bidi'ar a gidana, dan haka sisina ba zai yi ciwon kai ba, babu wani bikin birthday da za ayi.
Alhaji na kwana daya ne fa, kuma daga ni sai su za muyi abinmu, na yanzu ne da zarar sun girma ba za muyi musu ba.
Na dai ce ba za ayi ba in kuma ban isa da gidana ba sai naji.
Hmmm Allah ya kyauta, ni na wuce.
Tace cikin fushi tare da wucewa abinta, Abba ya bita da kallo yana girgiza kai, gaba daya ita tana son rayuwar turai, da ace tayi karatu me zurfi Allah Kadai yasan irin abinda zata yi, yasan duk tana irin wannan abin ne saboda haduwa da take yi da gogaggun Yan boko masu ra'ayin rikau, banda yana taka mata burki da irin abubuwa da zata tsiro da shi a gidan sai Allah, da yake kaifi daya ne shi shiyasa yake seta mata tunani. Ajiye jaridar ya yi ya dauki key din motarsa da waya ya fito, sashin mahaifiyarsa ya tafi ya sameta a falo suka kara gaisawa kana ya zauna suka taba hira daga bisani yayi mata sallama ya fito, har mota ta rakoshi tana zuba masa addu'a, cike da farin ciki ya fito domin a kullun addu'arta yana matukar kara samun nasararsa, kullun haka suke rabuwa shiyasa yake Kara samun Budi da falala saboda tsantsar kyautatawa mahaifiyarsa da yake yi.
Momy ta isa wajen taron da yake a arewa house ne ta samu har an fara, wato ta yi latti nan kawayenta suka yi Mata cha, hakuri ta basu da jero musu uzirinta, ta shiga wajen taron ta soma hada hada, ta hadu da mutanen da suka jima Basu hadu ba ciki harda Yar uwarki matar gomna Hajiya Kaltume wacce take cousin din First lady din gomna, suka gaisa na yaushe gamo a nan dai suka zabunta zumunci sosai har suka yi exchanging numbern juna. Taro ya yi taro sai wajen karfe hudu aka watse, daga nan Kuma suka dunguma zuwa gidan matar gomna domin suci liyafar da ta shirya musu, su Momy sai fi'ili take da shigewa matar gomnoni domin a dama da ita, da yake macece mai fara'a da barkwanci nan da nan ta kara fice a wajen taron.
Anas kuwa tunda ya fita be dawo gida ba, daga lesson sun wuce gidansu Faisal. Su Nabeel kuwa karfe hudu da mintuna suka dawo makaranta, sun samu ba kowa dan haka su Bushra suna gama cin abinci suka wuce sashin Kakus, Nabeel kuwa ya zauna yana duba littafansa tare da tunanin hanyar da zai samu dubu uku wanda zai kashewa abokansa a boko gobe Monday, da yake sun hada wani gasa ne a tsakaninsu wanda suke su shida a group dinsu, sun sanya gasar ko wacce rana daya daga cikinsu zai kashe musu kudu a break, dan haka Monday din data wuce suka fara a inda har ranar juma'a sunyi to wannan Monday din Nabeel shine karshe da zai kashe musu kudn break, to kullun abinda ake ba shi dari biyu ne saboda school bus ke kaisu ya dawo da su kuma suna tafiya da abinci, dari biyun sune ya tara na kwana biyar ya kama dubu daya, to yanzu yana niman dubu uku domin ya kashe musu kudi kamar yadda suke wasa shi, saboda kullun nunawa yake gidansu gidan kudi ne Suma abokan sun shaida haka, domin sun sha kawo musu ziyara a gida Kuma yadda suke ganin haduwar gidansu yafi na dukansu kyau da tsari, shiyasa suke ganin babansu Nabeel yafi iyayensu kudi, hakan yasa suka sanya shi karshe a gasar a ganinsu zai kashe musu kudi sosai, shi kuma baya so yasha kunya shiyasa yaketa damuwa da tunanin inda zai samesu, a sanin shi dai Abbansu baya sakar musu kudi ko da wani abu na makaranta in ya taso direct headmaster ke sanar da Abba a waya ya tura musu kudi, shiyasa ko Nabeel ya dawo yace ance a biya kudin kaza Abba ke karyata shi ya san ya biya komai kuma yana samun duk wani sanarwa a bakin shugaban makarantar, dole yasa ya daina kawo zancen saboda yasan ba zai samu komai ba, kuma ya san koda ya tambayi momy bai wuce ta bashi 1k ba shi Kuma so yake a kalla ya rike 4k ko 5k shi ne zai yi Masa yadda yake so, haka ya gama jera takardunsa ya sanya a jaka ya mike da sauri ya nufi dakin Abbansu sai dai kash ya samu a rufe, dama niyyarsa ya duba in yaga kudi ya dauka, sai kawai ya wuce dakin Momy ya san bata rasa ajiye kanunan kudi ya dauka tunda ba yau ya saba haka ba, da yake ita bame kula bace ko da bata ga kudinta ba bata cika damuwa ba saboda kullun cikin kudi take, tafi daura lamarin ga Yar aikinsu shiyasa Bata taba tambayarta ba, domin tunaninta Bai kai ga yaranta ba dan tasan ba suda matsala balle suyi tunanin daukar mata kudi. Nabeel Yana shiga dakin ya nufi drower ya fara dubawa baiga komai ba ana wannan gefen, Sai ya dawo dayan side din ya bude drowern kasa nan take yaci karo da bandir din kudin kungiyarsu data ajiye, jikinsa na rawa ya dauko ya zari guda goma ya maida sauran ya rude drower, ya fito dakin da sauri ya koma dakinsa ya kirga dubu biyar ya sanya a cikin takardunsa ya rufe jakar, kana sauran ya rike a hannu yana tunanin yadda zai yi da su saboda baya so ya tafi dasu makaranta duka, zai ajiye koda gasar ya sake dawowa kansa next week sai ya yi amfani dasu, amma yana tsoron ajiyesu a dakinsa kar azo a gani ya rasa amsar da zai bayar, dan ya san Momy ba zata kyale maganar ba sai Abba yaji, kuma yana tsoron hukuncin da zai fuskanta.
Rahma ce.