Free chapter · Read without an account
Part 5
Page👉🏻5
.....Nawaff ya tsuke fuska, itama yasmeen ta tsuke tata fuskar.
Yak'araso gareta cikin wani taku na isa da tak'ama, wajen yayi tsit ana kallonsu, yayinda masu hotuna suketa haskasu.
Yak'araso daf da ita, tamkar zai shige jikinta, tayi saurin ja baya, ya had'a yatsunsa biyu yana bugawa, yay k'asa da murya yanda ita kad'ai zata iya jinsa, ya ce, "wlhy kika yimini hauka awajennan saina aikata miki abunda 'yan jaridu da mujallu zasu buga a safiyar gobe juma'a.
Dukda tsoro mai tsanani yashigi yasmeen wannan bai hana ta hararar saba, ta rik'e k'ugi cikin tsiwa ta ce, "kai baka isa kasa 'yan jarida yad'aniba, kuma ALLAH shizaimin tsari da sharrinka.
Nawaff modeebbo yad'an d'ago yana kallon yanda hankalin mutane yadawo kansu, saiya saki murmushi na basarwa.
Gaba d'aya gurin yad'auki sowa da fad'in sun dace da juna.
Nawaff yaja tsaki tareda fad'in shashashu kawai, ta ina na dace da wannan mai kama da aljanar.
Yasmeen ce kawai taji furicinsa saikuma mai gabatarwa dayake kusada su tsaye.
Yasmeen tai murmushin takaici ta ce, "ai basu bane shashashun kaine babban shash............kafin tarufe baki ya damk'o hannunta ya murd'a da k'arfi, wani tsananin zafi yaratsata har kwakwalwa, ALLAH yasota fitilar gurun Blue ce tana kuma kunnawa ta kashe, dan haka ba kowa yaga muguntar da Nawaff yake mataba.
Zafin ya ratsata sosai, afusace ta watsa masa mari, da sauri yasaketa yana murza kumatu, itama takoma kusada amarya da sauri ta zauna tana haki.
Nawaff yad'ago da sauri danjin andafa shi, mas'ud yagani tsaye.
Mas'ud ya ce, "plz my bro's ka share kawai, karka bari wani yagane wani abu dake faruwa.
Nawaff ya kalli mas'ud da idanunsa dasukayi jaa, ya ce, "wlhy Mas'ud saina yima yarinyarnan abinda zatayi dana sani arayuwarta, kamar yanda ka buk'ata zan barta ammafa had'uwarmu tagaba batada k'yau ko kad'an, kuma ka rubuta ka ajiye.
Yana gama fad'a yakoma mazauninsa dake kusada ango, mas'ud ne ya wakilcesa, wajan fad'ar duk abinda ake buk'ata.
Asmy ta ce, "yasmeen wai miye had'inki da modeebbo??, yasmeen ta share hawayen fuskarta, ta ce, "karki damu zan sanar miki, amma ba yanzuba.
To shikenan asmy tafad'a, tacigaba da lallashin yasmeen, yasmeen ta ce, "Asmy kiyi hak'uri zan tafi gida, dan kaina yana mini ciwo.
Asmy ta ce, "babu damuwa dear kije gobe ma had'u, ngd da k'ok'arinki.
Yasmeen ta mik'e tana neman Ameena, bayan ta ganta suka fice, duk abinda take Nawaff yana kallonta, suna fita yarufa musu baya, shima mas'ud binsu yayi.
Yasmeen tana k'ok'arin neman balarabe saitaji an fisgota ta baya, tajuyo da sauri, gabanta yafad'i rass dan ganin NAWAFF,
Ya had'e fuska kamar bashiba, yasmeen ta ce, "lfy konaci bashinkane??.
Nawaff ya damk'i gashin yasmeen data d'aure abaya, ya murd'e da karfi, tako kwalla k'ara, saidai babu maijinta saboda hayaniyar wajen tayi yawa, gakuma kid'a yana tashi, gashi a tsakankanin motoci suke.
Cikin sark'ewar murya ya ce, "nikika mara ko??, to wlhy ki rubuta ki ajiye, wannan marin saiya zama FANSAR BUDURCINKI, NA MELODY , saikinyi dana sanin aikata hakan agareni, ya hankad'ata tadaki motar bayanta.
mas'ud dake bayansu yabi NAWAFF da kallon mamaki, shin miyake nufi da marin datayi masa saiya zama FANSAR BUDURCINTA!!!!????.
Da sauri yarufa masa baya, yayinda ameena ta k'araso takama yasmeen dake kwasar kuka, hannunta kawai taja batareda tace mata komaiba, mota suka shiga bala yajasu suka tafi.
Ahanyama yasmeen sai kuka take, dan furicin NAWAFF yayi matuk'ar gigitata,
ya dawomata da tunanin rayuwarta ta baya, lallai itakam tana cikin tarkunan maza azzalumai, shiyyasa takema maza KALLON KITSE na @UT@R H@JIYA@",, shin wai ita haka rayuwarta zata k'are, kowane NAMIJI burinsa yarabata da Abu mafi muhimmanci ARAYUWAR ta, miyasa haka???, mina musu???, miyasa suke son su rabani da mutuncina???, ta fad'a tana wani irin kuka mai ban tausayi,, Ameena da balarabe duk tausayin yasmeen ya cika musu zuciya, dan afili take maganar batareda ta saniba.
Ameena ta rungumeta tana lallashi, dahaka suka k'arasa gida..........................✍🏻